HS 56

122 22 1
                                    

HALACCIN SO
Zee Yabour
*56*

Baccin kusan awa uku tayi, hud'u saura ta tashi da sunan Allah a baki, Ta mik'e zaune, ledar da ta gani gefen drawer ta jawo ta bud'e, K'amshin nama ya daki hancin ta, Murmushi tayi ko ba komai yana nuna kulawar sa akan cikin, Yadda ta k'agu da cin nama yasa ta kasa tashi d'aurewa baki, Ta soma ci, tas ta shanye ta sha yoghurt rabin babbar gora, Ita kanta tayi mamakin cin nata na yau, wanda idan lafiya ne ba zatayi ci haka ba, Cikinta ta shafa a hankali tace "Allah ya kawo mun kai duniya lafiya yasa ka zama mai tausayi da jin kan iyaye". Ta tashi ta shiga band'aki.

*************************
Mu'azzam wata natsuwa ta musamman yake ji yau, sanin tabbas zuwa yanzu Waziri yayi ma Hajiya magana yasan kuma basu da ja kan maganar sa, Sosai ya maida hankali kan kasuwa, wanda kayan sa suka iso yau, Kamar ko da yaushe nan da nan kayan suka k'ara, Hakan ya k'ara tunzura zuciyar masu hassada su Kawu Kabiru, Kwanakin da suka rage ka shirin sa ya lissafa yana jin damuwar sa ta rage na ganin ya kusa fara galaba kan Mu'azzam,

Jefi-jefi tunanin Shatu na zuwan masa wanda yake alak'anta hakan da cikin sa dake jikin ta, Ba k'aramin so yake ji ba na cikin yana jin tamkar ya jawo kwanakin zuwan sa duniya ya rungume sa a hannu, Murmushi yayi tuna ya kusa zama baba, Tsintar kansa yayi da jawo waya yayi dialing number Shatu,

Ko daga bacci ta tashi tasan mai number, number ce da har abada ba zata goge a kanta ba, duk da ta goge ta cikin wayarta, Ina ma kiran da yake mata kamar da ne da zai kira dan jin lafiyarta da bin ta da kalamai masu dad'i, A raunane ta d'auka tare da yin sallama, D'an jim yayi muryarta na sauka kunnen sa, Ina ma Shatun sa ta da ba wannan ba, Meyasa ta zab'i cutar sa ta hanyar ruguza dukkan farin cikin sa, Wani zafi zuciyarta ta soma yana jin haushin ta, Ya kashe wayar batare da ya tambayi cikin sa da ya kira ji ba, Shatu wayar tabi da kallo tace "Bani yaje kira ba" Ta mayar da wayar kan drawer a raunane, "Ya Allah ka dawo da soyayyata had'i da yarda zuciyar mijina, Ya Allah kada ka sake raba mu". Tayi addu'ar hawaye na cika mata ido.

********************************

Ibrahim ba k'aramin damuwa ya shiga ba sai dai yana k'ok'arin fawwala Allah lamuran sa, tare da k'arfin gwiwar da Mahaifiyar sa ke basa, da nuna masa bawa ya yarda da k'addarar ubangiji ta haka yake jin sassauci, amma soyayyar Shatu ta kasa barin ran sa yana addu'ar Allah ya musanya masa da mafi alkhairi.

*************************

Umma sosai ta dage da yi ma Shatu addu'a fiye da lokutan baya, haka tana ganin rashin dacewa na wofantar da al'amuranta wancan karon, Zaune take kan sallaya tana lazimi Farha ta shigo, Ta duk'a gabanta a shagwab'e tace "Umma Dan Allah zanje gidan Yaya Shatu". Umma sai da ta kai lazimin k'arshe tace "Kuje malam isyaku ya kai ku ke da teema". Rungume Umma tayi cikin farin ciki tace "Thank You Umma". "Ni sakeni kar ki karyani". Ta saki Umma tana dariya ta fice, Umma tabi bayanta da kallo tare da musu addu'ar albarka a rayuwarsu baki d'aya.

Teema kanta ba k'aramin mamaki da farin ciki tayi ba jin Umma ta amince su je gidan Shatu, Cikin k'ank'anin lokaci suka shirya.

*************************

Hajiya Hafsatu da Anty Sahura kowane fuska babu annuri zaune suke jigum suna tunanin hanyar shawo bakin zare wanda al'amura suka cukurkud'e musu lokaci d'aya (Dama duk wanda bai dogara ga Allah ba haka take kasancewa dashi), Hajiya Hafsatu ta kalli Sahura tace "Ya kamata ki kawo mana wata shawara da zamu warware wannan matsala". "Dan' ki ya riga ya b'ata komai tunda har ya kai magana wurin waziri". "Da' na kuma gatsal Sahura". "Eh tunda ke kina nuna son shi a fili har kikayi sakacin da ya raina ki, da zaki bashi umarni ya kai k'arar ki". Hajiya Hafsatu wani haushin Mu'azzam taji ta cika zuciyar ta, tabbas hakane ya raina ta tunda ya kai k'arar ta, A zahiri tace "Naji, yanzu meye mafita?". "Sai nayi tunani dan gaba d'aya kaina ya k'ulle, kinsan ba wanda ya isa ja da maganar Waziri". Damuwa ta sake bayyana k'arara kan fuskar Hajiya Hafsatu, Sahura tace "Abu d'aya ne yanzu zamu fara dashi shine mubi duk wata hanya na ganin cikin bai zo duniya ba, haka mu takurawa rayuwarta fiye da". Hajiya Hafsatu ta jinjina kai tace "Dama wallahi bazan d'aga ma daga ita har uwarta k'afa ba, sai sun san ba'a ja da ni wallahi". "Shima kuma Mu'azzam kisa ya gane kuskuren sa". "Ya zama dole" Cewar Hajiya Hafsatu tana jinjina kai, Sahura tace "Ni zan tafi sai na dawo gobe". Hajiya Hafsatu tace "Allah ya kaimu". TACE "Amin" ta tafi cikin k'uncin zuci.

******************************

Halimatu ta had'a kayanta tsaf na tafiya tayi sallama da yan' gidan su, Kawu Kabiru yana jin sallamarta yak'i amsawa saboda kar ya bata kud'i, Halimatu ko a jikinta a ranta tace "Kud'in ka bana buk'ata zanje inda zan samu kuna na huta". Gidan k'awarta data had'a ta da senator taje, Direba yazo ya d'auketa ya kai ta airport, Da taimakon wani ya mata process na komai, har ta shiga jirgi bata had'u da senator ba, wanda a sirrance ake komai, baya so wani ya gansa da ita a b'ata mishi suna, yana first class, tana economy, Sai raba ido take cikin jirgi, ko zuwa wani gari bata tab'a ba, gashi yau zata bar k'asa, Tayi murmushin farin ciki, Tashin jirgin yasa hanjin cikinta hautsinawa ta k'ank'ame wuri d'aya, Na kusa da ita nata mata dariya, bata dawo daidai ba sai da jirgin ya soma lulawa sararin samaniya.

*********************

Na'ima yau ado ta chab'a sosai tana baza k'amshi ta hakimce kujerar falo, Tana jin k'arar doorbell tak'i, Su Teema ne tsaye waje, Ta kira Shatu wacce cikin bacci taji kiran ta d'auka, "Yaya gamu waje". "Yau zolaya kike ji kenan". "Allah da gaske nake muna bak'in k'ofa" Wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta, Ta tashi ta yafa k'aramin mayafi kan english gown dake jikin ta, Ta fito, Bata lura da Na'ima dake baje falon ba, Wanda tana ganin fitowar Shatu, tayi saurin saka k'afa, K'iris ya rage Shatu ta fad'i tayi saurin dafa kujera, "Ke makauniyar ina ce da bakya duba gaban ki". "Ke kuma idon naki lafiya suke da zaki ga mutum ba zaki bada hanya ba". "Kar dai ki sake kice zaki gaya mun maganar banza wallahi". Shatu kallon baki kai ba ta mata, ta wuce abun ta, Na'ima tabi bayanta da surutai,

Farha da gudu ta rungumeta tamkar sun dad'e basu ga juna ba, Teema tace "Yi a hankali dai kar ki bige mana baby". "Au" ta kama baki tana sakin Shatu, Murmushi ta musu suka shiga ciki, Na'ima wacce duka maganar akan kunnenta tace "Aikin banza kawai, mu za'a ma k'aryar ciki, an rasa tayi dan a dawo gidan daula an b'ige da cikin k'arya". SHATU tace "Shi ciki ai ba'a k'aryar sa dan akwai ranar haihuwa". Dogon tsaki Na'ima taja, Teema da Farha mamaki ya cika su, Shatu taja su zuwa d'aki, Sosai taji dad'in zuwan su, Sukayi ta mata hira, har d'akin suka gyara mata duk da baiyi datti ba suka wanke mata toilet, Sai ana gaf da magrib suka tafi, A harabar gidan suka ci karo da Mu'azzam, Suka gaisa ya musu kyauta kud'i, Shima yayi mamakin ganin su gidan yau,

Shatu bayan ta rako su, jira taji na d'ibarta ta zauna falon ta d'an huta, Na'ima na zaune na kallo tana jifan Shatu da harara, Doorbell tayi k'ara, Saurin tashi Na'ima tayi ganin lokacin dawowar Mu'azzam ne,

Cikin kwarkwasa ta bud'e k'ofar, Yana shigowa ta rungume sa tare da manna masa peck gefen kumatu tace "Sannu da zuwa my husby". Shatu saurin kawar da kanta tayi tana jin wani zafi na kishi na ziyartar zuciyar ta, K'ok'arin dannewa tayi, Mu'azzam tun shigowar sa idon sa ya sauka kanta, Kallonta yake yaga ko zai ga sauyin yanayi tare da ita, Sai dai juyar da fyskarta ya hana masa gani, "Babyna nayi missing d'inki sosai" Ya fad'a da k'arfi ta yadda Shatu zata ji, Na'ima tamkar an tsundumata aljanna, Ta narke jikinsa tare da rik'o hannun sa, Tace "Wallahi nima nayi naka baby" Ta kai masa sumba a baki wanda tayi da k'arfi, Shatu gam ta runtse idonta zuciyarta na harbawa da tsaanin k'arfi, Mu'azzam ta gefen ido ya kalleta, "Hakan na nufin tana kishina?" Ya tambayi kansa, "Meyasa zatayi kishin ka bayan bata son ka" Zuciyarsa ta bashi amsa, Wani b'acin rai yaji, Ya sake matse Na'ima jikinsa yace "Muje kimun tausa na gaji ssoaai". "Toh masoyina". Suka nufi d'aki, Shatu ta bud'e ido tana binsu da kallo, ganin yadda Mu'azzam ya rungumeta jikinsa ya sake dagula zuciyarta, kawai ta saki kuka ba tare da sani ba, Ta mik'e ta wuce d'aki fuskarta sharb'e da hawaye, Kishi ke nuk'urk'usar zuciyarta, yayin da haushin Mu'azzam ke mamaye, "Dama ya dawo dani ne dan ya wulak'anta ni, baya sona yanzu, Na'ima ce muradin ransa" Ta fad'a a raunane hawaye masu zafi na sake wanke fuskarta.


OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now