HS50

114 20 1
                                    

HALACCIN SO
Zee Yabour
*50*

Binne binne na laya kusan kala uku malamin tsibbun yaba Anty Sahura tare da wani gari yace ayi k'ok'ari a zuba mata a shayi ta sha, Matuk'ar akayi su buk'ata zata biya cikin zai zube, Anty Sahura ta karb'a cike da murna ta fita, Kai tsaye tasha ta fara nufa, ta saka sak'on motar had'eja da number mai karb'ar mata sak'o ya kai wa IYA, Kana ta yanki daji babu tsoron Allah da imani a ranta tayi binne binne, Ta nufi gida tana jin zuciyarta wasai.

*************************

Na'ima na kishingid'e falo tana shan wani mango juice, Tana waya da Farouq wanda ke mata k'orafin kud'i da cewar maganin shi sun kusa k'arewa tace masa zata turo, ya bita da kalaman soyayya, Kiran Anty Sahura da ta gani yana ta shigowa wayar yasa tace mishi bari taji lafiya,

"Da uban wa kike ta waya da ba zaki kashe ki d'auki kirana na ba". Anty Sahura ta fad'a a hasale, "Kiyi hak'uri Mama Yaya Mu'azzam ne". "Kirana nayi naji wai ke baki tab'a b'atan wata bane tun auren ku". "A'ah Mama". "To gara ki k'ara bada himma ki jawo mijin ki jiki dan Shatu nada juna biyu". "what". Ta fad'a da k'arfi, "Amma ba wanda ya san da zancen cikin, b'arar dashi zamuyi kafin Mu'azzam ya sani". Na'ima hankali tace "Dan Allah kuyi k'ok'ari Mama idan ya sani wallahi akwai matsala". "Ba zai tab'a sani ba". "Allah yasa" cewar Na'ima cike da damuwa, Anty Sahura tace "Ki k'ara iya takun ki" Ta kashe wayar, Na'ima wata zufa taji na rufta mata a yadda ta d'and'ani daular gidan Mu'azz bata fatan wata mace ta shigo su soma rabawa tare, haka tafi so ta farawa haifawa Mu'azzam yara bata hanyar wata Shatu ba,

Gama wayar tasu ba jimawa Mu'azzam ya shigo, Yau ma yanayin nasa babu sauyi, K'ok'arin b'oye damuwarta ta tayi, Cikin kwarkwasa ta mik'e ta nufe sa da cewa "Sannu da zuwa husby". Da kai ya amsa yana nufar hanyar d'aki tabi sa a baya har d'akin sa, Zama yayi bakin gado tare da sauke ajiyar zuciya alamar gajiya, Gefen sa ta zauna ta kashe wayar tace "Bana son ganin ka a irin yanayin nan, zuciyata kan shiga cikin k'unci da damuwa, ka sanar dani meke damun k". Shatu ta nuna masa yadda take kasa natsuwa duk sanda taga sauyin yanayi tare dashi, Ya watsar da tunanin da cewa "Ba komai ayyuka ne suka mun yawa kwana biyu". "Sannu my husby muje na gasa ma jiki da ruwan zafi". Kamar zai ce a'ah amma kuma yana buk'atar hakan dan akwai gajiya sosai tare dashi, Cikin salo da jan hankali take masa komai har sai da suka tara dan jin Shatu nada ciki ya matuk'ar karkata hankalinta ga son yin cikin, Mu'azzam bayan sun kammala wankan tsarki yayi ya kwanta, zuciyarsa cunkushe da tunani, babu abunda ya saka gaba yanzu kamar son sanin wake son ganin bayan sa, da me ya haddasawa Alhaji heart attack lokaci d'aya, Na'ima na gefen sa ta lafe, Mu'azzam idon sa rufe kamar mai bacci wanda ta d'auka ma baccin yake.

*****************************

Shatu sam cikin bai zo mata da laulayi ba, sai ciwon kai da bacci da take yawan yi, Tashin ta bacci kenan, Ta juyowa muryar Ibrahim a falo, IYA na jan sa zance da cewa "gaskiya kana k'aunar Shatu ba kamar shashancan ba, tunda ta aure shi yake gallaza mata shi da ahalin sa". Ibrahim yace "Allah sarki". "Shiyasa naso a b'arar da cikin kawai babu amfanin had'a zuri'a dasu". "Laifin su kar ya shafi jaririn ciki". "To ai shikenan, dama yaran yanzu taurin kan tsiya ne daku".
Ibrahim shiru yayi yana sunkuyar da kai k'asa, "Bari na kira maka ita idan ma bacci take ba dan bata da aiki sai shi". Ibrahim cikin sadda kai yace "A'ah kyaleta dama nazo gaishe ki ne kawai".(bana son ganin Shatu dan ganinta na tado masa zazzafar k'aunarta, gashi yanzu tana cikin idda), "Dan' albarka ka kyauta kuwa". Hannu ya zura aljihu ya ajiye kud'i gabanta yace "Gashi ku zata buk'aci wani abu". "Angode dan' nan Allah ya karu dubun su, godiya muke dole ka auri Shatu wallahi in dai ina raye". Ta k'arashe da washe baki taga kud'i, Ibrahim ya mata sallama ya tafi, Duka Shatu na jiyo su tana k'ara shaida mutunci da HALACCIN SO da ya nuna mata, lallai ba k'aramin so yake mata ba, K'asan cikin ta ta shafa tace "Allah ya nuna mun na kawo ka duniya lafiya, Na auri Ibrahim ya cancanci na bashi so". Ta fad'a,

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now