HS 63

109 15 0
                                    

HALACCIN SO
Zee Yabour
*63*

Shema'u kuka sosai take tamkar ranta zai fita ne, kuka ne na bak'in ciki, takaici da nadamar auren Kawu Kabiru, yayin da wata muguwar tsanar sa ta mamaye zuciyarta, Halimatu itama kukan take sosai na rashin yar'uwarta tana Allah wadarai da hali irin na mahaifin su, "Kun ga kuna damun sauran mutane da patient d'in mu, ku tashi ku d'auki gawar ta a kaita makwancin ta". cewar wani Dr, Halimatu mugun kallo ta masa tace "Mutane dai tasan k'ofar gidan kowa". "Kamar yadda ba'a kanku aka fara ta ba da zaku cika mana asibiti da kuka". Zata sake magana Shema'u ta dakatar da ita tana tashi tsaye, Kowannen su hawaye bai daina ambaliya saman fuskar sa ba.

******************************

IYA ce hakimce a falo tana yagar cinyar kaza, Saratu da Jummai na gefenta wuya da fiffiki ta basu, tana cin saura, sau tari sai dai suci sauran ta, "Ke kira mun Jabiru naji ya dabbobi na an siyan musu abincin satin nan". Saratu tace "Toh". Tana lalubo number sa ta kira, Yana d'auka ta mik'awa IYA, "Alo Jabiru dabbobin nan nace ana kula dasu sosai dai, kuma an siya abincin su". Yace "IYA ina wuni?". "Kai Dalla bata gaisuwa nake ba lafiyar dukiyata nake tambaya". "Komai lafiya IYA, d'azu ma naje wurin su suna kula dasu sosai". "Da kyau". Ta dak'ile wayar bata jira sunyi sallama ba, Kai ya girgiza yace "IYA da son kud'i ta tsufa amma bata daina som duniya da dogon buri ba, maimakon ta koma neman lahirar ta, Allah ya kyauta". Ya cigaba da sabgogin gaban sa.

*******************************

Shida da arba'in daidai Mu'azzam ya shigo falon gidan sa babu kowa sai k'arar tv dake tashi yana da tabbacin Na'ima ce ta barshi kunne, D'akinta ya fara lek'ewa waya take da Farouq tayi nisa sam bata ji shigowar sa ba, Juyowar da zatayi suka had'a ido zabura tayi tamkar taga Dodo ta sauke wayar kunnen ta, Kallon ta yayi yace "Ya dai?". "Umm umm tsoro ka bani banji shigowar ka ba sai ganin ka nayi". "Yau yan' tsoro ne kenan a kanki, ai nasha irin shigowar nan ko" Ya k'arasa da murmushi, Tace "Eh kam sune" tana dariya a ranta tana hamdala bai ji wayar ba, Tasowa tayi da zumar rungume shi dan har ga Allah ciki take so gashi yak'i zuwa, Ta ware hannaye zata rungume sa, ya d'an kauce da cewa "Bara na watsa ruwa na gaji" Ya fice d'akin, Bayansa tabi da mugun harara tace "Ba dai mayyar can ta fara shiga tsakanin mu ba, to wallahi bata isa ba sai dai ita ta bar gidan nan, ba ni ba gayyar matsiyata" Taja dogon tsaki.

****************************

Budaddiyar riga ce jikin ta, yau ko bra bata saka ba saboda yadda take son watayawa, cikinta da ya fara girma ta soma jin nauyin sa, Waya take da Umma cikin raha da jin dad'i, yanzu sakewar dake tsakanin su tafi ta da, wanda Umma ke ganin gara taja yar'ta a jiki tana jin matsalolin ta, ko addu'a ta rik'a mata tare da bata shawarwari, A speaker ta saka wayar, "Umma ni dai idan na haihu gida zan dawo". Dariyar Umman tayi tace "Idan mijinki ya amince kenan". "Ni dai gara na dawo nayi jego a gida". "Ke dai kiyi addu'a Allah ya sauke ki lafiya ya baki rayayya ko rayayye mai albarka". Tace "Amin". "Ga Farha ta dameni na bata waya". Ta mik'awa Farha dake gefe, "Hello Yaya Shatu yaushe ne edd d'inki Allah na k'osa na fara goya baby dama su Yaya Maimuna basa bari muna d'aukar babyn su". "Ke dai Farha bakya gajiya da k'orafi suma ba basa bari ne ba, kinyi k'arama ne kar ki yadda musu baby". "Kai Yaya Shatu am 12 yrs fah, gaskiya wannan baby ni zan rik'a mishi komai". "Toh ki rik'a mun addu'a na sauka lafiya". Tace "Kullum ina yi, kinsan me?". Shatu tace "A'ah". "Umma har ta fara siyan kayan babies". Shatu tace "Tun ba'a san baby gender ba". "Unisex ne". Shatu tayi dariya, "Bye Yaya Shatu zanyi assigmenta". Tace "Tohm bye".

Duka hirar akan kunnen Mu'azzam wanda tunda ya shigo yaji da Umma take waya, yak'i yin dogon motsin da zata san dashi yana som yaji me zasu tattauna, "Hakan na nufin suna son cikin, idan hakane meyasa tayi yunk'urin zubarwa" Kansa ya d'aure yayin da ya shiga wasi wasi, Shatu gyarawa tayi da zumar kwanciya ta ganshi tsaye, "Sannu da zuwa" Ta fad'a tana ganin Mu'azzam tamkar sabon mutum a wurin ta, "Yawwa" Ya amsa, Yana k'arasowa ciki, Yau ma wani kyau sosai yaga ta masa, yayin da rabin hankalinsa na kan abunda yafi so cikinta, Daga kallon da yake mata tasan jarabar sa ta motsa, tun ba yau tasan shi da yawan neman ta, "Ko haka yakewa Na'ima" ta ayyana a ranta tana jin kishi, Saukar hannun sa kan cikinta da ya taso, ya katse tunanin ta, "Mashaa Allah My baby ya fara motsi". Ya fad'a jin d'al d'al alamar motsin baby, Fuskarsa a washe wanda rabon da taga annashuwa kan fuskar sa tun kafin barin ta gidan, kwantar da ita taji yayi jikin sa, Yana d'age rigarta ya d'aura hannun sa sosai yana murmushi, Sumba ya kaiwa cikin, cikin yanayi na farin ciki da d'oki, Daga haka yanayi ya canza sai dai ya bita a hankali dan gani yake tamkar zai shafi babyn sa, Shatu itama sosai take enjoying duk wani abu da yake mata, hakan yasa bata hana shi itama tana basa nata gudunmuwa, Sai dai a duk sanda suka kammala baya nuna wata kulawa ko yabawa kamar yadda ya saba mata a baya, Yau ma hakan ne yana samun natsuwa ya fice d'akin, "Tabbas Yaya Mu'azzam baya sona yanzu, sha'awata yake sai babyn sa dake jikina shine kulawar" Ta fad'a a raunane, Tare da d'aga hannayen ta sama ta rok'i Allah.

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now