HS 19

80 20 1
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na sha Tara

Hakimce take kujerar falo cikin isa da tak'ama wanda take jin jinin sarauta na yawo a jikin ta, Sallamar Mu'azzam ta amsa tana maida dubanta k'ofa, Cikin natsuwar sa da kamala ya shigo falon wanda shima idan baka fahimce shi ba zaka ce yana da girman kai duba da yadda yake abu komai cikin natsuwa da girma, Mu'azzam ko kad'an baya son raini hakan yasa baya shiga abunda bai shafe shi ba,

A ladabce ya gaishe da Hajiya, Ta amsa tana d'aukar remote gefen ta ta rage k'arar tv, Hankalinta ta mayar kansa ta kira sunan sa "Mu'azzam" cikin murya mai amsa amo, "Na'am" Ya amsa, "Sai yaushe zaka farka daga mummunan mafarkin da kake, sai yaushe zaka wanke yanar dake cike da idon ka wacce ta hana maka gane gaskiya kake kallon komai baibai", Shiru yayi zantukan nata na sosa ransa ta yadda baya jin dad'in su, "Miyagun k'wayoyin da aka saka booth na motar ka babu wanda zai aikata haka sai makusancin ka, yanzu kud'i cikin dak'in ka shima ba wanda zai yi haka sai makusancin ka, shin wa kake tunanin zai je har gidan ka ya saka ba tare da an ganshi ba, wake da access na d'akin ka, ka zauna kayi nazari mai kyau ka gane mak'iyan ka ne kewaye da kai ba masoya ba", Mu'azzam jikinsa ne yayi matuk'ar sanyi yayin da zantukan Hajiya ke kai kawo zuciyar sa, Tabbas idan an duba maganarta gaskiya ce, makusancin sa zai aikata haka amma waye?", "Shatu" Ya tsinkayo muryar Hajiya wanda bai san kalmar waye ta fito fili ba, A razane ya kalli Hajiya, Kai ta jinjina masa alamar tabbas,

Girgiza kai yayi da cewa "Shatu ba zata tab'a aikata haka ba, wallahi ba zata yi haka ba", Dogon tsaki Hajiya tace "Bansan yaushe ka koma sakarai ba wallahi, wanda ya d'auki yarda da amana yaba mace, ko da yake ban ga laifin ka ba ba banza aka bar ka ba, amma nice nan zanyi maganin komai", "Hajiya Dan Allah ki daina munana zato akan Shatu, wallahi mutuniyar kirki ce", "Dalla can rufe mun baki, ai ba'a barka a hankalin kan ka ba", Mu'azzam sunkuyar da kansa yayi k'asa zuciyar sa na zafi, Ba abunda yake k'auna a rayuwar sa irin SHATU, ya yarda cewa soyayyar da yake mata daga Allah ce shi ya dasa mishi ita cikin zuciya da ruhin sa, baya k'aunar a aibata ta ko a danganta da wani mummun wani abu, "Tashi ka tafi" Cewar Hajiya a hasale, "Sai da safe" Ya fad'a yana mik'ewa, Uwa uwa ce ko da kuwa mahaukaciya ce, ya zama dole ya darajata ya bata girman ta da matsayi da Allah yace, banda haka ba zai tab'a d'auka tana aiba ta masa SHATU,

**********************************

Na'ima na kwance d'aki tana waya da masoyinta Farouq cikin shauk'i, Jin shigowar mahaifiyarta tayi saurin kashe wayar tana cusawa k'ark'ashin pillow, "Sarkin kwanciya tashi" Anty Sahura ta fad'a tana kunna globe na d'akin, Na'ima ta tashi ta zauna bakin gado, Anty Sahura ta zauna gefen ta,

"Naga kin shantake kwata kwata bakya bada wata gudunmuwa ko himma kan auren ki da Mu'azzam", "Mama ai na bar komai ne a hannun ki", Anty Sahura harararta tayi tace "Matsalata dake sakarci duk doloncin yan' fari yana kan ki, ko zan miki yak'i ya zama dole kema kiyi k'ok'arin farautu soyayyar sa", "Mama baya bani fuska, wallahi baya gani kowa sai shegiyar can", Anty Sahura taja numfashi tace "Da sannu zai gwammace ganin bak'in maciji a kan ta, sai na doshe tauraron Shatu a zuciyar Mu'azzam wallahi,  na dasa taki", "Anya Mama akwai abunda zai saka k'iyayyar Shatu a zuciyar Yaya Mu'azzam kuwa", "Ki zuba ido kiyi kallo, yanzu naki ki cigaba da k'ok'arin farautar soyayyar sa", Tace "Tohm Mama", "Yawwa gobe ma ina so kije ziyara gidan amma ki tabbatar da lokacin da yake nan", "Mama ina tsoron wulak'ancin sa", "Zaki je a matsayin kin kawo musu ziyara amma ki d'auki ado mai d'aukar hankali", Tace "Toh" k'asan zuciyarta tana jin kamar ba mai wuya ba ne, Tsawon shekarun baya ba kalar adon da bata masa ba amma daidai da rana d'aya bai tab'a nuna yasan tana yi ba, ta rasa wane irin so yake wa Shatu, tabbas kam sai aikin asiri, Anty Sahura na fita,

Ta jawo wayar ta sake kiran Farouk, "Mama ce ta shigo kan maganar aurena da Yaya Mu'azzam", "To ya ake ciki an kusa ne", Farouk ya fad'a da murna, "Wai kai meye damuwar ka da aurena da Yaya mu'azzam har kana murna", "K'aruwar muce duka", "Taya aurena da Yaya Mu'azzam zai zama k'aruwar ka, ina ce ma sai dai ka shiga bak'in ciki na rasa ni, na zama mallakin wani", Murmushi yayi wanda ta jiyo sautin sa ta waya yace "Babyna kenan a sannu zan fahimtar dake komai, yanzu dai kimun kisses guda goma", "Uhmm" ta fad'a cikin shagwab'a, "Please mana babyna", Kisses d'in ta soma masa, suka tsunduma zantukan su na soyayya.

*******************************

Mu'azzam ko kusa bai bari Shatu ta fahimci magana mara dad'i ya tarar wurin Hajiya ba, Chocolates kala kala ya tsaya ya siyan mata a shopping mall kana ya dawo gida, Ta tarbe sa cikin far'a, Ya sumbaci goshin ta ya kama hannun ta zuwa ciki, Sai da suka zauna kan kujera ya mik'a k'atuwar ledar, Ta karb'a tana dubawa, Baki ta d'an bud'e ganin yawan su, Tace "Ni dawa Ruhina", "Ke da cikin ki", Dan' jim tayi tana jin ina ma ace tana d'auke da juna biyu yace "Ita da babyn cikin ta", "Ya dai" Ya fad'a yana d'aga mata gira, Murmushi tayi tace "Kawai mamakin soyayyar da kake nuna mun a kullum nake", "Ki daina mamaki dan Allah ne ya dasa mun masifar k'aunar ki", "Kamar yadda ya dasa mun naka a cikin nan" Ta nuna zuciyar ta, "Ke zuciya kad'ai ni duka ruhina", "Ba wani", "Allah", "Ai zuciyar kika ce" Ya fad'a yana dariya, "Allah duka ruhina komai nama", Dariya yayi zuciyar sa na k'ara gaskata masa Shatu ba zata tab'a aikata haka gare sa ba.

********************************

Dandazon yan' mata ne birjik a falon kallo d'aya zaka musu kasan sun gogu da bariki, Dan babu mai shigar arzik'i cikin su,

"Wai ke duk kud'in mahaifin ki da zuri'ar ku amma kina kwalta", Cewar d'aya daga cikin su tana duban Halima, "Saky kenan ba zaki gane ba, kud'in da ba cin su ake ba, ai tunda kika ga na fito bariki babu ce tasa", "Toh Allah ya rabamu da dukiya irin wannan", Halimatu tace "Amin fah", "Kinsan fah akwai appointment d'inki da Alhaji Gambo ki tashi muje", "Da wuri haka", Saky tace "Gara na kai masa ke da wuri yaji dad'in mun sallama mai kyau", "Shegiya k'awata" Halimatu ta fad'a suna yin shewa.

************************************

Sigarin ce rik'e hannun sa yana busawa har ta hanci, idon sa sunyi ja alamar yasha da yawa, "Mutumina ka sassauta sigarin nan haka", Cewar Abokin sa, Bashar sai da ya k'ara zuk'a yace "Barni nasha anan kad'ai nake samun damar sha", "Shege nawan baka da kyau wallahi", Wata dariya yayi yace "Kai dai Allah ya ka damu ga harawa zanyi bura uba a garin nan", "Mu dai kada a manta damu", "Kune na amanan tafiyar ai ba zatayi ba daku ba", "Nawan nawan kace zamu fantama", "Fad'a ma b'ata baki ne", "Ya maganar wancan Mu'azzam yake ko wa", "A sannu zan b'atar da sunanshi wallahi", "Kai ne ka tsaya wasa ai, mu da tuni ka bamu dama mun gama masa aiki", "Ba mutuwar sa nake so, nafi so yana raye amma ya zama abun tausayi ba'a gani ko jin kowa sai ni", Jinjina kai yayi yace "Nawan nawan Ina yin ka", Bashar yayi dariya.

Am so occupied zaku ga typing din kwanakin nn ba yawa
Sai kunyi hakuri kafin na dawo daidai In shaa Allah

OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now