HS 26

96 17 7
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na ashirin da shida

Gani da jin Mu'azzam ya d'auke na wucin gadi, tamkar iskar guguwa haka yaji komai na juya masa fad'uwa yayi a wurin, Hankalin mutanen wurin ya dawo kansa, wanda mafi yawa daga ciki kuka suke na rashin Allah, Hatta Kawu Kabiru dasu Lamido jin mutuwar lokaci d'aya ba k'aramin girgiza su yayi ba, Lallai rai bak'on duniya haka idan mutuwa zata d'auke ka bata shawara da kai lokaci d'aya zak tsinci kanka a kabari,

Take gari ya d'auka da mutuwar Alhaji, mutane da dama sun ji mutuwar sa yayin da suke fad'in anyi babban rashi da mutumin kirki,

Umma da labarin mutuwar yazo mata sai Allah ya sauko mata wani hak'uri da dangana, "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ta dinga nanatawa, zafi da rad'adin dake zuciyarta ya haddasa mata kukan zuci, wanda yafi hawaye ciwo, Hajiya Hafsatu kuwa ihu ta dinga yi tana fad'i k'asa tana cewa "WAYYO Alhaji shikenan ya tafi ya barmu, wayyo ni Allah wayyo kaina", Sahura ce ta dinga lallashin ta, Su Maimuna ma tuni suka hallara gidan suna kuka tamkar ran su zai fita, tabbas sunyi babban rashi na uba nagari,

**********************

A hankali ya bud'e idon sa wanda yake jin tamkar an zuba masa barkono tsabar yaji, Yatsun hannayen sa da yaji sark'afe cikin na wani yasa ya kalli gefen sa, SHATU ce rik'e da hannun sa, ta sunkuyar da kanta gefen gadon hawaye na ambaliya saman fuskar ta, Tukur yasa aka d'auko ta aka kawo ta, "Shatu na" Ya kira sunanta cikin raunannan murya, Saurin d'agowa tayi ta kalle sa da idonta sukayi jajir tsabar kuka, "Da gaske ne mun rasa Alhaji?", Kasa bashi amsa tayi ta sunkuyar da kai k'asa wasu hawaye masu zafi na wanke fuskar ta, tabbas tayi rashin uba dan tun tashin ta Alhaji ta sani matsayin uba, bata san mahaifin ta ba,  ya maye mata gurbin da sam batayi maraici ba, ya mata dukkan hidima da gata da uba ke ma yar' sa, zata iya cewa Alhaji ya zamar mata babban bango na majingina ta tabbata ko yaran da ya haifa da cikin sa ba zasu fi ta jin rad'ad'in rasa shi ba sai dai su zo d'aya idan bata fi su ba,

"Allah ya jik'an Alhaji ya mishi rahama, Allah ya bashi ikon amsa tambayoyin kabari", Mu'azzam ya fad'a cikin tsananin rauni, ji yake ya rasa wani babban b'angare na rayuwar sa, Shatu cikin shesshek'ar kuka tace "Amin Ya Allah", "Ki daina kuka Shatuna, Alhaji addu'ar mu yake buk'ata", K'ok'arin tsagaita kukan nata tayi, Drip dake hannun sa ya fisge da cewa "Tashi mu tafi ina son halartar jana'izar Alhaji", Bata ce komai ba sanin ya kamata ya halarta d'in,

A passage suka ci karo da Dr zai zo duba sa, "Ah Mu'azzam ya ka taso", "Am sorry Dr amma halartar jana'izar Alhaji itace kan gaba", "Shikenan Allah ya k'ara sauk'i", Bai tsaya amsa Dr ba yaja Shatu suka wuce.

*****************************

Tun daga kan layin gidan motoci ne wanda unguwar ta cika mak'il, mai bolt da ya d'auko su Shatu dole ya ajiye su kan layi, Shatu hijabin ta taja ta rufe fuskar ta, suka soma ratsa dandazon mutane da motocin dake cike layin, "Alhaji yayi mutane" cewar Shatu a ranta, ko dan halayyar sa ta gari da taimakon mutane dole yaga jama'a, Mu'azzam yana ta k'ok'arin kare fuskar sa kada mutane su ganshi su tsayar dasu, har sai da ya kai Shatu k'ofar da zata sada ta da sashen UMMA, Dawowar sa cikin mutane yayi daidai da fitowar gawar Alhaji, Kansa yaji ya mugun sara masa ya k'ara tsinkewa da lamarin duniya, Yau Alhaji ne kwance cikin makara babu bakin yin magana balle k'afafun tafiya, Lallai dan' adam ba bakin komai yake ba, haka duniya zancen banza, duk kud'i mulki da tak'amar ka k'arshen ka likafani, Ya tuna maganar su ta k'arshe da Alhaji da yake cewa ya sanar da mutane su d'aga zuwan su jibi, kowane rai yana mutuwa da buri, Alhaji bai kawowa kansa mutuwa yau ba, gashi cikin k'ank'anin lokaci Allah ya d'auki abun sa, Ya kamata mutuwa ta zamar wa mutane wa'azi,

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now