HS 09

103 23 0
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na Tara

"A duka gwaje gwajen da mukayi sakamako d'aya yake bayarwa shine kuna d'auke da lafiya bakwa tare da wata matsala", Mu'azzam ya katse Dr da cewa "Amma how is that possible Dr, tsawon shekaru hud'u da auren mu bata tab'a conceiving ba", Gyara zama yayi sosai yana duban Mu'azzam yace "K'warai hakan na faruwa, sau da yawa ma'aurata kan d'auki lokaci basu haihu ba, ba dan suna da wata matsala ba sai dai Allah ne bai kawo lokacin haihuwar ba, Ni musulmi ne kai ma musulmi ne ya kamata mu yarda tsari ne na ubangiji, shi ke halittar mutum a cikin mahaifiyarsa a lokacin da yaso", Mu'azzam numfashi yaja yace "Hakane amma Dr ba wani taimako da zaka iya bamu da maybe zai taimaka tayi conceiving da wuri", Kai ya girgiza yace "Da akwai wata matsala ne tare daku shine zan iya d'aura ku kan medication but dukkan ku kuna da lafiya, sai dai ku jira zuwan haihuwar daga ubangiji", SHATU tun fara bayanin Dr jikinta ya sake yin sanyi, ta yarda da ubangiji ke bada haihuwa a lokacin da yaso ga wanda yaso, Sai dai ta rasa dalilin da zuciyarta ta kasa natsuwa tana ganin kamar akwai abunda likitocin ke b'oye musu basa son sanar dasu, Tsawon shekaru hud'u bata tab'a ko da b'arin wata ba kuma ace babu matsalar komai, "TSARIN UBANGIJI NE" Cewar wani sashe na zuciyarta, K'ok'arin kwab'ar kanta tayi daga sak'e sak'en dake kai kawo zuciyarta tana ganin rashin dacewar hakan da tamkar shiga hurumin ubangiji ne, FOLIC ACID supplement ya rubuta musu kan cewar Shatu ta rik'a sha, Sukayi sallama da Dr suka fito ofishin sa, Shatu k'asan zuciyarta tana jin rashin dad'i na mak'udan kud'in da aka kashe zuwan su, asibitin kanta tsadaddiya ce a garin, tana ganin anyi asara ne kawai ba tare da an samu wani cigaba ba, Mu'azzam ya lura da k'ara sanyin ta bai ce mata komai ba, Taxi ya d'auka musu zuwa wani had'adden restaurant, Ganin direban yayi parking bakin wurin ta kalli Mu'azzam alama ya mata da ido su sauka, Yana kama hannun ta,

K'eb'antaccen wuri da babu taron mutane, ya samar musu suka zauna, Abinci iri d'aya ya saka musu order, Wanda cikin mintuna biyar aka kawo, "Feed me" Ya fad'a yana mata narkakken kallon sa, Waigewa tayi gefenta ganin babu mai kallon su, Ta d'auki cokali ta soma d'iba ta kai bakinsa, Shima ya soma feeding d'in ta, Vibrating wayar sa dake gefe ta soma, Ya kai dubansa sunan HAJIYA ne bayyane kan screen, Take yanayin fuskar sa ya canza, yasan rashin kiran nata ta biyo jin ba'a si, tamkar zai share tuna rashin d'aukar bashi ne mafita ba, ya danna receive,

"Da alama agola tafi mahaifiyarka muhimmanci da zata sa ka manta da kiranta", Har cikin ransa yake jin zafin yadda Mahaifiyar tasa bata k'aunar abu mafi soyuwa gare shi, ko dan soyayyar da yakewa SHATU ya kamata ace ta ajiye kishi ta k'aunace ta, "Kiyi hak'uri Hajiya", "Kalmar kenan Hak'uri ka zama saltacce sai yadda akayi da kai, ya kamata ka bud'e ido ka gane komai, ka fuskanci mak'iyanka ne kewaye da kai ba masoya ba", Tana fad'a ta datse wayar, "Tabbas maganar Sahura gaskiya ce asibiti sukaje, ban da haka banga dalilin Mu'azzam na kasa kirana", Ta jinjina kai "Wallahi wallahi wallahi Umma baki isa ba, burinki ba zai tab'a cika ba, nayi wahalar daukar ciki wata tara na kawo sa ido ki fini morar sa, over my dead body" Ta fad'a tana yarfa hannu,

**************************

Mu'azzam haka suka cigaba da cin abincin ba dan yana jin dad'in sa ba, Shatu ta lura da sauyin yanayin sa tasan tabbas yana da alak'a da wayarsa da hajiya, lokuta da dama yana bata tausayi sosai tana danganta kanta da shiga damuwar sa, tana ganin tun shigowar ta rayuwar sa bai k'ara samun daidaituwa tsakanin sa da mahaifiyar sa ba, Babban burinta bai wuce na ganin kyakkyawar mu'amala ta cigaba da wanzuwa tsakanin sa da mahaifiyarsa, "Sai yaushe hakan zata kasance?", Ta tambayi kanta, "Sai bakya cikin rayuwar sa" Zuciyarta ta bata amsa, Mummunan fad'uwar gaba yayi tayi saurin watsar da tunanin, Duk abunda zai rabata da Mu'azzam bata k'aunar sa ko kad'an, ya zama wani sashe na rayuwarta wanda bata jin rayuwarta zata daidaita ba tare dashi ba, farin cikinta da samun natsuwarta mu'azzam na tare da ita,

Sha biyu da mintuna na rana suka shigo hotel, lokacin su na sallah yayi, Kai tsaye band'aki Mu'azzam ya fara shiga ya d'auro alwala, Kana itama ta shiga tayi, Shi yaja su sallar azahar, Bayan sun kammala suna zaune kan sallaya, Ta d'aura kanta kan kafad'ar sa tare da rik'e hannun sa tana lazimi dashi, Lokuta da dama haka take yi a cewarta su samu ladar tare, Bayan ta kammala tafin hannun sa ta shiga shafawa tamkar mai tafiyar tsutsa, Sosai yake jin dad'in hakan, Cikin sanyin murya tace "Am sorry Rouhina", "Sorry kuma SHATUNA", Kai ta d'aga masa alamar eh, "Me ya faru?  bansan kin mun wani laifi ba", "Sanin damuwata yasa ka jajirce kan zuwan mu germany duk da Alhaji ya kawo shawara, amma ka k'ara k'arfin gwiwa ne saboda ni, gashi asarar ku....", Hannu yasa kan bakinta, Fuskar sa na nuna b'acin rai kafin taga yanayi irin haka kan fuskar sa ana jimawa, "Ban tsammaci jin haka daga bakin ki, dukiyata da kaina gaba d'aya mallakar ki ce SHATU, ko da komai nawa zai k'are a kanki ba asara ba ce, face HALACCIN SO, duk abunda na mallaka bai kai kwatankwacin darajarar ki a wurina, ya zama na farko na k'arshe da zaki k'ara danganta wani abu da na miki asara", Girma, matsayi da soyayyar Mu'azzam taji ta sake shiga zuciyar sa, hak'ik'a tayi dacen miji nagari me zata cewa ubangiji banda godiya, "Alhamdulillah nagodewa Allah da samun miji irin ka YAYA MU'AZZAM" Ta fad'a tana masa kallo mai cike tsananin so da jefa zuciyar wanda ake ma cikin shauk'i, B'acin ran yaji na barin sa a hankali, Yayin da yake jin abu na tsirgar masa, Hannun sa ya zura cikin rigarta da ta bud'e ta sama, Lafe masa tayi tana jin dad'in yadda yake sarrafa dukiyar fulanin ta, "SHATUNA" Ya kira sunanta da muryarsa data soma canza sauti, "Na'am" Ta amsa itama tata ta sauya, "Ina son komai naki, komai na jikin ki abun burgewa ne da so", Narkewa tayi jikinsa cikin farin cikin yadda baya tab'a kushe komai nata sai dai yabawa, hakan ke k'ara bata k'arfin gwiwar sake gyara, Sosai suka jagalgala juna kafin suka lula duniyar ma'aurata cike da marmarin had'i da gamsar da juna.

**********************************

"Baban Zulfa magana nake tun d'azu" Cewar Shema'u cikin magiya, Hannun babbar rigar sa d'aya ya gyara, Ya tsaya bakin k'ofa cikin masifa yace "Ban tab'a ganin mace mai rainuwa irin ki ba wallahi, tsabar rashin godiyar Allah d'ari biyar fah na baki", "Haba Baban Zulfa kasan fa muna da yawa, kuma yau na fad'a maka za'a yi bak'i ya kamata asa nama", "Ke bana son salo kinji ko, su bak'in basu san babu bane, bani dasu ba zan kashe kaina dan burge wasu ba, dan ma bance ayi fara da mai ba", Ya bula babbar rigar sa yayi gaba, Shema'u tabi bayansa da kallo cike da takaici halin mak'o da rowar sa, duk irin dukiyar da Allah ya basa, iyalansa basu shaida ba, hatta kud'in cefane kullum sai anji kansu, abinci da nama kuwa ba maganar sa, Yau ma yan' uwanta da zasu zo daga garin su yasa ta mishi magana, Haka ta dawo ciki rai jagule, ZULFA dake kwance kan doguwar kujera tana matsa waya tace "Mama Dan Allah idan kina da kud'i ki bani na siya littafan makaranta na fad'awa Baba yace bashi dasu", Shiru Shema'u tayi cikin takaici, Yara uku kad'ai Allah ya basu tare Bashar, Halima sai Zulfa amma baya iya d'aukar d'awainiyar su wanda ko gidan yawa sunfi su jin dad'i,  Duka yaran akwai tazara sosai tsakanin su, Kawu Kabirun ya nuna baya son haihuwa da yawa, hakan yasa tun lokacin ya sata yin family planning wanda yake ganin tara yara zai k'ara masa hidima, baya son kashe kud'in sa ko kad'an burin sa kullum ya tara dukiya,

*******************************

"Kana da labarin ya tura Mu'azzam da matarsa wani aiki k'asar germany" Cewar Lamido fuskar sa zallar hassada, Kawu Kabiru mik'ewa yayi daga zaune da yake yace "Yaushe, aikin me ya tura shi", "Ina zamu sani tunda mu an mayar damu yan' kallo, bamu da amfani", "Jar' uba wallahi bazai yiyuwa ba ya zama dole mu d'auki mataki da gaggawa", "Zancen ka haka yake matuk'ar bamu tashi tsaye ba wallahi za'ayi bamu, amma yanzu meye abun yi?", Kawu Kabeeru waigawa yayi gefe da gefe ya tabbatar ba kowa kana ya rad'a masa zance a kunne, "Kaii amma ka kawo shawara hakan kawai za'a yi", Kawu Kabeeru yayi dariyar mugunta, Babu komai cikin zuciyar sa sai zallar hassada da bak'in cikin MU'AZZAM, Yana jin shi ya cancanta a tura k'asar germany, kafin Mu'azzam d'in yazo duniya duk wani aike ai shi Alhaji ke sawa, sai yanzu ne zai nuna son kai, bazai tab'a bari hakan ya cigaba ba, Ya ba kansa tabbaci cikin zuciya.

*****************************

Manne suke jikin juna, kowanne yana jin d'umin jikin d'aya, Hannayen sa zagaye da ita, Yayin da  ta lafe sosai a jikin sa, "A duk sanda nake jin d'umin jikin ki na kan tsinci kaina cikin natsuwar zuci", "Ni kaina bazan iya misalta yanayin da nake ji ba" Ta fad'a tana shafa sajen sa, "Allah yasa mu kasance da juna har abada", "Amin" Ta furta tana sake shigewa jikin sa wutar son sa na rurawa a zuciyarta, "Me zan samu to" Ya fad'a cikin wani salo yana zuba mata mayun idon sa, "Babu" Ta fad'a cikin zolaya, "Uhmm baki isa ba", Ya fad'a yana zuge zip na bayan rigarta, tare da b'alle bra d'in ta, Bata hana sa ba, Sai ma bakinta da ta kai wuyan sa ta soma sumba, Suka shiga jagalgala juna cikin yanayi na tsananin k'aunar juna kowane yana ji tamkar ya had'iye d'aya.

OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now