HS 47

96 18 8
                                    

HALACCIN SO
Zee Yabour
*47*

Iskar hancinta ta sake ja dan son tabbatar da abunda hancin ta ke juyo mata, Warin sigari take ji duk da ya gauraye da k'amshin room freshner, "Me zai kawo warin sigari nan? Yusrah ta tambayi kanta wacce ta shigo wanke band'aki kamar yadda take bayan kwana biyu kasnacewar ba kasafai ake amfani dashi ba, bata masu aiki su shigar mata d'akin miji, "Watak'ila daga waje ne ya shigo ta window". Tacewa kanta ko kusa bata kawo zargin Bashar ba, ta bashi yarda sosai ta yadda ko sau d'aya zargin sa bai tab'a zuwa ranta ba, ya toshe duk wata mafaka ta zarge, Wankin band'aki tayi tare da gyaran d'akin ta fice.

BAYAN WATA BIYU

A cikin watanni biyun Ibrahim yayi nasarar shawo kan Shatu ta hanyar kyautatawar sa da nuna mata tsananin k'auna, kowa a ahalin sa yasan Shatu kuma kowa k'auna yake nuna mata, Takanas yaje har kano ya gaishe da Umma, Ranar ta kirata ta mata nasiha sosai, da nuna mata Allah ya dubeta ya musanya mata Mu'azzam da wani, Kar ta butulcewa ni'imar Allah ta hanyar k'in yin aure bayan shine martaba da darajar mace, Sosai nasihar ta shige ta haka bata jin zata k'ara bijirewa umarnin mahaifiyarta, da kuma duba da yadda ahalin sa ke nuna mata k'auna tun kafin auren sab'anin ahalin Mu'azzam da basu tab'a k'aunar ta ba, Ta b'angare d'aya IYA ma ta saka mata wuta kan dole sai ta auri Mu'azzam har tana ce mata yar' bak'in ciki bata so Ibrahim ya cigaba da alkhairin da yake mata, ita kam mamakin son kud'i da rashin godiyar Allah irin na IYA take, D'awainiyar su da cefanen gidan duka UMMA ke yi, ko tsinke bata bari su siya ita ke bayar da kud'in, amma ba zai hana IYA kiran bata dashi ba, Shatu a kullum tana ma Allah godiya da ya bata mahaifiya irin UMMA tun rabuwarta da Mu'azzam bata barta tayi rashin komai ba ta jajirce kan lamuran ta, Ibrahim mutum ne mai kyauta wanda Shatu a ranta ta ayyana watak'ila daga masu sunan ne duba da Mu'azzam shima yana da tsananin kyauta,

Ibrahim kullum cikin mata d'awainiya yake har kunyar sa take ji, Haka su Jummai baya gajiya da basu kud'i, IYA ma duk yazo sai ya mata alkhairi hakan ke sa tana k'ara son auren su da Shatu, Tuni ta sanar da k'annen mahaifin Shatu ta samu wani miji, ko da aka zo neman aure babu ja suka yarda, aka saka biki sati biyu masu zuwa, dan Shatu ta nuna mata son hidimar biki a d'aura aure kawai, Shi kanshi Ibrahim ya k'osa ta zama mallakin sa gudun ta sub'uce mai.

**************************

Zaune take d'akin INNA tana bin tulin kayan matan da  Gwaggo Jamila ta kawo mata, "Kin tsaya kina kallon su maimakon naga kin fara k'ok'arim sha". Dariya tayi tana duban Gwaggo Jamila tace "Ina mamakin ina zan kai su". "Ah lallai ba fah auren fari bane, kin ga kuwa dole ki zage damtse kiyi gyara da kyau, yadda zai kasa tantance ba budurwa ba ce". Murmushi kawai tayi a ranta tace "Ai an bar gini tun ran zana, budurci kam ya tafi sai yan dabaru". Gwaggo Jamila ta jawo wani k'aton galoon na tsumin tabaje, ta zuba mata a kofi tace "Karb'i ki shanye, sai kin kwana biyu a gidan mijin ma na d'auke ki muje wurin Zee Yabo ta had'a miki supplements masu masifar kyau da zaki rikita shi". Ita kam Shatu Gwaggo Jamila kunya take sata, Hakanan ta karb'i tsumin ta sha, tana d'an yatsina fuska saboda baurin sa.

************************

Ta b'angaren Mu'azzam ya sake maida hankali sosai kan neman halal d'in sa, ko kusa bai yarda ya had'a neman sa da haram ba, shine Allah ke k'ara bud'a mishi ta kowacce hanya, yana yawan sadaka kamar yadda idan kana sadaka dukiyar ka bata k'arewa sai dai ta k'aru, sai abu na kan gaba addu'a baya wasa da ita wanda ta zame masa wata katanga daga duk sharrin su Kawu Kabiru wanda a kullum suke fara shiryawa yana warwarewa, Kowannen su da bak'in cikin Mu'azzam yake kwana yake tashi, gashi yak'i sake musu ko kad'an daga cikin sirrin kasuwancin sa, Duk iya wayo da dabarar Kawu Kabiru jiya iya yau, Mu'azzam sai ya b'ullo da wata hanya da zai tare sa,

****************************
*10 ga watan Rajab*

A kowacce shekara Mu'azzam yake fitar da zakka, Gaba d'aya plaza cike take da bayin Allah masu karb'ar zakka, yawan kud'in dasu Kawu Kabiru suka ga yana rabawa ya matuk'ar d'aga hankalin su,

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now