HS 11

106 20 2
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

Shafi na sha d'aya

Mu'azzam yayi saurin bata kariya ta fad'a kan fad'add'an k'irjinsa, a take ta saki kuka mai sauti, kuka ne na bak'in ciki da damuwa wanda yake taho mata tun daga zuciyarta zuwa mak'oshin ta, Hannayen sa biyu ya zagaye ta dasu, Wani turnak'ak'i zuciyar sa ke yi har tsakiyar kansa yake jin kukan ta, Ina ma yana da damar tsayar da dukkan damuwa had'i da cin zarafin da ake mata, Sai dai yana fitowa ne daga mutum mafi daraja a rayuwar sa, bashi da iko ko katabus na yin komai, Shesshek'a da sautin kukan ta ke tab'a zuciyar sa yana jin wani zafi ba zai iya jure saurare ba, A hankali yaja ta zuwa d'an k'aramin lungu na wurin, Duk'ar da kansa yayi kad'an saitin kunnen ta cikin wata irin murya mai nuna tsantsar damuwa da sanyi yace "Kina azabtar da zuciyata da kukan ki SHATUNA, ki taimakeni ki daina", D'if tamkar d'aukewar ruwan sama ta dakatar da kukan, sai hawayen da basu fasa zuba ba, D'ago da kanta yayi ya saka hannun sa masu laushi yana share mata hawaye, "Kiyi hak'uri SHATUNA, bani da iko na hana hakan faruwar da tuni na dad'e da k'watar miki yanci, na dad'e da nuna muhimmanci da matsayin ki, sai dai bani da damar hakan" Ya k'arasa cikin zallar takaici, K'ok'arin danne hawayen take bata k'aunar ganin damuwa tare da shi, Murmushi ta aro ta saka kan fuska duk da yadda k'asan zuciyarta ke zafi kalmar JUYA na mata kai kawo, A zahiri tace "Kasancewar ka cikin rayuwata kad'ai ya isheni farin cikina, lallashin ka gareni ya kawar da duk wata damuwa had'i da b'acin rai", "Kin tabbata SHATUNA" Ya fad'a yana kallon k'wayar idon ta, Murmushi ta sake yi tace "Eh Farin cikina", Hancinta yaja kad'an tare da mata light kiss, Fuskarta ya k'ara gyara mata yadda UMMA ba zata fahimci tayi kuka ba, Har k'ofar sashen UMMA ya mata rakiya, "Zanje wurin ALHAJI idan na gama zan shigo" , Tace "Toh" Tana wucewa ciki,

Ba kowa a falon sai k'ira'ar SUDAIS dake tashi a tashar  QUR'AN TV, Tsaye tayi tana sauraren karatun dan samun natsuwar zuciya, Na tsawon minti biyar ta saurara amma ya tafi da b'acin rai mai yawan kaso daga zuciyarta tabbas QUR'ANI waraka ne, Tafin hannun ta tasa ta k'ara gyara fuskar ta, Kana ta nufi hanyar bene, Falon sama ta same su, Suna hira da UMMAN cikin raha, "Yau zaman falon sama kuke" Cewar Shatu tana duban Farha wacce ta taso ta k'ak'abe ta, "Da mukayi sallah shine muka zauna anan" Cewar Farha, "Umma ina wuni?" Shatu ta gaisheta cikin ladabi, "Lafiya lau mutane germany", Zama tayi kan kujera tana ajiye handbag d'inta gefe, "YAYA Shatu sannu da zuwa", Cewar Teema dake rik'e da k'aramin littafi na addu'a, "Yawwa Teema", Shatu k'ok'arin jawo hira tayi tsakaninta da k'annenta dan k'ara ragewa kanta damuwa, Sai dai kalmar JUYA ta kasa daina mata yawo a kai, A saninta kalmar juya na nufin wacce bata haihuwa kwata kwata, meyasa Anty sahura zata kirata da hakan, bayan likitoci sun shaida lafiya take lokacin haihuwar ne bai yi ba, meyasa ita kad'ai ta danganta da juya ba tare da Mu'azzam ba ko dai kalmar juya yana da ma'anoni daban take zancen zuci, Yayin da zuciyarta ta bata tambayar UMMA, Cikin sanyi murya tace "Umma Dan Allah me kalmar JUYA take nufi?", Umma jim tayi tana nanata kalmar a ranta ko shakka babu wani ya kira SHATU da kalmar shiyasa take tambaya, ranta taji ya sosu a zahiri tace "Meyasa kike tambaya SHATU?", "Uhmm kawai ina son ji ne Umma", Babu fa'idar yi mata k'arya fad'a mata ma'anar shine daidai Umma ta ayyana a ranta wanda ta soma tunanin canza ma'anar gudun jefata damuwa, 

"Yana nufin wacce bata haihuwa" Umma ta fad'a ba tare da ta k'ara da komai ba, duk da k'asan zuciyarta tana jin tamkar ta tambayi Shatun dalilin tambayar sai dai tuna alwashin da ta d'aukarwa kanta na gunewa jin duk wani abu na rashin dad'i a rayuwar auren Shatun yasa tayi shiru,

Shatu ranta ya k'ara sosuwa sosai kalmar na sake mata zafi, Tayi k'ok'arin b'oyewa hakan kan fuskarta, UMMA tuni ta d'ago yayin da ta sake jin tausayin yar'ta ya shigeta, "Allah ya kawo sauyi rayuwar Shatu" Tayi addu'ar cikin zuci, ko kad'an ba irin rayuwar auren tayi mata sha'awa ba,

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now