HS 21

120 20 6
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na ashirin da d'aya

"Lissafin namu daidai ne, container hud'u suka zo cikin satin nan", Alhaji Hali Inuwa ya fad'a yana duban Mu'azzam gefe d'aya Kawu Kabiru na hakimce, Mu'azzam ya numfasa yace "Sai container d'aya na Dubai lace", "Hakane na manta ban saka dashi ba", Kawu Kabiru yace "Ai shekarun ne sun ja, kana k'ok'ari ma wasu kamar ka suna gida suna hutawa sun bar wa yara", Alhaji Inuwa murmushi yayi yace "Gara dai a cigaba da lallab'awa", Kawu Kabiru yace "Allah yasa a raka lafiya", Alhaji Inuwa yace "Amin", Kawu Kabiru yaso cin galaba kan Alhaji kan ya tattara ya bar musu komai, Yadda cikin sauk'i komai zai dawo hannun sa, dan a ganin sa tarwatsa Mu'azzam k'aramin aiki ne, Tunda yaga shigowar Mu'azzam shima ya shigo da sunan gaishe da Alhaji, wanda yak'i tafiya ya zauna ana tattaunawa dashi,

"Ina ga idan za'a k'ara order china zai fi kyau muga zahiri", Alhaji bai gama rufe baki ba Kawu Kabiru ya karb'e da cewa "Haka ya kamata dan gani ya kori ji gara aje a gani a zahiri a duba yanayin quality su kafin a d'auka", Alhaji Inuwa ya jinjina kai yace "Mu'azzam sai ka shirya tafiya", Kawu Kabiru wani bak'in ciki yaji ya tsaya mishi  gudun Alhaji ya fuskanci wani abu ya hana mishi magana, Yana k'ok'arin danne bak'in cikin sa wanda yake jin tamkar ya rufe Alhaji da duka akan takaicin da ya basa, Bai k'ara minti biyar ofishin ba yace "Zai koma akwai customers d'in shi da zasu zo", Daga Alhaji har Mu'azzam basu fuskanci sauyin yanayin sa ba, Har bayan fitar sa suna cigaba da tattauna abubuwan da zasu k'ara bunk'asa kasuwancin su,

*******************************

"Allah yayi wadaran son kai da butulci wallahi", Kawu Kabiru ya turo k'ofa yana masifa, Lamido da Rabi'u a tare suka dube sa da jefa masa tambaya iri d'aya a tare
"Lafiya Kabiru?", "Lafiya ba zata tab'a tabbata a kasuwar nan ba matuk'ar Alhaji bai daina nuna son kai akan yaron sa ba", Rabi'u yace "Ni lamarin har ya daina bani mamaki, sai d'aure kai, dama ance so so ne amma son kai yafi, k'iri k'iri Alhaji ya wofantar damu ya kama dan' sa", Kawu Kabiru cikin zafin rai yace "Ku duba muna tattaunawa fah yace wai Mu'azzam ya tafi china wurin order kaya, a gabana bai yi kawaicin cewa naje ba, yau na k'ara shaida son kan Alhaji yayi yawa", Lamido yace "Tirk'ashi shirin mu ya zama na banza kenan sai ma k'ara tura shi k'asar waje", "Bazan tab'a gajiya ko sarewa ba har sai na cimma burina" Kawu Kabiru ya fad'a, Rabi'u yace "Burin ka ko namu", Kabiru sai yanzu ya ankara yace "Burin mu duk d'aya ne na ganin mun samu kaso mai tsoka bamu yi wahalar banza ba", Lamido yace "K'warai da gaske", "Ku matso da kunnen ku kuji", Maganar tsawo minti biyar ya rad'a musu, Suka d'ago suna jinjina kai cike da gamsuwa da maganar tasa,

***************************

Kawu Kabiru yana komawa gida ya buk'aci ganin Bashar, "Duk wani shiri na auren ku kayi sa cikin sati biyu kwanaki 17 masu zuwa Yusrah zata zama matar ka". Tsananin farin ciki ya bayyana kan fuskar sa yace "Toh Abba nagode", "Yadda na maka k'okarin kan auren nan kai ma ya zama dole kabi sharad'i na", Cewar Kabiru yana magana tamkar ba da dan' sa ba, Bashar kai ya jinjina yace "Toh Abba menene sharad'in", "Da sannu zaka sani, zaka iya tafiya", Yace "Toh" ya mik'e ya fita kwata kwata bai yi mamakin sharad'in mene ba, sanin tatsuniyar gizo bata wuce ta k'ok'i, Kawu Kabiru gyara zaman sa yayi kan kujera yana nazari tare da sak'a da warwara a zuciyar sa.

************************

Ayyukan yau sun so had'e mata saboda ciwon kan da ta tashi dashi wanda ke haddasa mata jiri, Jollof na shinkafa mai had'i da kayan lambu tayi, sai pepper soup na yan' ciki, Da k'yar ta kammala ta kunna burner turaren wuta, Ta koma d'aki kwanciya taji tana buk'atar yi hakan yasa ta kwanta, Tare da jan bargo ta rufa saboda yanayin garin na sanyi,

***************************

Tuk'i yake a natse yana sauraran karatun qur'ani wanda ke k'ara masa natsuwar zuci, Wayar sa tayi k'ara alamar shigowar text message, Ya jawota daga aljihun gaba ya duba, Bak'uwar lamba ce "Ka tsallake rijiya da baya", Ya maimaita kalmar ta kai sau biyar yana son gane mai take nufi amma ya kasa, Hakan yasa ya mayar da wayar aljihu yana cigaba da tuk'in sa, har ya kawo gida zuciyar sa cike da wasi wasin sak'on, 

Bai ga rabin ran tasa a falo hakan yasa ya nufi d'aki, Yayi mamakin ganinta kwance sanin bata bacci a irin lokacin nan, Bakin gado ya k'arasa, Saukar hannun sa kan wuyanta dan yaji lafiyar ta, Ya sata bud'e idonta dake lumshe tamkar mai bacci, "Shatuna bakya jin dad'i ne", Kai ta d'aga masa alamar eh, "Subhanallah meke damunki?" Ya tambaya cike da kulawa, "Ciwon kai da jiri", Mik'ewa yayi ya bud'e drawer da suke ajiye maganganu, Ya d'auko paracetamol, k'aramin fridge na d'akin ya d'auko ruwa marasa sanyi sosai, Ya zaunar da ita ya bata maganin ta sha, Ya kwantar da ita kan k'irjin sa, Yana shafa bayanta a hankali tamkar yana lallashin k'aramin yaro,

Sun jima haka tana jin ciwon kan na ragewa sosai, "Muje kaci abinci nasan kana jin yunwa kuma kada ka makara komawa kasuwa", Ta fad'a cikin kulawa, "Lafiyar ki tafi mun koma Shatuna", "Naji sauk'i" Ta fad'a, D'ago da kanta yayi ya kalli idon ta dan tabbatar da sauk'in, Ya hango sauyi tare da ita sab'anin d'azun, "Muje amma da sharad'in kema zaki ci", Kai ta masa nodding,

*********************

Shi yayi serving d'in su jollof d'in wanda yana bud'e warmer k'amshin ya cika mishi hanci, Ya kalleta da mata alamar yabawa, Tayi murmushi, Shi ke feeding d'in ta, Cokali na uku amai ya taho mata ta soma kwarawa tamkar zata amayar da yan' cikin ta, Mu'azzam ya rik'e ta yana jera mata sannu, Sai da ta gama ya bata ruwa ta sha, Ya kamata zuwa d'aki, Al'adar yan' aikin ce idan sun gama cin abinci suzo su kwashe kwanuka, su suka gyara wurin da tayi aman,

************
Tana kwance jikin sa ya shafa mararta da cewa "Ina ganin Allah ya dubi kukan mu ya bamu abunda muka dad'e muna nema", Da mamaki ta kalle sa, Gira ya d'aga mata yace "Yes ina kyautata zaton nayi ajiya anan", Murmushi tayi tace "Yaya Mu'azzam kenan daga d'an rashin lafiya sai hasashen ciki", "Toh ai baki tab'a irinta bane SHATUNA, kuma alamu ne na masu ciki, dama naga kwana biyu kina k'ara kyau", Ya kai hannun sa kan dukiyar fulanin ta yace "Nan suna cika", Shiru tayi a zuciyarta tana ayyana ina ma hasashen nasa ya zama gaskiya da ko shakka babu ta kwana k'iyamul laili tana godiya ga ubangiji, haka sai tayi azumi uku na godewa Allah, "Kinyi shiru Shatuna", Murmushi tayi tace "Allah ya bamu zuri'a ta gari mai albarka", Ya amsa da "Amin", Bai koma kasuwa ba, ya zauna gida yana tarairaiyarta tamkar likita ya basu tabbacin tana d'auke da juna biyu, Shatu kam har mamaki ya rik'a bata a zuciyarta tana raya ashe haka yake son haihuwa, b'oyewa kawai yake saboda damuwar ta, Ta k'ara shaida Mu'azzam ba k'aramin masoyi ba ne, mai HALACCIN SO gare ta, wanda a kullum yake saka damuwar ta a saman tasa.

*********************

Alhaji Inuwa ke ta faman kasa kayan neman auren Yusra, Umma ganin har ya gama bai cire na Hajiya Hafsatu ba, Cikin natsuwa tace "Alhaji baka cire na Hajiya ba", "Babu amfani tunda ta nuna bata buk'atar su", "Ba za'a yi haka Alhaji ba, watak'ila dai tana da wata manufa na k'in bari a kai sashen ta", Alhaji Inuwa kallon Umma yayi yana k'ara yaba nagartar ta, tana da zuciya mai kyau wanda ba kowa ke da irin ta ba, duk da k'iyayyar Hajiya gareta amma kullum da alkhairi take bata, Tabbas yayi dace da mace ta gari, "Shikenan zan cire mata", Umma ta nuna jin dad'in ta,

Alhaji da kansa ya kwashi kwalayen ya kaiwa Hajiya da cewa "Ga naki ki rabawa mutanen ki", "Alhaji har ka gama raba kayan ne", "Eh na gama", "Amma Alhaji fisabillahi an mun adalci kenan, ace Hajaru itace zata raba kayan Yusrah ban da tsabar makirci da son nuna maka iyakar ka", Mugun kallo ya mata yace "Ke yanzu maganar da kike ba son nuna iyakar bane, idan da kara Yusrah ai yar' Umma ce meye aibu dan ta raba kayan auren ta", Hajiya shiru tayi zuciyarta na harzuk'a "Lallai ta gama da Alhaji amma wallahi sai na lalata sihirin nan" Tayi zancen zuci, Alhaji Inuwa ya juya ya fice, Da Umma ya fara aure ko kusa ba zaiyi shawarar k'ara aure ba, dan ta had'a dukkan nagartar mace ta gari sab'anin Hajiya da kullum halayyarta ke tab'arb'arewa.

*********************

Shatu yau da zazzab'i sosai ta tashi, ga yawan jiri da tashin zuciya tana faman yunk'urin amai, Mu'azzam ya shiryata zuwa asibiti, A mota yana ta fama jera mata sannu, Direba yaja su, suna seat na baya tana kwance jikin sa.

Ba lallai gobe ku samu post ba, ina ga sai jibi
Ina da wani uzuri

OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now