HS 27

96 14 1
                                    


HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na ashirin da bakwai

Rashin Alhaji ba k'aramin sauyi ya kawo ga rayuwar iyalan sa ba, ba wai ta fannin abinci, sutura ko wani abu na more rayuwa ba, Sauyi ne na gangar jikin su da zuciya wacce ta kasa sabawa da rashin Alhaji, tun ba Mu'azzam ba wanda Alhaji ya zama tamkar amini gare sa, Kusan sha'awar komai dashi yake yi, hatta harkar kasuwancin sa da Alhaji yake tattaunawa bashi da wani amini na kusa, Su Kawu Kabiru sun nuna kawaici na rashin komawa kasuwa har sai an gama had'a dukiyar Alhaji an raba gado, A cewar su barin gadon ba'a raba da wuri ba, wani hakk'i ne gara su tabbatar an sauke, Wanda yau akace za'a yi zama na k'arshe a tantance bashin da ake bin Alhaji, kana a soma rabon gado,

*************************

Duka iyalan sa sun hallara a babban falon sashen sa, wanda duk yawan su suke jin su kad'an saboda rashin babban jigon nasu, wanda basu tab'a taruwa haka falon ba tare dashi ba, Musamman Mu'azzam wanda yake jin falon ya masa girma sosai, Kujerar da Alhaji ke zama ya kalla yaji zuciyar sa ta karaya, "Rai bak'on duniya yau gashi Alhaji ya tafi, tafiya ta har abada wacce ba dawowa". "Allah ya jadadda rahama gare sa". Yayi addu'ar a zuci, K'wararren malami wanda yasan kan harkar rabon gado suka kira sai kuma limamin unguwan wanda shima yana da d'an nasa sanin kan rabon gado, da kuma k'arin ya zama shaida, Su Kawu Kabiru ma duk suna zaune falon,

Malamin yayi gyaran murya yace "Babban abun da ya tara mu nan shine rabon gado na marigayi Alhaji Hali, wanda muna fatan Allah ya jik'an sa ya masa rahama", Kowa ya amsa da "Amin", "Shi sha'ani na rabon gado yana da wuya, amma In Shaa Allahu zanyi k'ok'ari da ilimin da Allah ya bani naga an ba kowa hakk'in sa ba tare da an tauye wani ba", Mu'azzam jikinsa ya sake yin sanyi, ya tsinke da lamarin duniya, Yanzu duk tarin dukiyar Alhaji gashi ya tafi ya barta za'a rabawa magada babu abunda zai tsiratar dashi sai kyawawan ayyukan sa, Malamin ya k'ara cewa "Ina so na muku wata yar' fadakarwa, kunga dukiya da kuke gani ba komai bace sai dattin duniya, wanda idan Allah ya baka ita to ya jarabaka ne ya gani, ba wai rashin so Allah ke sa ya hana ma bawan sa kud'i ba, mutuwar Alhaji ya kamata ya zamar ma kowannen ku darasi, duk dukiyar da ya tara lokaci d'aya ya tafi ya barta, gashi za'a raba muku, dan haka nake jan hankalin ku kuyi amfani da dukiyar da yanzu zaku mallaka wurin neman lahirar ku, kada ku bari dukiya tasa ku shagalta da duniya, haka hannun ku ya zama sake wurin sadaka, zakka da kyauta dan wanda ka bayar shine naka, komai zaku kashewa kanku iya duniya ne banda lahira, amma wanda ka bayar shine naka gobe k'iyama, Allah yasa dukiyar da za'a raba muku yanzu ta amfane ku", Duka suka amsa da "Amin"

"Kafin mu fara kasafin dukiyar da ya bari, an gama biya masa bashi duka?", Kawu Kabiru yayi caraf yace "An gama biya masa bashi, sai dai akwai wasu filaye da ba nashi bane, kada a had'e a raba dasu", Kowa kallon sa yayi, Hajiya Hafsatu tace "Wane bashi aka biyawa Alhaji, tun sanina ai Alhaji baya cin bashi ko naira d'aya ce", "A sanin ki kika ce kuma harkar kasuwa ma, taya zaki san komai, magana ma ta wuce meye na dawo da ita baya", Cewar Kawu kabiru, Zata sake magana Liman yace "Dan Allah kuyi hak'uri ya isa haka, wane filaye kake maganar ba nashi ba", Kawu Kabiru ya numfasa yace "Filaye uku ne, d'aya na nsarawa gra, d'aya na hotoro sai d'ayan na janbulo", Manyan filayen Alhaji ya zab'a yace su wanda dukkansu kowane zai kai kimanin miliyan hamsin zuwa sama, Mu'azzam mamaki ya kama sa "Idan bai manta ba ko kwanaki sunyi maganr filayen da Alhaji yana maganar a bud'e company da d'aya, A zahiri yace "Amma Kawu taya filayen suka zama ba nashi ba", Kawu Kabiru kai ya jinjina yace "K'warai ba nashi bane, dan takardun su yanzu haka suna hannu na, tun kafin a haife ka ya mallaka mana su, Ni, Lamido da Rabi'u", "K'arya kake wallahi ka shirya cuta ne, a ina Alhaji ya mallaka muku filayen sa", Hajiya Hafsatu ta fad'a a hasale, Shi kansa Mu'azzam dan kar ace yayi rashin kunya yayi shiru amma sam ya kasa yarda da hakan, Musayar baki ta kaure tsakanin Hajiya Hafsatu da Kawu kabiru, wanda Lamido da Rabi'u suka saka baki kan cewar tabbas Alhaji ya basu filayen, Malamin ya tsawatar musu da cewa "Dan Allah ku bar bawan Allah nan ya kwanta lafiya cikin kabari", Shiru ne ya ratsa falon,

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now