HS 62

101 21 1
                                    

HALACCIN SO
Zee Yabour
*62*

Kallon kallon sukewa juna kowanne da abunda ke yawo ransa, Bashar yace "Nasan kana fargabar karaya ko saboda cire dukiyar tata zai kawo nakasu ga ta ka". Dariyar da Mu'azzam ya bushe da ita ya saka Bashar masa mugun kallo, "Dukiyar Yusrah a cikin tawa tamkar allura ce a cikin ruwa, abu d'aya nake so ka sani duk harguwarka ba zata sa na damk'a maka dukiyar marainiyar Allah, kayi yadda kake so". "Ka shirya cutar yar'uwar ka dai amma kasan dukiyar matata sai dai na tattala dan yaran mu". "Idan hakane meye na tashin hankali ga son ta dawo wurin ka" Cewar Mu'azzam yana kafe sa da ido, "Saboda ni nafi iko da cancanta da dukiyar" Ya fad'a a gadarance, Mu'azzam murmushi yayi ya kunna system yana bin kissafin mutanen da suke bi bashi,

Bashar ya k'ufule ya tashi tare da buga tebur yace "Wallahi ku zuba baka isa cin dukiyar nan ba". Mu'azzam ko kai bai d'aga ba balle ya nuna alamar yasan dashi.

Bashar ya fita a ransa yana ayyana "Plan d'ina zaiyi aiki a kanka wannan karon, dama nasa ta baka kud'inta ne dan na biyo da cewa fin rabin dukiyarka tata ce". Yayi zancen zuci yana shiga shagon sa.

***************************

Lamid'o da Rabi'u tuni suka fara sarewa ganin lamarin baya nasara, hassada na cin zuciyar su amma basa iya aiwatar da komai, Hakan yasa suka koma kan kasuwancin su basa wani shiri sai dai fatan Mu'azzam yaja baya, Ta b'angaren Kawu Kabiru shiri sosai yake na son ganin bayan Mu'azzam, Kasuwar sam bai cika zama ba ya sakarwa yaransa komai saboda mugun nufi da dogon buri da ya sakawa kansa.

***********************

Shatu sosai taci breakfast da Mu'azzam ya kawo mata, wanda tana ci da murmushi tana jin k'aunar sa na nunawa kulawa gareta, bayan ta kammala ta fito kai plate kitchen, a falo ta tarar da Na'ima na kallo bata bi ta kanta ba ta wuce, Tabi bayan Shatu da harara tare da jan tsaki, "An samu gidan daula ana son maida yar' kiba anje kauye ansha rama". Ta yada habaici, Shatu bata tanka ta ba sam bata jin magana yau d'in, Na'ima ta cigaba da wak'e wak'en habaici,

Shatu bayan ta koma d'aki Umma ta kira ta gaisheta ta saka mata albarka sosai.

********************************

Halimatu yau ta dawo gida nigeria wanda tun a cikin jirgi suka rabu da Sanata Abu saboda tsaro, Siyayya sosai tayi har su Shema'u ta musu tsaraba, direban sa ya d'auketa daga airport ya kaita har gida, A tsakar gida ta samu Shema'u tana tsintar shinkafa, "Mama ina wuni?". D'agowa tayi ta dube ta tace "Halimatu ina kika shiga wayarki sam bata shiga". "Sace mun waya akayi wurin kamu". "Shiyasa nayi ta kira shiru, wannan kayan fah ko na biki ne". Murmushi tayi tace "Baban wata kawata ne ya bamu kud'i shine na muku siyayya". Kallon Halimatu tayi dan taga ta k'ara wani haske da cikowa tace "Toh Allah ya biya shi, ga zulfa nan ma kwance babu lafiya fin sati kenan". Halinatu cikin damuwa tace "Bakuje asibiti ba". "Munje kud'in da ya gagara yasa na buk'aci a sallame mu". "Allah yayi wadaran dukiya irin ta Baba". Shema'u tace "Amin" tana sake jin bak'in ciki k'asan zuciyarta, Halimatu tace "Bara na shiga na kamota muje asibiti akwai kud'i wurina". SHEMA'U tace "To ku fara yin gaba idan na gama girki na same ku". Halimatu tace "Toh tana k'arasawa ciki da sauri, Yanayin da taga Zulfa ya matuk'ar d'aga hankalinta amai take sosai tamkar zata amayar da yan' cikin ta, A kid'ime ta k'arasa tana rik'e ta, Sunan Mama take fad'i da k'arfin gaske wacce ta shigo a kid'ime suka d'auki Zulfa'u cikin wani irin yanayi suka nufi asibiti, suna isa aka karb'e ta emergency.

*************************
Bashar yau babu walwala sam a fuskar sa ya shigo gida, Yusrah cikin kulawa ta tarbe sa tana tambayar damuwar sa, "Na rasa meyasa Mu'azzam bai yarda dani ba yana ganin kamar zan cinye dukiyar ki". Yusrah tace "Nasan ba rashin yarda ba ne". "kar kice zaki kare yayanki bayan ni da shi muka tattauna". Yusrah shiru tayi jikinta na sanyi, "Kije ki same shi ya baki dukiyar ki naga alamar ko gaba ba bayarwa zaiyi ba gara tun wuri ki karb'i hakkin ki, kuma dukiyar ki ta ninka sau goma akan yadda kika basa ina da tabbacin haka". Yusrah duk da tayi mamakin ace har ta ninka sau goma amma tace  "Toh" tana masifar son Bashar ta yadda duk abunda yace ba zata iya tsallakewa ba, A ransa yana kud'ura kud'in na shigowa hannun su zai bar k'asa.

*********************************

Shema'u da Halimatu ke ta faman kai kawo tsakanin d'akin da aka shiga Zulfa, Fitowar nurse yasa sukayi kanta "Kune yan' uwan Zulfa". Suka ce "Eh". "Kuna sakacin me ciwo yaci ta sosai haka ba tare da kun kawo ta asibiti ba". SHEMA'U tace "Wallahi rashin kud'i ne". "Yanzu ana buk'atar jinin da za'a k'ara mata, jininta yayi k'asa sosai kuje ku siyo leda uku". Halimatu cikin hanzari tace "Toh" tana nufar ward da suke siyar da jini tatacce wAnda yayi daidai da group na Zulfa, Kud'i masu yawa aka fad'a, Jakarta ta laluba basu kai haka ba, Cikin hanzari ta fiddo wayarta ta sona kiran Sanata Abu a kashe take ji, "Watak'ila yana baccin hutawa". Ta fad'a tana canza akalar kuranta ga wani sai dai yau cikin rashin sa'a duka samarin nata bata samu ko d'aya, Kawu Kabiru ta yanke shawarar kira yana gani yak'i d'auka har ta tsinke sai a kira na biyu, Ya d'auka da cewa "Lafiya kike damuna da kira kinsan ina kasuwa". "Zulfa'u ce bata da lafiya tana buk'atar jini kuma babu kud'in siya". "Ai ba sai an siya ba ga ki ga Shema'u ku had'u a dib'i naku a sa mata". "Baba Dan Allah ka taimaka wallahi bata da lafiya sosai". "Ke ina kasuwa kina hanani aiki". Ya datse kiran, Halinatu tamkar ta kurma ihu, Mutanen wurin ta rok'a su bata da alk'awarin zata kawo musu kud'i, sam suka k'i yarda,(Allah ya tsaremu da rashin imani da tausayi)

"Gashi nan sakacin ku yaja ta rasa ranta duk da cewa kwananta ne ya k'are amma hadda sakacin ku wallahi" Cewar Nurse d'in cikin masifa, Shema'u da Halimatu a tare suka zube k'asa.

ALLAH YA RABAMU DA DUKIYAR DA BAZAMU IYA TAIMAKON IYALANMU BA
ALLAH YA KARA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA LAHIRA

OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now