HS 14

108 25 3
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na sha hud'u

Aikace aikace gidan yau Shatu tayi sa ne babu dad'in rai, sam babu wata natsuwar zuci tare da ita wanda hakan nada alak'a da damuwar Mu'azzam, K'arfin k'aunar dake tsakaninsu tasa ka damuwar d'aya ta zama ta d'aya, matuk'ar d'aya na cikin damuwa dukkan su babu mai natsuwa, Shatu ba mai yawan surutu bace ko fad'ar abunda ya shafe ta, hakan yasa bata da aminiya sai abokan mutu nci ba, Kaf k'awayenta babu wanda yasan me take ciki, Shigowar Mu'azzam rayuwar ta ya zamar mata aboki wanda take shawarar komai nata dashi, Yau kuma matsalar shi ta shafa balle ta tunkare sa da maganar ambaton Allah ta soma sanin tashi zata samu natsuwa (KAMAR YADDA ALLAH YA FAD'A: Da yawan ambaton Allah zuciya ke samun natsuwa),

D'aya da mintuna na rana ta kammala girki, kamar kullum Mu'azzam ta kira, Bugu biyu ya d'auka basu jima da idar da sallah ba wacce jam'i suke a k'eb'antacce wuri a plaza, Ta sanar dashi ta kammala girki, Yace "On my way Shatuna" Ya kashe wayar, Bai koma shagon sa ba daga wurin motar sa ya nufa wacce tafi kowacce tsada a wurin, Bashar yana kallon sa ta gefen ido yayi zancen zuci da cewa "Da sannu zan mallaki motar da tafi taka, zan b'atar da sunanka sai nawa za'a rik'a ji", Hannun sa ya zura cikin aljihu yayi dialing number Yusrah wacce yayi ma saving da future wife, Tana kwance d'aki tana chatting kiran nasa ya shigo, har ta tsinke bata d'auka ba, Text ya shigo ta bud'e "Ki taimaki zuciyata wallahi ina son ki so na gaskiya, ina cikin damuwa na rashin jin muryarki", Wayar ta kifa kan k'irjinta tana sauke ajiyar zuciya, Tabbas ta fara son BASHAR sai dai ba zata iya bijirewa umarnin mahaifiyarta ba, "Meye laifin auren wanda gidansu suka fi sa kud'i, ina ce ba kud'i ke zaman aure ba" Cewar wani sashe na zuciyarta haka ta rik'a sak'e sak'e,

Bashar yana tura text d'in ya jefa wayar aljihun sa da cewa "I must win your heart Yusrah, sai kin bijirewa tsohuwar makirar ce a kaina", Ya wuce shagon sa dake kusa da na Mu'azzam wanda ganin yawan customers dake bakin shagon ya k'ara hargitsa zuciyar sa.

******************************

Fitted gown ce jikinta wacce ta fito shape na mazaunanta, ta d'an kamata ta sama ta yadda dukiyar fulaninta tamkar zasu fasa rigar, Tun bud'e masa k'ofa da tayi ya bita da wani kallo bata ankara ba ya jawota jikin sa, Cikin murya mai sanyi yace "Na yaba kwalliyar nan SHATUNA", Murmushi tayi tare da fatan damuwar tasa ta kau, Hannayen sa taji kan mazaunanta yana shafawa, bata hana sa har suka k'arasa falon, Narkakken kallo ya mata da cewa "Me za samu?", "Na maka delicious food", Harararta yayi alamar bashi ba, Ta gane me yake nufi sai dai tafi so zuwa dare lokacin ta k'ara shiri, Saukar hannun sa taji cikin rigarta, A marairaice ta kalle sa, "In dai zaki rik'a mun irin shigar nan SHATUNA dole na buk'ace ki", Ya fad'a a raunane yana had'e bakinsu wuri d'aya, Dan dole ta soma mayar masa da martani wanda itama taji buk'atar mijin nata, Sun lula duniya mai zurfi wacce ta kasa ankarar dasu falo suke, Basu dawo hayyacin su ba sai da dukkan su suka samu natsuwa, Mu'azzan a duk sanda ya kusancenta wata natsuwa yake samu tare da jin soyayyarta mai k'arfi, "SHATUNA" ya kira sunanta tamkar mai rad'a, "Na'am" Ta amsa tana lafewa kan k'irjin sa, Hannun ta ya kama ya saka cikin nasa yace "Kiyi alk'awarin kasancewa dani har abada, zuci, ruhi da gangar jikina ba zasu iya rayuwa ba tare da kai ba", "Yadda rai baya iya rayuwa ba tare da numfashi ba, haka nima bana jin zan iya ba tare da kai ba YAYA MU'AZZAM, babu wani abu da zai sa na barka", Hannu ya k'ara matsewa da cewa  "Allah yasa mu kasance da juna har abada", "Amin tare da bamu zuri'a ta gari", "Ko bamu haifi yara ba kasantuwarki cikin rayuwata kad'ai ya isheni farin ciki SHATUNA", "In Shaa Allah ma Allah zai baka masu maka addu'a a doron k'asa", Hancin sa ya cusa cikin gashin kanta mai santsi wanda ke fitar da k'amshi mai dad'i, Basu jima falon ba suka tashi zuwa d'aki tsaftace jikin su.

********************************

"Uwar ki ta koya miki masifar son kud'i kullum bani bani to bani dasu" Kawu Kabiru ke fad'a cikin masifa, Zulfa'u a marairaice tace "Baba wallahi yace yau korata zanyi idan ban zo da littafi ba", "Ya kore ki mana, ai ba dole sai kinyi boko ba, shiyasa ban saka ki ba, inda kin damu da karatun sai kije wanda ya saka ki ya baki kud'in littafi, kada ki sake zuwar mun da buk'atar kud'i", Zulfa'u wacce k'walla ya cikawa ido ta tashi jiki sanyaye ta fita falon nasa, Kawu Kabiru ya cigaba da masifa kan cewar sun cika rok'o ya tabbatar ma k'arya take ba wani littafi da zata siya, Halima dake tsakar gida tana juyo su tace "Uhmm kece ai bakya jin shawara na fad'a miki kar kije dan ba bayarwa zaiyi ba baki ji ba", Zulfa'u hannu tasa ta share hawaye tace "Wacce irin rayuwa ce wannan ace mahaifin ka baya iya hidimar ka, kuma yana dashi ba babu ba", "Ni yanzu abun Baba ya daina damu na, kud'in da yake tarawa dole ya mutu ya barsu wataran", Zulfa shiru tayi tana cigaba da sharar hawaye, "Kije cikin jakata ta makaranta akwai dubu d'aya ki d'auka", Tace "Toh nagode" A zuciyarta tana mamakin ina yayar tata ke samun kud'i wanda kullum bata rasa na kashewa, "Ko Alhaji ke bata" tayi zancen zuci tana nufar d'akin su, ta d'auki kud'in ta tafi dama makaranta zata je, Tana ss2, Halima kuwa ta soma BUK.

**************************

"Ban ga alamar zargin da na d'asa masa kan Shatu yayi tasiri ba har yanzu banji wata rigima tsakanin su ba" Cewar Hajiya cike da damuwa tana duban Sahura, "Yaya kenan ai ba lokaci d'aya hakan zata faru ba a sannu wannan shine mataki na farko", Hajiya taja nunfashi tace "Wallahi na gaji Sahura, na gaji da ganin Shatu cikin rayuwar Mu'azzam, hakan tamkar nasarar UMMA ne wanda bana son ko kusa ta mori Mu'azzam", "Kwantar da hankalin ki Yaya kina dani", "Tuna hakan ke sa lokuta da dama na rage damuwa", Shu'umin murmushi Sahura tayi tace "Ki bani lokaci kad'an komai zai tafi daidai, SHATU da k'afarta zata fita rayuwar sa", "Idan hakan ta kasance na miki alk'awarin kyauta mai tsoka", "Kina magana tamkar ni d'in ba jinin ki bace, kada ki manta uwa d'aya uba d'aya ya wuce wasa", "Ina sane da hakan amma yaba kyauta tukwici", "Faruwar hakan duka amfanin kanmu ne", Hajiya ta jinjina mai da cewa "Hakane", Sahura tayi murmushi.

Kuyi hakuri da wannan mu hadu gobe

OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now