HS 28

87 17 0
                                    


HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na ashirin da takwas

Kowa ya koma kasuwa an cigaba da gudanar da kasuwanci, Duniya zance banza rashin ka ba shi zai hana  cigaba da wanzar da abubuwa ba, idan wani muk'ami ne da kai daga zarar ka mutu wani za'a samu ya mayar gurbin ka, Haka kasuwa yaranka ko wasu zasu cigaba da gudanar da kasuwancin ka, Yau ga Alhaji ya zama tarihi, Mu'azzam ya maye gurbin ofishin sa, Zaune yake jigum yana k'ara tsinkewa da lamarin duniya idan ance zai zauna kan kujerar nan ta Alhaji da sunan mallakin office d'in tabbas zai ce k'arya ne, ko kusa baya kawowa Alhaji mutuwa nan kusa, sai dai kana shirin ka Allah nasa, Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke yana k'ok'arin k'arfafa ma kansa gwiwa da rage ma kansa damuwa, Ya jawo wasu file yana dubawa, "Ya zan fara ba tare da shawara ko tattaunawa da Alhaji ba" Ya fad'a yana jin karaya, Turo k'ofar da akayi yasa shi d'ago kai, Kawu Kabiru ne ya shigo fuska sake, "Kawu Ina kwana?", Ya gaishe shi da girmamawa, "Lafiya lau Mu'azzam", Yaja kujera ya zauna a zuciyar sa yana jin bak'in cikin ganin Mu'azzam ya maye gurbin Alhaji, yana ganin shi yafi cancanta da aka mik'awa ragamar komai hatta ofishin ya zama shi ke zama ciki ba Mu'azzam,

"Kana ta faman aiki ko", Cewar Kawu Kabiru da sakewa, "Eh" Mu'azzam ya bashi amsa, "Yanzu ai haka zakayi ta fama, ayyukan ma zasu maka yawa, ya kamata ka samu mataimaki", "In shaa Allahu" , "Ko kuma gani ma duk abunda ya shige maka duhu ka nemi shawarata, ka d'aukeni tamkar Alhaji kada kaji shakkun komai", Mu'azzam yace "In shaa Allahu Kawu", "Yawwa, files d'in meye gaban ka, wani business ne kake tunanin yi", "A'ah kawai ina dubawa ne" Mu'azzam ya fad'a hakanan yaji ya kasa sakewa da Kawu Kabirun ya fad'a, "Toh, in dai akwai wani abu ka rik'a sanar dani, kasan mun fi ka dad'ewa kasuwa dole kana buk'atar shawara akan wasu lamura", Mu'azzam yace "Hakane", "Yawwa bara na koma shago ko", Ya tashi ya fita, Mu'azzam komawa yayi baya ya jingina da kujera sosai, yana dogon nazari.

*************************

"Da sannu dukiyar da kake tak'ama sai ta dawo hannu na, Ni Kabiru ban tab'a nema na rasa ba, bazan fara akan dukiyar da na jima ina ma bauta ba" Cewar Kawu Kabiru, Yana kallon office d'in daga waje, Kana ya wuce zuciyar sa cike da sak'e sak'e,

*************************

Yusrah damuwa biyu ta had'e mata rashin Alhaji da Bashar wanda ta sawa ranta bai aikata hakan ba sharri aka masa kamar yadda aka ma Mu'azzam, Su Asiya har sun fara sakewa sun shiga hidimar gaban su, Ta b'angaren Hajiya itama ta ware damuwar ta yanzu a raba Shatu da Mu'azzam, a aura masa Na'ima wacce zata yi iko a kanta, matsayinta na yar' k'anwarta mafi kusanci gare ta,

*****************************

Sallama kusan uku tana yi shiru ba'a amsa ba, tura k'ofar d'akin tayi wanda k'arar k'ofar yasa Sahura juyowa, "Mama lafiya kuwa ina ta sallama shiru na d'auka ma sallah kike", Dogon numfashi taja tace "Ina fah lafiya, ai babu lafiya matuk'ar ba fitar da Shatu nayi gidan Mu'azzam ba, kika aure shi", "Toh ai Mama dama can wannan shine burin ki, meyasa yanzu zaki damu haka sosai", Sahura kallon Na'ima tayi sosai tace "Rabon gadon da aka yi Mu'azzam ya tashi da dukiya bata wasa ba, dukiyar da baki yayi kad'an wurin fad'a miki irin ta, dukiyar da idan ba wata jarabtar ubangiji ba yayi hannun riga da talauci har abada, zuri'ar sa ma sai sun kwashi arzik'i", Na'ima ido ta zaro waje tace "Ashe Alhaji ba k'aramin mai kud'i ba ne", "K'warai da gaske, kuma shi kansa Mu'azzam kinsan yana da kud'i, yanzu ga k'arin dukiyar da ya gada, dole na shiga damuwa dan matuk'ar muka zuba ido Shatu da mahaifiyarta zata mora", Na'ima bata tab'a jin zak'uwa da auren Mu'azzam irin yau ba, babban burinta ta mallaki mota gida da sauran abubuwan more rayuwa, ta kece tsara cikin sa'annin ta a rik'a jin ta ana nuna ta, tabbas idan ta auri Mu'azzam ta taka wani babban tsani, k'awayenta sai dai su bita a baya, Tuna irin k'aunar dake tsakanin sa da Shatu ta d'an ji karaya tace "Amma Mama kina ganin rabuwar su da Shatu kuwa zai yiyu", Cikin tabbaci tace "K'warai da gaske, na sha alwashi rusa duk wata soyayyar k'arya da dangantaka dake tsakanin su, sai na dishe tauraruwar ta cikin zuciyar sa, na maye ta da taki", Murmushin jin dad'i tayi tace "Allah yasa Mamana", Kanta ta shafa kamar k'aramar yarinya tace "Kar ki damu"

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now