HS 05

118 21 1
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na Biyar

Mu'azzam kasancewar sa d'a namiji tilo a wurin Hajiya Hafsatu da Alhaji Inuwa, ta d'aura dogon buri a kansa, tana ganin ta Mu'azzam kad'ai ta mallake gidan, ita ke da power, Bambamcin halayyar dake tsakaninta dashi yasa ta kasa cimma wasu burinka da take son aiwatar wa, MU'AZZAM halin sa sak na mahaifin sa Alhaji Inuwa, tun da ya girma ya kai munzalin aure, Hafsatu ta d'auko Na'ima yarinyar Sahura ta dawo gidan, Wacce tun zuwanta duniya suka yanke shawarar had'a su aure da Mu'azzam, Hafsatu tana ganin ta haka ne zata cigaba da mulkin ragamar komai, Yarinyar yar'uwarta na k'ark'ashinta sai yadda tayi da ita, komai zai cigaba da zama cikin ikon ta sab'anin wata bare, Dukiyar Alhaji Hali Inuwa fin rabi mallakin Mu'azzam ce yafi kowa k'arfin gado a ciki, Shi kanshi Mu'azzam ya soma tara arzik'i mai yawa, idan ya auro bare ita da danginta zasu zo suci, haka idan ta haihu duka dukiyar zata koma kansu, Da tunanin haka suka tsara had'in aure ita da Sahura tsakanin yaran su, Na'ima kwad'aita mata dukiyar Mu'azzam da mahaifiyarta ke yi kullum, yasa ta saka auren shi a rai ba dan tana jin wata soyayyar shi ba, a b'oye tana kula wani saurayi wanda ba d'an kowa bane bashi da komai, Soyayya ce da Allah ke had'awa tsakanin bayin sa, Amma Na'ima tarbiyar da mahaifiyarta ta d'aura ta na son kud'i yasa ta taso yarinya mai dogon buri da son expensive life, hakan ya k'ara mata kwad'ayin son zama matar MU'AZZAM,

Mu'azzam duk da kasancewar sa ba mai sakewa ba da son yawan magana, A duk inda yaga Shatu ya kan jata da hira, Natsuwa da hankalinta ke k'ara burgeshi da ita wanda tarbiyarta ta fita daban da sauran K'annen sa, Ganin sakewar da yake mata yasa hatta assignment Shi take kawowa ya koya mata, Daga haka shak'uwa ta shiga tsakanin wacce a hankali soyayyar Shatu ta kamsa ba tare da ya ankara ba, Bai bayyana mata ba ganin tayi k'arama ta fuskanci me yake nufi, Hankalinsa ya k'ara kwanciya ne da sankankacewa ganin bata kula samari wanda duk wani motsin ta da lamuranta yana bin sa, ba tare da ta sani ba,

Na'ima duk k'ok'arinta na son samun shiga wurin sa yak'i bata fuska, Sakewar dake tsakanin su da Shatu ya soma bata haushi, ganin ita bata samun ko doguwar far'a daga gare sa, Ta d'auki k'iyayya ta d'aurawa SHATU, komai far'ar dake fuskantar ta tana ganinta zata d'aure, Tun Shatu bata fuskanta har ta gane, Hakan bai wani dameta ba duba da ahalin dama basa sonta, bata da farin jin a wurin su,

A lokacin da ta kammala sec school, ranar ya bata had'adden gift a ciki ya had'a da k'aramar takarda ya bayyana mata soyayyar sa, D'unkule takardar tayi ta runtse ido kunya ta rufeta tamkar yana gabanta, Gift kad'ai ta nunawa UMMA wacce a ranta ta ayyana jinin su yazo d'aya, Daga ranar Mu'azzam ke nuna mata kulawa ta musamman had'i da soyayya cikin nasa salon, SHATU cikin kwana biyu itama ta fad'a fagen k'aunar sa, wacce suke gudanar da zazzafar k'auna ba tare da sanin iyayen su ba, Kowane da nasa daliliin na kasa sanar da mahaifiyar sa, MU'AZZAM sanin irin k'iyayyarta ga SHATU yasan ba zata tab'a maraba da zancen ba, shine babban fargabar sa na kasa sanar da ita, Ta b'angaren Shatu kunya da nauyin mahaifiyarta ya hana,

Ranar wata lahadi bai fita kasuwa ba, suna zaune garden suna hira cikin nishad'i da soyayya, Naima tazo
neman shi gardener sanin mafi yawan lokuta nan ne wurin hutawar sa, "INA SONKI SHATU SON DA BANA YIWA WANI MAHALUKI A DORON KASA BA ZAKI K'ara shaida hakan ba sai na zamo miji gareki" Sune kalaman da suka sauka kunnen Na'ima, k'afafunta suka soma rawa tayi saurin juyawa cikin tashin hankali ta nufi falon HAJIYA, Kuka ta rusa tana k'arasawa ciki ta fad'a cikin Hajiya, "Lafiya Na'ima?", "Yaya Mu'azzam ya fara soyayya da Shatu", Ture tayi da k'arfi cikin kid'ima tace "Bana son zancen banza, kinsan me kike fad'a", "Wallahi da gaske nake, naji yana fad'a mata zai aure ta", "Kutumar uba kai, Wallahi da sake, Baki isa ba Umma nasan shirin ki ne, ba zai tab'a yiyuwa ba matuk'ar ina numfashi a doron k'asa", Ta mik'e a hasale zuwa sashen UMMA ba kalar rashin mutunci da bata yi ba, tace asiri Umman tayi ganin bata da' namiji dan su mallake dukiya take son lik'a masa yar'ta, Umma bata tankata ba ita kanta zancen yazo mata a bazata, Yaushe Shatu ta fara soyayya da Mu'azzam bata sani ba, Dama shirin nasu soyayya ce kenan, "Tun wuri ki gaggauta lalata shirin ki ko yar' ki ta had'u da masifar rayuwa", Ta juya ta fita kamar zata tashi sama,

Umma damuwa k'arara ta bayyana kan fuskarta, zuciyarta na ayyana mata dole ta raba alak'ar, Banda karambani irin na SHATU Mu'azzam ai ba sa'an auren ta bane, Fitar Hajiya na jimawa, SHATU ta shigo, Umma ta tsareta ta fad'a mata tsakaninta da Mu'azzam, A kunyace ta sanar da ita, Fad'a ta rufe ta dashi tare da mata kashedi kan ta kiyayi kanta da Mu'azzam ba sa'an auren ta ba, Daga ranar ta soma k'auracewa masa duk da k'asan zuciyarta tana jin rad'adi na rashin sa, Kowane dare da kuka take bacci, Bata san haka soyayya take ba da batayi gigin fara son sa ba,

Mu'azzam shi kansa ya shiga damuwa ba kad'an ba, ya kasa daurewa ya samu Mahaifinsa kan yana son Shatu, Ya nuna jin dad'in sa sosai, Sai dai da yazowa duka matansa da maganar babu wacce ta nuna farin cikin ta, Hafsatu tijara tayi kan bazai yiyu ba, Ta b'angare Umma ta cikin ruwan sanyi ta nuna masa a bar zancen had'in, Wanda ya lurar da ita fa'idar haka, bata musa mishi ba duk sa k'asan zuciyarta bata son had'in,

Hajiya Hafsatu ba kalar tijara da rashin mutunci wanda bata shukawa Umma da Shatu ba, wanda mafi yawa tare da Anty sahura suke yi, Umma tsananin hak'urin ta yasa bata tab'a biye musu, Sun sha mata alwashin matuk'ar Shatu ta auri Mu'azzam sai rayuwarta ta tagayyara, Jin hakan Umma ta k'ara gargad'in Shatu ta kiyaye sa, Itama ta sanar dashi ba zata aure shi ba, ba tare da amincewar mahaifiyar sa ba, Mu'azzam duk iya k'ok'arin sa na shawo kan mahaifiyar sa, abun ya gagara har ta kaisa ga kwanciya asibiti, Rai hannun Allah tsakanin uwa da d'a sai Allah Hajiya ba zata iya jure ganinsa haka ba dan dole ta amince, Ba'ayi event ko d'aya a auren ba, kasancewar babu mai armashi dashi sai ALHAJI INUWA, yan uwa da yawa na bak'in cikin sun so ace yar' su ya aura, dan tarin dukiyar da suke hango zai mallaka bayan Alhaji ya kwanta dama, bayan basu san gawar fari ba tsakanin Alhajin da Mu'azzam,

Tun auren Mu'azzam da SHATU suke fuskantar kalubale iri iri, Mafi girman barazanar rayuwar aurensu HAJIYA HAFSATU DA ANTY SAHURA wanda sukayi karan tsaye a ciki, suka sha alwashin ganin bayan auren, tare da nisanta tsakanin su, da haddasa gaba wacce zata sa har abada ba zasu dawo tare ba.........

SHIN ZASU CIMMA BURIN SU KUWA
KU BIYO Ni cikin littafiN HALACCIN SO

SHAFIN YAU BAIYI TSAWO BA

MU HAD'U GOBE

OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now