HS 44

108 22 2
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na Arba'in da hudu

Mansura da Maimuna daga gidan Mu'azzam, gidansu suka nufa wurin Hajiya Hafsatu,

Tas suka zayyane mata irin tarbar da suka samu daga wurin Na'ima da abunda tayi akan fasa kofi, Hajiya Hafsatu ta numfasa tace "Kun cika k'orafi wallahi da maida k'aramin abu babba, sai kace bak'i yarinyar da kusan tare kuka tashi da ita a gidan nan, wacce tarba kuke so ta muku, kuma maganar fasa kofi meye dan ta nuna rashin jin dad'in ta ai gaskiya ce ya cika k'iriniya ni kaina kuka zo b'arna nawa yake mun, maganar Shatu ai makira ce da tayi gadon halin uwarta taya zata nuna maka b'acin ranta, daga yau bana son sake jin wani zance". Sukayi shiru kowacce rai ba dad'i, tuna k'aunar dake tsakaninta da Anty Sahura yasa basuyi mamaki sosai ba, yadda ta fifita ta akan kowa, take girmaama lamuran ta, Sabgogin gabansu suka cigaba.

******************************

"Kai naga sam lamarin karb'uwar kayan Mu'azzam da yadda ya kwashe duka customers bai dame ka ba, na rasa wane irin rashin sanin ciwon kai ne tare da kai". KAWU kabiru ke cewa Bashar cikin masifa, Dan' gyara zama yayi kan kujera yace "Ba haka bane Baba". "Toh yaya ne?". Bashar shiru yayi ko kusa ba zai sanar da Kawu Kabiru nasa shirin ba wanda yake ganin ba da jimawa burinsu zai wuce, ya shallake Mu'azzam shima
Sunan sa ya samu karb'uwa sosai, "Dama nasan baka da tunani komai a kan ka, sai son kud'i baka san dabarun samun su ba, to bani kunnen ka nan, babban dalilin da yasa kaga na dage kan auren ka da Yusrah dan ka k'ara samun shiga jikin Mu'azzam na samu cikar burina". Bashar dama yasan can Kawu Kabiru ya nufa sai dai ba zai yarda yayi amfani dashi kad'ai ba, ba tare da shima ya yagi nasa rabo ba,

"Yusrah matarka ce kai kasan salon da zakayi amfani wajen nuna mata kana son yin business tare da Mu'azzam, ma'ana ya jawo ka cikin kasuwancin sa ku rik'a yi tare, ta haka zamu samu damar yashe sa". Bashar kai ya jinjina da nuna alamar gamsuwa, amma k'asan ransa yana da nasa shirin da yake ganin ta haka zai cimma burin sa, Kawu Kabiru ya sake zayyana masa hanyoyin da zai bi, Kafin ya fito falon, Ya shiga wurin mahaifiyar sa suka gaisa ya bata dubu biyar, karon farko da ya mata kyauta ta kai haka, kyautar tasa bata wuce dubu d'aya dubu biyu, Shima yanzu kud'in Yusrah da ya had'e da nasa ne yana kasuwanci ganin sun k'ara yawa a ransa yasa sun zama nashi,

K'ofar gida yaci karo da Halimatu wani saurayi ya ajiyeta, Tana ganin sa jikinta yayi sanyi dan daga wani hotel suke, Cikin sanyin jiki ta gaishe da Bashar, "Daga gidan uban wa kike, wane dan' iskan ne ya ajiye ki". "Gidansu k'awata direban gidan su ne". "wallahi ki kula ko naci maki uwa, wuce kafin nayi k'wallo dake". Ta wuce cikin hanzari, a ranta tana gongoni "Ku ba kula da mutum ba, sannan kace ka hana mutum hanyar da yake dan' samu, banda wannan harkar ai da na zama abun tausayi, babu k'awar da zatayi mu'amala dani, Ga zulfa'u nan tana wahala".

Bashar gidan sa ya nufa zuciyar sa cike da tunani, Yusrah na zaune falo tasha ado tana jiran dawowar nasa, soyayya take masa ta bilhakk'i kana tana matuk'ar yi masa biyayya, Tun da taji shigowar motar sa, Ta tashi zuwa k'ofa tarbar sa, Shi kansa irin kulawar da take bashi tana sake shiga ran sa, sai dai k'aunar da yakewa kud'i da dogon burin dake ransa sune gaban sa a yanzu, Kyakkyawar ruguma ta masa, Shima ya manna ta da k'irjin sa, Suka shiga ciki,

Wasi-wasin yi mata maganar yake yana ganin tamkar yin haka zai rusa shirin sa, yayin da zuciyar sa ke nuna masa riba biyu zai tashi da ita, ta kowane gefe zai samu, Tunanin haka ya zaunu zuciyar sa, Ya d'an marairaice fuska yace "Kasuwa yanzu ta tsaya cak babu wani cigaba". Yusrah tace "Subhanallah, garin yaya haka to". "To gashi nan dai, ni bansa me zance ba wallahi abun saia addu'a". Damuwa k'arara ta bayyana kan fuskarta, "Mu'azzam shi dai Allah ya saka masa albarka kullum gaba yake yana k'ara bunk'asa". "Kai ma Allah ya saka maka albarkar ya d'aukaka ka". "Amin amma irinsu Mu'azzam da zasu jawo ka jiki su d'an saka ka kasuwancin su da kaji dad'i kai ma ka farfad'o". "Me zai hana ka masa magana to, sai ku gwada yin kasuwancin tare, idan ka samu sosai, sai ka cigaba da naka kai kad'ai". Kai ya girgiza yace "Ko na masa magana ba lallai ya fahimceni, kece k'anwar sa ke ya kamata ki mishi". Kai ta d'aga tace "Ba damuwa gobe sai ka kaini na masa magana". "A'a kije ke kad'ai da dabara, bana so yaga ni na saka ki, kuma kada ki nuna masa ni na nuna buk'atar haka, kawai ki nuna masa ra'ayin ki ne". Tace "Toh". Bashar ya kwanto ta jikin sa yana jin farin ciki, da ganin auren Yusrah ba k'aramin riba bane gare sa, ta hanyar ta zai cimma duka burinkan sa.

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now