HS 43

106 15 3
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na Arba'in da uku

Ibrahim baccin sa yau ragagge ne sai faman juyi yake kan gado da tunanin Shatu, lokaci d'aya zuciyar sa ta kamu da azabtaccen son ta, alla-alla yake safiya tayi yaje ya ganta ya bayyana mata sirrin zuciyar sa.

***************

Kiran sallar farko ya tashi Mu'azzam, ya karanta addu'ar tashi daga bacci "Alhamdulillahil lazi ahyana ba'da ma amatana wa ilayhin nushoor". Duban sa ya kai gefe Na'ima na bacci hankali kwance, Bargon da ta rufe ya janye a hankali da cewa "Tashi kiyi sallah". Ya sauka gadon ya shiga band'aki yayi alwala ya fito zuwa masallaci,

Na'ima sake gyara kwanciya tayi ta cigaba da baccin ta,

Mu'azzam ya jima masallaci yana karatun qur'ani da addu'o'i, Sai da gari ya waye ya shigo gida, Ganin tana bacci yayi tunanin tayi sallar ne ta koma, Fita yayi ya koma d'akin sa, Yau da wuri zai fita kasuwa saboda kayansa da suka iso wanda su KAWU KABIRU suka so k'onawa, an samu delay na zuwan su, Cikin mintuna talatin ya shirya cikin shadda coffee brown ta matuk'ar yi masa kyau, ta k'ara saka masa cika da kamala, Ya fito falo yana d'aura agogo, Na'ima ce ta mik'e tana nufa sa tace "Kawo na d'aura ma". Kamar zai basar sai kuma ya mik'a mata, Cikin salo tana kwarkwasa ta saka mishi, Bayan fitar sa d'akin ba jimawa ta tashi tayi sallah tayi wanka, "Kayi kyau angona". "Nagode". Ya fad'a yana nufar dining table, Ta rufa masa baya,

Cikin hanzari ta soma k'ok'arin serving d'in sa da hannu ya dakatar da ita, Ta koma ta zauna, Ruwan shayi kad'ai ya had'a ya fara sha, Ta jawo plate tayi serving kanta, Yana kammala sha ya mik'e da cewa "Na tafi kasuwa". "A satin amarcin". Ta fad'a a marairaice, "Uzuri yasa haka". Yana fad'a ya bar dining area bai jira amsar ta ba, "Dama nasan za'ayi haka, ni dai idan zaka cika mun account da kud'i ai shikenan". Ta fad'a tana kai chips bakinta.

***************************

Cikin sauri take shiri ta kusa makara, bacci mai nauyi ya d'auketa bayan sallar asuba, A falo ta k'arasa saka hijabi, IYA na baccin safe haka su Jummai suma basu tashi ba ta fice, Turus tayi ganin motar da ta kawota jiya bakin gate, Ibrahim yana ganin fitowar ta, Ya fito motar, "Barka da safiya gimbiyar mata". K'irjinta ya duka ya tuna mata da Mu'azzam haka yake kiranta wasu lokuta, "Kiyi hak'uri na sake biyo ki sai dai ba laifina bane zuciyata ce ta kwad'aitu da son sake ganin ki". Numfashi taja da cewa "Ina kwana?". Bata son wulak'anta kowa a rayuwarta, kowane dan' adam tana bashi daraja, "Lafiya lau". Ya amsa cikin jin dad'i, "Zan wuce makaranta". Ta fad'a tana yin gaba, "Zuwa nayi dama na kai ki". "A'ah ka barshi nagode". "Dan Allah kada kice haka". Bata son wani kusanci da da' namiji hakan yasa ta sake fakewa kan a'ah, "Dan girman Allah ki amince na kai ki, kiyi hak'uri da na zama mai shisshigi a rayuwar ki". Bata da wani zab'i ganin magiyar sa, Ta juyo ta shiga bayan mota, Godiya ya rik'a mata tamkar ta bashi babbar kyauta, har ya shiga mota ya soma driving,

"Gimbiyar matar bata fad'a mun sunanta ba". "Aysha". Ta fad'a a dak'ile, "Suna mai dad'i ni kuma Ibrahim". Shiru tayi tana maida kallon ta window, Shima sai yayi shiru yana satar kallonta ta mirror har suka kawo makarantar, "K'arfe nawa zaki kammala?". "Gaskiya ban sani ba". Murmushi yayi sanin ta fad'a ne dan kar ya dawo yace "Korata kike ko, gashi zuciyata ta kwad'aitu dake". "Ina bata shawara ta cire dan matar wani ce". Dariya yayi yace "Da ke matar aure ce tun a jiya zaki sanar dani, haka ba zaki shiga mota ta ba". "Ina nufin an bayar dani aurena saura sati biyu". "Tunda ba'a d'aura ba nima zan iya shigowa sahu". "Ka tab'a ganin anyi neman aure kan aure". "Ni dai tunda na ganni zuciyata ta bani ke tawa ce dan haka bazan karaya". Numfashi taja tare da bud'e motar ta fita, Yabi bayanta da kallo tare da addu'ar Allah ya mallaka mishi ita matsayin mata,

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now