HS 16

84 19 1
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na sha Shida

"Kawo ta ko, kin k'ak'ame kamar zaki had'iye ta" Anty Sahura ta fad'a tana d'auke jaririyar jikin Shatu, Ranta ya k'ara sosuwa sosai, Ambaton Allah ta soma, Umma ganin idan suka jima gida za'a cigaba da sakar musu magana ne wacce zata ci musu zuciya, Yasa tace su tashi su tafi, SHATU kud'in taba mai jego, Gaf da k'ofar fita suka jiyo muryar Hajiya Hafsatu na cewa "Bak'in ciki ba zai bari su zauna ba, cikin nata bashi da amfanin komai sai ci a kasar", Shatu tamkar zata bi ta kan Teema tayi saurin ficewa gudun sake jin abunda zai dagula zuciyar ta,

Dukkansu rai babu dad'i suka shiga mota, Teema tace "Kiyi hak'uri Yaya Shatu, In Shaa Allahu Allah zai baki yara masu yawa da albarka", Murmushin yak'e tayi tace "Allah ya amsa Teema", A tare suka ce Amin da Farha, Ita kanta Umma tun fitowar su take addu'ar samun zuri'a nagari ga Shatu,

Gida ta buk'aci su ajiyeta ba abunda take buk'ata kamar kuka, bak'in cikin da ya tsaya mata ta kuka kad'ai zata amayar dashi, Bata son yin gaba Umma ko su Farhq ta tada musu hankali, "Umma zan bi ta" Cewar Farha, Kai ta girgiza alamar a'ah, duk da k'asan zuciyarta tana jin tamkar ta bar Farha zata ragewa Shatu zama dogon tunani,

******************************

Jaka da mayafin ta ta cillar gefe d'aya ta fad'a kan gado, ta saki kuka mai sauti wanda yake cunkushe da bak'in ciki, damuwa had'i da rad'adin zuci, ta kasa sabawa da halayyar su Hajiya Hafsatu ba tun yau suke mata gorin haihuwa ba, tun a shekararta na farko ga aure, A kullum da kalar cin mutunci had'i da tijarar da suke mata, Gorin haihuwa tana jin ba abunda ya kai sa zafi da rad'ad'i, abu ne da baka da iko akan sa, Ubangiji kad'ai ke bada haihuwa meyasa mutane sun kasa fahimtar haka, kowa na son ganin gudan jinin sa, meyasa ba za'a bar mutum da zafin rashin haka ba sai an k'ara masa, zantukan ke kai kawo zuciyarta yayin da hawaye ke ambaliya kan fuskarta suna jik'a zanin gado.

********************************

Shida da minti biyu daidai ya fito daga plaza, Tunda ya hau kan titi, Yake kiran wayarta bata d'auka ba, Zuciyar sa ta bashi bata kusa, Hanyar gidan su ya d'auka yana k'ara sautin radio wanda k'ira'ar Sudais ke tashi, Mintuna kad'an ya kawo sa gidan, B'angaren Hajiya ya fara shiga, Babu kowa basu dawo daga gidan Maimuna ba, Bai saba shiga sashen Umma kai tsaye ba tare da iso ba, Hakan yasa ya k'ara kiran wayar Shatu har ta tsinke, Bashi da wani option da ya wuce kiran Umma, Fitowar band'aki kenan tayi alwalar magriba, Kan dressing mirror ta k'araso ta d'auki wayar, ganin kiran Mu'azzam gabanta ya fad'i sanin baya kiran ta, fatan ta ba wani abu ya sami Shatu ba, Ta d'auka cikin fargaba, Ya gaishe ta da ladabi ta amsa, Ya tambayi Shatu, ta sanar dashi ai sun ajiye ta gida, Yace "Toh" ya kashe wayar, Umma jikinta yayi sanyi tabbas Shatu na cikin wani hali tunda bai sameta ba, "Ya Allahu ka bamu ikon cin jarabawar nan, Allah ka kawo sauyi na alkhairi a rayuwar Shatu"

*****************************

Ko ba'a fad'a masa ba yasan ba lafiya ba, Hakan yasa ya k'ara gudun motar sa zuwa gidan sa, Tun daga bakin k'ofa ya soma jiyo sautin kukan ta, Cikin hanzari ya shiga, Bata ji shigowar sa ba sai d'agota da yayi ya d'aura kan k'irjin sa, Yana jin wani zafi a ransa sosai kukan nata ke tab'a shi

"Sai yaushe zaki daina zubar da hawaye akan abunda baki da iko kan sa, bayan komai rubutacce ne kuma muk'addari daga ubangiji, haka bawa bay cire rai ga rahamar Allah", Cikin murya mai cike da kuka tace "Na sani Yaya Mu'azzam amma bani da iko na hana zuciyata zafi, rad'ad'i da k'unci, bani da iko na hana idona zubar hawaye ta hakan kad'ai nake rage nauyin zuci", "Kukan ki gare ni tamkar zubar dalmar wuta ne a zuciyata, bana k'aunar ganin damuwa kan fuskar ki balle zubar ko da k'walla d'aya ce, Dan Allah ki tausaya mun ki koyi juriya da hana kan ki zubda hawaye" Lafewa tayi kan k'irjin sa tana tsayar da sautin kukan ta, sai dai hawaye bai fasa zo ba, Mu'azzam matse ta yayi kan k'irjin sa, Tsawon minti biyu, Cakulkuli ya soma mata ta saki dariya bata shirya ba, Shima dariya yake yana mata suna dariya cike da annashuwa, Zame jikinta tayi zata gudu ya kamo ta ta fad'o jikin sa suna dariya.

*******************************

Bashar yau cikin da k'arfin gwiwa had'i da gadara yazo gidan, yana da goyon bayan Alhaji hakan yasa yaji zai iya tunkarar Hajiya Hafsatu yau gadaga,

"Uwar wa zai ci shegen girkin nan kin cika uban gishiri, yanzu kije ki sake wani sabon girki sakwara da miyar ganda" Hajiya Hafsatu ta fad'a cike da masifa, Luba jiki na rawa tace "Toh Hajiya", Masifar da take ta hana mata jin sallamar Bashar d'in wanda sai bayan wucewar Luba ta gan sa,

"Hajiya Ina wuni?" Ya gaishe ta yana daga zaune, "Baka iya gaisuwa bane cikin ladabi, kuma a haka kake tunanin na baka auren ya' ta", "Ai auren nata kuma a hannun namiji yake", "Kai mara kunya indai wurin Yusrah ka zo tashi ka tafi", Murmushi yayi yace "Hajiya nan ai gidan mu ne, bani korowa", "Lallai Bashar wuyan ka ya isa yanka, to bari kaji in dai ni na haifi Yusrah ba zaka aure ta ba wallahi", "Lokaci zai shaida", Ya fad'a yana fiddo wayar sa gaban aljihu ya soma kiran wayar Alhaji, Sai da ta kusa tsinkewa ya d'auka, Bashar ya gaishe sa cikin ladabi, Ya amsa, Kana yace "Dama nazo wurin Yusrah ne, Hajiya ta hana ta fitowa", "Bani minti biyu ina zuwa" Cewar Alhaji ya kashe waya cikin b'acin rai ya soma kiran Hajiya Hafsatu wacce ke tsaye cikin tsananin takaici tana jin tamkar ta rufe Bashar da duka, lallai ya kai mugun tsagera mai tsaurin ido, Tana ganin kiran Alhajin ta san kanun zancen, Ta d'auka, "Yusrah ta fito ga Bashar yazo wurin ta", Yana fad'a ya kashe,

Mugun kallo ta watsawa Bashar tace "Uban ka ma yayi kad'an balle kai wallahi", Ta juya ta hau sama tamkar zata tashi sama, Yusrah dake kwance suna hira tare da Asiya, Turo k'ofar da k'arfi yasa katse musu hira, "Ki wuce kije wurin Bashar, amma da sharad'in kada ki sake ki bashi fuska", Ta juyo tana rufe k'ofar da k'arfi, Yusrah mamaki ya kamata meyasa zatace taje wurin shi idan har bata amincewa auren su ba, Asiya tace "Bashar ya raina mutane ma wallahi, yana k'ark'ashin Alhajin zai wani ce son ki yake, wutsiyar rak'umi ai tayi nesa da k'asa", "Kuna bani mamaki wallahi, a ina Allah ya haramta aure tsakanin talaka da mai kud'i, ko ai Bashar nada rufin asirin sa", "Da alama kema kina so kenan" Cewar Asiya tana tab'e baki,

Yusrah bata sake cewa komai ba, ta yafa mayafinta ta fita, Bashar tun ganin fitowar ta ya gyara zama yana bin ta da kallo fuska d'auke da annashuwa, Yusrah wuri d'aya ta takure, Cikin nasa salon ya soma zuba mata kalamai masu tsayawa a zuci, wanda ya saka ta mutuwar jiki tana sake jin wani yanayi a tare da shi, Ya jima kana ya tafi bayan ya bata k'aramar jaka mai d'auke da gift, Yusrah ta koma d'aki cikin sabon shauk'i, Sosai gift d'in ya burgeta turaruka ne sai bracelet na azurfa mai kyau, Ta tsinci kanta da d'aurawa a hannu.

*************************

Hajiya ke ta faman kai kawo a d'aki, gaba d'aya ta rasa natsuwa, "Ba zai yiyu ba wallahi, ban gama kashe wutar ba, za'a k'ara kunnu mun wata, Yusrah ba zata tab'a auren Bashar ba wallahi, ya zama dole nasan abun yi", Ta k'arasa da yin k'wafa.



OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now