HS 29

100 19 1
                                    


HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na ashirin da tara

D'an matsawa tayi gefe dan ta bata damar shigowa, Fuska babu annuri ta shigo tana bin falon da kallo tamkar bak'on ganin ta, Shatu cikin ladabi tace "Sannu da Zuwa Anty", Kai ta d'aga ba tare da ta kalli saitin Shatu ba, "Kazo gida amma babu mai maka oyoyo, kullum tsit kamar mak'abarta", Shatu jikinta ne yayi sanyi yayin da raunin da kullum take k'ok'arin binnewa ke son tashi, Anty Sahura zama tayi kan kujera ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya, Shatu k'aurin girkiwa da ta somawa jiyowa yasa tayi saurin shiga kitchen, ta kashe gas, Ta kwashe girkin ta dawo falo,

Anty Sahura na hakimce falo ta d'auki remote tana canza channel, "Mutum sai yayi kallo ai tunda babu abokan taya hira", Shatu zama tayi wuri d'aya a takure tamkar ba gidanta ba, idan tana gaban Hajiya ko Anty Sahura bata iya sakewa sam gudun laifi, amma duk da hakan lokuta da dama bata tsira sai sun yab'a mata bak'ar magana,

Masu aikin gidan ne suka kawo mata abun motsa baki, Ta kalla a yatsine ta kawar da kai, Tace "A sanina kaf zuri'ar mu babu mai matsalar rashin haihuwa, haka ta b'angaren Alhaji kowa na haihuwa", Shatu tuni ta d'ago inda ta dosa, ta rasa dalilin da kullum suke jinginta mata rashin haihuwar wanda ta alak'anta hakan da tsabar k'iyayya, "Allah sarki Mu'azzam ni tausayi ma yake bani, ace ka haura shekaru talatin babu magaji, babu mai masa addu'a a doron k'asa, mutuwar nan dake zuwa lokaci d'aya yanzu ga Alhaji ya tafi". Ta girgiza kai tana k'ok'arin matsar k'walla, Shatu cikin raunin murya tace "Allah ya jik'an Alhaji. "Amin, Gaskiya Mu'azzam na buk'atar magaji ko ba komai kana son ganin jinin ka, muma muna son ganin jikokin mu" Ta fad'a da mik'ewa, Lemon kwali ta d'auka ta nufi k'ofa ba tare da ta ma Shatu sallama ba, wacce take zaune a wurin tamkar ruwa yaci ta, zantukan Anty Sahura sun jefe ta cikin zurfin tunani da yanayi mara dad'i, "Shin ko nice bana haihuwar  Yaya Mu'azzam ya b'oye mun?" Ta tambayi kanta, "Kada ki manta a gabanki Dr a germany ya shaida lafiyar ku k'alau". Tacewa kanta, Yayin da wani b'angare na zuciyarta yace "Kika sani had'in baki ne", K'irjinta yayi mummunan dokawa bata fatan hasashe da tunanin ta ya zama gaskiya, idan ta kasance JUYA ce da gaske hakan na nufin ba zata ga gudan jinin ta ba, "Ya Hayyu Ya Qayyum kada kasa hakan ya kasance, Ya Allah ka nuna mun gudan jinina kafin na bar duniya". Tayi addu'ar cikin sanyin jiki, Yayin da bakinta ya soma ambaton Allah tana son samun sassaucin abunda take ji a zuciya.

"Matakin farko",  Cewar Anty Sahura bayan ta shiga mota ta hakimce seat na baya, tayi shu'umin murmushi kana ta umarci direban ta ya wuce da ita gida.

******************************

Bashar a kasuwa ya samu Kawu Kabiru ofishin sa, yaci sa'ar tarar dashi shi kad'ai ba tare dasu Lamido ba, "Lafiya na gan ka, dan nasan tabbas akwai abunda ya kawo ka", Bashar ajiyar numfashi yayi yace "Baba matuk'ar ba'a tashi tsaye ba, Matar Alhaji sai ta lalata auren nan", Kawu Kabiru gyara zama yayi yace "Tayi kad'an wallahi, daman nasan sai tayi bori ganin babu Alhaji, amma idan tasan wata ai bata san wata ba, auren ka da Yusrah babu fashi, nama jawo kwanakin auren jibi In Shaa Allah za'a d'aura ba sai anyi shagalin biki ba, lefe idan taje ka bata", Bashar cike da farin ciki yace "Nag...." Da hannu ya dakatar dashi yace "Bana son godiyar ka, nima amfanin kaina ne", Bashar yayi shiru a ransa yana k'ara jinjina ba k'aramin buri Kawu Kabiru yaci ba, duba da yadda ya tsaya tsayin daka dan ganin ya tabbatu, Bashar na fita Kawu Kabiru ya nufi ofishin Mu'azzam,

Yana tattaunawa da wasu daga cikin yan' plaza kan kayan da suka shigo za'a raba kasuwa, Kawu Kabiru ya shigo kai tsaye, Bin kowa da kallo yayi yace "Me ake tattaunawa ba tare dani ba", "Wasu kaya ne za'a raba kasuwa" Mu'azzam ya fad'a, "Haba Mu'azzam ace har kaya sun shigo za'a fitar kasuwa baka sanar dani ba, hakan na nuna baka d'auke ni matsayin Alhaji ba", Mu'azzam d'an jim yayi yana ganin ba wani abu bane da ya kamata sai Kawu Kabirun ya sani, A zahiri yace "Na d'an shafa'a ne", "Shikenan" Cewar Kawu Kabiru xuciya cike da hassada, Sauran suka tashi suka fita, Ya zauna kan kujera yana duban Mu'azzam, Yace "Kamar yadda ka sani tun kafin rasuwar Alhaji yayi maganar auren Yusrah da Bashar", Mu'azzam ya jinjin kai, "Yanzu kuma Hafsatu ta fito ta nuna adawarta wanda hakan ba daidai bane, tun Alhaji na raye bata nuna ba sai yanzu da ya kwanta dama, dan haka na yanke shawarar d'aura auren su gobe, na soke duk wani biki", Mu'azzam kai ya jinjina yace "Allah ya tabbatar mana da alkhairi", Kawu Kabiru yace "Amin, na sanar maka ne a matsayin ka na babban Yayan ta", Mu'azzam yace "Ko ba'a sanar dani ba ai Kawu, tunda tun Alhaji na raye ya zartar da hukunci kuma kai ma mai iko ne akan Yusrah", Kawu Kabiru dariya yayi ya washe baki yana matuk'ar son a girmama shi a nuna shi ke da iko akan komai,

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now