HS 31

101 17 5
                                    


HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na talatin da d'aya

A gajiye ta dawo gida dan kusan gidan kowa taje hakan yasa tayi dare, ruwa masu d'umi ta buk'ata ta shiga tayi wanka wanda taji  k'arfin jikinta sosai, Ta shirya cikin wani yadi, ta dawo k'aramin falon INNA wanda ciki da falo ne, Teema kad'ai ce da Inna, Farha tabi Gwaggo Jamila, Suka dasa hira cikin nishad'i wanda Shatu ke ji tamkar bata d'auke da wata damuwa,

Daren ranar Mu'azzam da Shatu raba shi suka yi suna waya cike da kewar juna, kai kace sababbin masoya ne saurayi da budurwa wanda basu jima da juna ba tsabar yadda suke nuna zak'uwa, Mu'azzam gadon d'akin yaji ya masa fad'i, dan dole ya jawo filo ya rungume, "SHATUNA ba zaki iya dawowa gobe ba", Ya fad'a a marairaice, Numfashi taja tace "Matsalar su teema nasan basu gama ba". "Shikenan kar a takura su, Allah ya kaimu jibin lafiya". Tace "Amin". Suka cigaba da wayar cikin soyayya wanda sai da bacci ya kwashe ta, kana ya kashe wayar.

**************************

Kawu Kabiru shi yayi tsaye wurin shirin komai na auren Yusrah da Bashar, hatta gidan Bashar d'in shi ya saka furnitures a cewar sa Yusrah yar' sa ce, Yan' uwan Shema'u sun zo mata Allah ya sanya alkhairi, da d'auko kamar yadda Kawu Kabiru ya buk'ata, Matan su Lamido ma duka suna gidan sanin wulak'anci. haiiya Hafsatu yasa basu je can ba,

Motoci kusan shida suka yi na zuwa d'aukar amarya kai kace ba bikin dangi ba,

Yusrah na kwance d'aki ciwon kai sosai ke addabarta saboda kukan da tayi, Hajiya Hafsatu sam bata bi ta kanta, Su Asiya ne masu nuna damuwar su kanta, Sai Mu'azzam da ya kira ta a waya yana mata nasiha kan aure,

Tun daga harabar gidan suka soma gud'a da fad'in "Mun zo d'aukar amarya". Anty Sahura ce ta kalli Hajiya Hafsatu tace "Kina jin abunda nake jiyo wa". "Ina ji ai komai sukayi wancan yar' banzar ta jawo, da bata manufunceni ba da ba'a yi auren su ba". "Hakane amma Allah ya tsara faruwar hakan". Cewar Anty Sahura, Hajiya Hafsatu fuska na nuna k'ararar damuwa tace "Ni dai da alama bani da sa'ar rayuwa, auren yarana ace na kasa aiwatar da komai, Auren Mu'azzam haka ina ji ina gani ya auri tsinnaniyar can, yanzu Yusrah ta auri wancan shashaha, ace duka yaran ja basa bin ra'ayin ka", Anty Sahura dafa k'afad'arta tayi tace "Ki daina fad'ar haka, da sannu komai zai warware auren Shatu da mu'azzam kuma, ki shirya jin labari mai dad'i". "Kullum haka kike cewa Sahura, amma tsakani da Allah na fara sarewa wallahi". Murmushin gefen baki tayi tace "Na miki alk'awarin kawo k'arshen matsalar". Hajiya Hafsatu numfashi mai nauyi taja tace "Ina fatan hakan dan bamu da lokaci". Sahura tayi shu'umin murmushi.

Har yan d'aukar amarya suka shigo Hajiya Hafsatu da Anty Sahura basu fito ba, K'us k'us suka soma da fad'in dama ba son auren take ba, Yusrah jin su yasa ta tashi da sauri ta shirya cikin sababbin kayanta, dama basa rabuwa da sabon kaya dan ko yaushe cikin d'inki ake, Atika matar kawu lamido, da Ramatu matar kawu Rabi'u sune suka shiga d'akin Yusrah fito da ita, Basu yi mamakin ganinta ita kad'ai ba sanin irin auren da akayi, ba'a gayyaci kowa ba, Cikin ladabi ta gaishe su, Suka amsa da fad'in "Amarya". Babban mayafi Atika ta d'auko cikin drawer Yusrah ta rufa mata, kana ta ja hannun ta, suka fito d'akin, Ganin basu nufi d'akin Hajiya ba, Cikin sanyi murya tace "Dan Allah zan shiga wurin Hajiya". Sakin ta sukayi suka ce "Toh ki d'an yi sauri". Ta jinjina kai,

Cikin sanyin jiki ta tura k'ofar d'akin, a take Hajiya da Anty Sahura suka kallo k'ofar, wanda Hajiya ganin Yusrah tayi saurin kawar da kanta gefe, Duk'awa tayi gaban Hajiya tace "Dan girman Allah kiyi hak'uri Hajiya ki samun albarka ko zan ga haske a rayuwar aurena". "Baki so ganin haske ba tunda kika zab'i wani a kaina, kuma sai kinyi dana sanin auren shi kije zaki gani". (subhanallah ya kamata iyaye su san irin furucin da zasu rik'a ma yaran su), Yusrah cikin damuwa tace "Dan Allah kar kimun baki Hajiya, kiyi hak'uri". "Tashi ki fita bana son ganin ki". Anty Sahura ta dubi Hajiya tace "Dan Allah kiyi hak'uri kada fushin ki ya tab'a ta". "'Na gama magana taje gata ga Bashar". Kan Yusrah ta koma tace "Tashi kije Yusrah zan k'ara mata magana, Allah yasa albarka a auren ku". Cikin sanyi jiki ta mik'e ta fito, Atika suka kamata zuwa mota.

"Haba Yaya bai kamata ki d'auki fushi da ita haka ba, aure an riga an yi sai hak'uri". Wani kallo tama Sahura tace "Meyasa auren Yusrah da Bashar bai dame ki sosai ba kamar na Shatu da Mu'azzam". "Kin san tabbas shima ya dameni, fushin da kika yi da Yusrah ne naga bai kamata ba wanda baki da Mu'azzam ba". Shiru Hajiya hafsatu tayi sanin hakane lokacin Mu'azzam batayi fushi dashi ba, Zuciyarta na raya mata ta janye fushin ta kan Yusrah, ta maida akalar rabuwar Shatu da Mu'azzam kafin saura su biyo  baya.

********************************

"Yau daren amarcin naka ma sai kasha sigari baka gudun amaryar taji warin ta". Cewar NINJA yana duban Bashar dake ta faman zuk'ar sigari yana busawa,  "Kasan fa idan ban sha ba, bana ji na daidai gara nasha kara d'ayar nan". Ya sake zuk'a, "Toh Allah ya tsare tsautsauyi dai". Bashar guntun murmushi yayi, Sai da ya gama sha, Ya zaro toothpaste da brush cikin aljihun sa ya shiga band'akin NINGA, Ya d'auki kusan minti ashirin yana goge bakin sa, kana ya fito ya feshi bakin sa da mouth fresh tare da jefa chewing gum orbit ya soma taunawa, NINGA ya dube shi yace "Shege Nawan". Bashar yayi dariya, Ya d'auki mukullin motar sa ya fita, sai da ya biya ya siya kaji kana ya nufi gidan sa dake HOTORO,

A daren ranar zallar k'auna ya nunawa Yusrah wacce tasa ta manta damuwar da take ciki wanda take ganin ba k'aramin dace tayi ba, Wanda da tayi kuskuren barin sa tayi asara.

**********************************

Kwanaki biyun da Shatu tayi Hadeja taji dad'in su sosai dan tayi zumunci wanda Allah yayi ta mai son yan' uwa, Farha rai bai so ba zasu koma, taso a barta garin ba Umma tace su dawo dan kwana biyun da basa nan kad'aici ya mata yawa, Har waje su Inna suka musu rakiya suna d'aga musu hannu, Gidan IYA suka biya tayi mata sallama,

Su Saratu sun tafi talla, ita kad'ai ta tarar gidan, "Ina fatan kinzo d'aukata ne mu tafi dan tuni na had'a kayana". Shatu ta numfasa tace "A'ah nazo miki sallama ne dai zan koma, sai naje can muyi magana dashi sai direba yazo ya d'auke ki". "Ja'ira ni zaki ma wayo, ko uwar ki ba zata mun wayo ba balle ke, to wallahi kwana biyu na baki matuk'ar baki aiko an tafi dani ba zan taho da kai na, shi mijin naki ai nasan ba zai kore ni ba". Shatu kasa cewa komai tayi sai rafar d'ari biyar da ta ajiye gaban IYA, Ta mik'e da cewa "Mun wuce". Gudun maganganun da tasan IYA zatayi yasa bata ce su Farha su shigo su gaishe ta,
IYA ko godiyar kud'in bata yi ba saboda k'udurin ta na son bin Shatu, a ganinta idan taje can zata tara arzik'i, nan kad'an suke yagowa suna aiko mata.

Shatu cike da tunanin yadda zata tunkari MU'azzam da maganar suka bi hanya, Anya ba zata rok'i UMMA siyan ma IYA gida ba anan had'eja ba, dan a ganinta kamar gidan ne bata so, Shawarar haka ta zauna mata a zuciya har suka iso garin KANO,

Sai da suka fara ajiye SHATU gida, kana direban ya wuce dasu Farha, ba komai yasa tace a fara ajiyeta ba, sai gudun had'uwa da Hajiya,

Tana danna doorbell aka bud'e k'ofar, Mu'azzam ne hannayen sa bud'e ba k'aramin kyau ya mata cikin shigar shadda fara sabuwa dal tamkar wani ango, tayi mamakin ganin sa gida a tunanin ta ya tafi kasuwa, Shigewa tayi jikin sa yayi mata kyakkyawar runguma, K'amshin turaren ta ya saka shi jin wata natsuwar zuci, A hankali yace "Nayi missing d'inki sosai SHATUNA, daren jiya sai naga yamun nisa saboda k'aguwa safiya tayi na soma k'irga awanni ganin ki". "Ashe bani kad'ai ba ce naga tsawon daren jiya". Ta fad'a, "Dan Allah ki hak'ura da tafiya ba tare dani ba, kwana biyun nan kinsan yadda na azabtu kuwa". "IN shaa Allah" Ta furta, Tana k'ara shaida zazzafan k'aunar da yake mata, Hot kisses ya soma bin ta dasu, Itama tana mayar masa dan ba k'aramin kewar mijin ta tayi ba.

Naso na muku yafi haka kuyi manaji mu had'u gobe

OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now