HS 53

114 18 6
                                    

HALACCIN SO
Zee Yabour
*53*

Shatu tashi tayi zaune cikin kid'ima da furucin sa, Ibrahim ma nunfashin sa ya d'auke na wucen gadi yayin da wata zufa ta ruftu masa, Hatta Saratu da Jummai dake gefen furucin ya dake su, Mu'azzam fuskar sa babu annuri ko da na sanin furucin sa ya dubu Ibrahim yace "Ka fita, ban amince wani ya tsaya kan matata ba". IYA ce ta turo k'ofar da k'arfi da cewa "Babu inda za shi sai dai kai ka fita, dan shine mijin ta banda giftawar wannan galbararren cikin". "Enough!" Ya fad'a da k'arfi tamkar wani sabon soja, IYA sai da hantar cikinta ta kad'a tayi gum, "Babu wani mahaluki dake da iko kan canza cewar SHATU matata ce, haka babu wanda zai amsa sunan mijinta sai ni MU'AZZAM, ciki kuma sai yazo duniya da izinin Allah". Ibrahim zuciyar sa ke wani zafi yayin da kansa ke sara masa tamkar ana buga masa guduma bai tab'a tsintar kansa cikin tashin hankali irin na yau ba, sai dai bashi da jayayya sanin hukuncin Miji ya maida aure idan mace na cikin idda, ko iyayenta basu isa hana ta ba, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya furta, Yana kai duban sa ga Shatu, Idon Mu'azzam a kansa yace "Ka san haramcin kallon matar wani, so please out" Ya nuna masa k'ofa, Ibrahim juyawa yayi ya fice, Shatu tabi bayansa da kallo cikin tausayawa, tana son Mu'azzam so mai tsanani son da kullum take kwana tana tashi dashi, son da ta kasa cirewa sai dai kullum take k'ok'arin binne shi a zuciyar ta, son da take son maye na ibrahim dashi, sai dai zuciyarta ta kasa bata wannan damar, Amma tana tausayin Ibrahim sosai ya nuna mata so da halacci, Farin ciki zatayi na komawa gidan Mu'azzam d'auke da cikin sa ko bak'in ciki na Ibrahim, "Allah ne ya tsarawa faruwar haka bake ba, ikon sa wanda shi ke sawa ko ya hana". Cewar wani sashe na zuciyarta, Idon ta ta mayar ta rufe tare da addu'ar Allah yasa haka yafi zama alkhairi, Mu'azzam idon sa a kanta yayin da yake jin haushin ta sosai, tamkar ya rufeta da duka yaga kallon da tabi Ibrahim dashi, hakan ya sake fusata zuciyar sa,

"Daga asibiti gidana zaki wuce ban amince kije ko'ina ba" Yana fad'ar haka ya wuce, SHATU mamakin zafin sa take yanzu, tamkar ba Mu'azzam d'inta ba mai sanyin hali da far'a, maganar sa ma yanzu cikin zafi yake yin ta, Numfashi taja tana sake gyara kwanciya da addu'ar Allah yasa hakan ya zama alkhairi gareta, tabbas tafi son rayuwarta da Mu'azzam akan kowane namiji, abunda yasa ta bar sa yanzu ya samu, Tuna Na'ima yasa gaba d'aya yanayin ta canzawa, "k'ila itama tana d'auke da juna biyu, yanzu mun zama mu biyu wurin Yaya Mu'azzam shikenan zan yi sharing d'in shi da wata" Tayi zancen zucin cikin karaya, "Allah ya tsara hakan cikin k'undin k'addarar ki" Cewar wani sashen na zuciyarta, "Allah ya sassauta mun kishi ya bamu zaman lafiya dashi da ita". Tayi addu'ar a ranta,

"Ke kuma sauna kina ji yana zartar da hukunci kanki ba zakiyi magana, kin wani bi sa da ido, kin dai san irin halin su sahura, matuk'ar kika koma, uk'ubar yanzu sai tafi ta da, dan sai kin gwammace kid'a da rawa, shi kansa cikinsa yake ma bake ba, zaki koma tankar bora ne" IYA ta fad'a da fatan yin galaba kan Shatu, "IYA dan Allah meyasa yanzu kike adawa kan alak'ata da Mu'azzam, duk wani abu kansa k'ok'arin dak'ile sa kike, zancen ciki kina ta nuna adawar ki, fad'uwar da nayi ma tamkar abu aka zuba mun bakin k'ofa na zame". "LAAA sharri zaki mun Shatu, daga ina son ceto rayuwar ki daga uk'uba ina son baki gata da yancin kan ki, yanzu sharri zaki mun kice na zuba miki abu lallai Shatu kin isa". "To IYA naga bamu tab'a zancen aurena dake ba, kuma hasalima da kina nuna son Mu'azzam, lokaci d'aya kika fara adawa dashi". "Ke jakar ubanki, ko ubanki marigayi bai isa tsare ni balle ke, shashashar yarinya ai sai kije can ki k'arata ni na cire hannuna a lamarin ki". Ta mik'e ta fita zuciyarta na dukan uku-uku kada Shatu ta gano shirin su da Anty Sahura,

Shatu idan da sabo ta saba da halayyar IYA tun tana yarinya hantara ce tsakanin su babu wani dogon sakewa, ko zumud'i na ganinta batayi duk sanda suka zo, Kanta ta mayar kan pillow ta runtse ido tana tuna irin soyayya da rayuwa mai dad'i da sukayi tare da Mu'azzam, rashin haihuwa shine babban nakasu a auren su tana kyautata zaton yanzu rayuwar aure nasu zata fi baya dad'i.

*************************

Mu'azzam motar sa ya shiga, tare da kwantar da seat ya kishingid'a, ya lumshe ido, gani yake tamkar idan yayi nisa da asibitin wani abu zai iya samun cikin sa, dan haka ya yanke shawarar buk'atar sallamar ta gobe da safe su wuce Kano, "Me zaka cewa Hajiya? Kasan ba zata tab'a karb'ar ta a karo na biyu?" Ya tambayi kansa, Dogon numfashi yaja yana nazarin yadda zai tare ta da zancen amma yasan komai zai zo da sauk'i, Na'ima ta fad'o masa rai, Ya kira ta, Wayar na hannun ta ringing d'aya ta d'auka,

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now