HS 10

112 21 0
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na Goma

Mu'azzam sunyi waya da Alhaji amma bai sanar dashi bayanin Dr ba ya bari sai sun dawo nigeria, Shima Alhajin bai tambaya ba duk da ya k'agu da son ji tare da fatan an dace,

Tafiyar sai ta zamar musu tamkar honeymoon, Soyayya mai cike da kulawa ke gudana tsakanin su, Kullum sai sun fita wurin shak'atawa da more rayuwa, Mu'azzam k'ok'arin sa ya kawar mata da damuwa ta hanyar hanata dogon tunani, Yayi nasarar kawar da kaso mafi yawa daga damuwarta, Ta k'ara fawwala Allah lamuran ta tare da kai kukanta gare sa, Mu'azzam sai yake ji tamkar suyi zaman su anan d'in da babu damuwar kowa, Babu mai ganin SHATU balle ya jefeta da munanan kalamai,

Zaune suke bakin k'aramin swimming pool k'afafun su cikin ruwa, hannun su rik'e da juna, "SHATUNA sai nake ji tamkar mu cigaba da rayuwar mu anan", Murmushi tayi tace "Mu bar iyayenmu dawa", Dariya ta bashi yace "Kamar dai sune yaran mune iyayen", "Yadda yara ke b'ukatar kulawar iyayen su, haka muma iyayen akwai wata kulawar tamu da suke buk'ata", "Hakane amma wa'inda aiki ke kamawa fah suyi nesa da gida na tsawon lokaci", "Suma dole ce tasa, mu kuma ba aikin komai sai mu dawo nan", "Ke dai kawai kice yar' lelen Umma ce bakya son nisa da ita", Murmushi tayi k'asan zuciyarta bata k'i suyi rayuwar tasu anan ba, sanin halin Hajiya da ahalin sa za'a ce ta nesanta dashi dasu, yanzu ma ya aka k'are balle sunyi nisa dasu, tana da tabbacin da zata nuna mishi son dawowar ko shakka babu zai bi duk wata hanya dan ganin sunyi relocating , ko da kuwa ba germany bane wata k'asa, Sun jima a wurin suna hira cikin shauk'i da k'aunar juna, gabatowar magrib yasa suka tashi zuwa masaukin su.

**********************************

Hayak'i mai k'auri ke fitowa daga d'akin yayin da sautin kid'a ke tashi kad'an kad'an, Tarin samari ne su biyar kowane rik'e da abun shaye shaye, Biyu daga ciki na rik'e da shisha pot, D'aya sigari, Bashar dake gefe jingine da bango tabar wiwi hannun sa yana busawa, "Baaba wai ya maganar yarinyar nan ne kar kayi wasa da damar ka fah, idan ka aure ta ba k'aramin kaya zaka ja ba", Cewar D'aya daga cikin su, "Ina kan k'ok'ari NINJA babban burina na mallaki dukiya wacce za'a rik'a jin sunana a fad'in nigeria", "In dai ka sameta ai magana ta k'are, nasan kanka naja komai na ALHAJI HALI INUWA zai dawo k'ark'ashin ka", Bashar hayak'in wiwin ya busu tare da yin shu'umin murmushi, Bashar green snake kenan(FUSKA BIYU), A gaban mutane natsattse ne mai addini a bayan fage babu tantirin sa kan sa wanda abokan sa sun sarawa iya shegen sa, Kaf ahalin nasu babu wanda yasan yana shaye shaye hatta sigari zaka rantse baya sha, Ya iya takun sa ta yadda ba'a ganewa, tun yana secondary ya tsunduma harkar, Yana da wani lipstick mai tsada da yake amfani dashi na hana labb'an sa yin bak'i, baya tab'a bari aji warin wani kayan maye tare dashi,

Sai da ya kammala shan tabar wiwin sa, Ya zare jallabiyar dake jikinsa ya shiga band'aki yayi wanka, Ya saka kayan da ya shigo dasu, NINJA ya kallesa yace "SHEGE NAWAN baka da sauk'i fah", Yayi dariya, yana d'aukar mukullin motar sa da wayoyi ya fita.

*******************************

"Babe ba wani kud'i ne a hannunki na samu na kati" Cewar Faruk, Na'ima murmushi tayi tace "Nima d'ari bakwai ce, dama dubu d'aya Mama ta bani kud'in napep", (Tayi k'arya da cewa zata dubiyar k'awarta bata da lafiya, tazo wurin shi), "To ki bani d'ari biyar nasan d'ari biyu zata mayar dake gida", Ba musu ta zuge zip na jakarta ta fiddo ta basa, Ya karb'a da yin murmushi yace "Shiyasa nake sonki, Allah ya nuna mun nima nayi kud'i muji dad'i", Dariya tayi tace "Amin", "Wai ya zancen had'in da ake son miki da dan'uwan ki", Numfashi taja tace "Hmm wallahi Mama fa tana nan kan bakanta sai na aure shi", "Wow" Cewar Faruk babu wata alamar damuwa kan fuskar shi, Kallon mamaki tabi shi tace "Ban gane ba, wow fah kace", "Eh mana ai abun murna ne", "Abun murna fah kace Faruk ana zancen had'ani da wani kamar dai baka kishi na", Murmushin gefen baki yayi yace "Ke kan ki kinsan irin tsananin son da nake wanda kishin ki dole ne", "Idan hakane meyasa kake murna da had'in aurena da wani ba kai ba", "Babyna kenan, zuwa gaba zan fahimtar dake, yanzu ki koma gida kafin Mama ta fara neman ki", Sai da ya mata peck a kumatu kana ta tafi cike da soyayyar shi, Faruk gyara zaman shi yayi kan kujera tare da shafa k'asumbar da ya soma yace "Farouk millionaire wow", Ya dunk'ule hannunsa ya naushe iska yana wata irin dariya.

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now