HS 32

67 12 1
                                    


HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na talatin da biyu

Daren ranar Shatu da Mu'azzam tamkar zasu had'iye juna tsabar so, Sai take jin ba zata k'ara tafiyar ko kwana d'aya ba tare dashi ba, Shima yake jin ba zai sake barin tayi nisa dashi ba ko na dogon yini ne, Sun so makara sallar asuba dan bacci bai d'auke su ba sai uku na dare, Mu'azzam ya fara farkawa da sunan Allah a baki, gefenta ya kallo ta k'udundune cikin bargo da alama baccin yana mata dad'i, A hankali ya soma mata tafiyar tsutsa kan fuska, Ta bud'e lumsassun idonta tana kallon sa, "Ki tashi mun kusa makara". Jin haka tayi saurin yakice baccin dake son rinjayarta ta tashi, Ya kama hannun ta har zuwa band'aki sukayi wankan tsarki tare, towel d'aya ya rufa masa a jiki, Basu tsaya shafa ba kasancewar wankan tsarki ne, Mu'azzam jallabiya kad'ai ya zura, Shatu ta saka k'aramar riga tare da dogon hijabi yaja su jam'i.

**********************************

Hasken rana da ya dalle d'akin yasa Bashar yin wata mik'a yana jawo wayarsa ya duba lokaci takwas saura, Yusrah ya d'an bubbuga alamar ta tashi, "Uhmm bacci" Ta fad'a tana gyara kwanci, "Ki tashi muyi sallah". "pls bari na d'an k'ara bacci". Ta fad'a tana jan bargo, Sam Hajiya Hafsatu bata koyawa yaranta tashi sallar asuba ba, Sallar ma dan suna zuwa islamiyya suka koya da sanin muhimmancin ta, Bashar k'yaleta yayi ya shiga band'aki yayi wankan tsarki had'e da wanka, Ya fito yayi sallah, Ya koma kan gado ya kwanta yana danna wayarsa, k'arar status da yake bud'ewa ya tashi Yusrah, Cikin hanzari tayi wankan ta gabatar da sallah ganin lokacin yaja sosai duk da ba kasafai take tashi sallar asuba ba amma bata kai irin lokacin nan, Har ta kammala shirin ta, tayi kyau ta fito sak a amarya, Yana kwance kan gadon yana danna waya, Kusa dashi ta zauna, Ya dubeta tare da kama hannun ta yace "Kinyi kyau wifey". Murmushin jin dad'i ta masa, Ya murza hannun kad'an yace "Ina so na tambayeki kuma na baki shawara". Kai ta jinjina alamar tana sauraro, "Dukiyar ki ta gado me kike tunani yi da ita?". Baki ta d'an tab'e tace "Bani da plans na komai". "Dama nasan ku mata yana da wuya kuyi tunanin juya kud'in, kuma bai kamata a barsu haka ba, suna hannun waye?". "Wasu na account d'ina wasu na hannun Yaya Mu'azzam". Jim yayi kana ya jinjina kai yace "Na account d'inki ki kawo na juya miki, na hannun Mu'azzam kice ya saka cikin business d'in shi". "meyasa ba zaka karb'a duka ba?" Ta tambaya tana duban sa, Kai ya girgiza yace "Gara a raba hannu, kuma Mu'azzam yafi ni samu da sanin hanyoyin da zai bunk'asa miki kasuwancin ki". Kai ta jinjina alamar gamsuwa tace "Kai ma ina fatan watarana ka shahara a ji sunayen ka a k'asashen duniya ba ma nigeria kad'ai ba". Kallon ta yayi cike da farin cikin zancen nata yace "Da gaske wifey". Kai ta jinjina masa alamar tabbaci, Janyota yayi jikin sa yana jin komai zai zo masa da sauk'i.

********************************

"Sai nake jin kamar kada na tafi kasuwa na zauna gida nayi ta kallon ki har na d'ebe kewar kwanaki biyu da nayi ba tare dake ba". Cewar Mu'azzam dake tsaye bakin corridor yana duban Shatu ta masa rakiya, "Ni kaina ban k'i ka zauna a gidan nayi ta kallon ka ba, sai dai zuwa kasuwar yana da matuk'ar muhimmanci". Kai ya d'aga yace "Haka dan ga vibrating na wayata na tabbata daga can ake kiran". "Toh Allah ya bada saa sai ka dawo". "Amin". Ya fad'a ya sumbaci goshin ta ya fita, Ta koma cikin gida, Zama tayi falo ta d'auki remote ta kamu tashar arewa, ganin shirin da suke yasa ta maida hankalinta kai.

*******************************

Zulfa'u ce zaune tsakar gida da littafi gabanta tamkar mai karatu amma ba karatun take ba, zurfin tunani ta tafi, Halimatu da ta shigo gidan tana ta faman sallama shiru har ta k'araso kusa da ita ta tab'a ta, Tayi zumb'ur ta juyo, "Tunanin me kike haka da ya d'auke miki hankali da yawa". Dogon numfashi taja tace "Rayuwa YAYA Halima, ki duba irin rayuwar da muke, mahaifin ka baya iya d'aukar hidimar ka, dama Alhaji ne ke taimaka mana yau babu shi, zamu fara zana jarabawa ba'a biya mun kud'in waec da neco ba, kuma ance duk wanda bai biya ba ba zai zana ba". "Hmm ina ganin ki hak'ura da makarantar zai fi". Saurin kallon Halimatu tayi tace "In hak'ura fah kika ce bayan har na kai matakin k'arshe". "Shi na gani mafita amma ina zaki samu kud'in, ni kaina nan fad'i tashi nake ina biyan nawa". "Amma Yaya Halima wane aiki ne kike ne kike samun kud'i haka". "Aikin da ba kowa zai iya ba". "Dan Allah ki fad'a mun komai wahalar sa zanyi in dai zan samu kud'in zana jarabawa". "Ki hak'ura da aikin nan ki nemi wata hanya". Tana fad'ar haka ta wuce bata jira cewar Zulfa'u wacce tabi bayanta da kallon mamaki, Tagumi ta rafsa tana tunani mafita Mu'azzam yazo mata a rai sanin shi kad'ai ne mutumin da zai iya taimakon su kan tsaye bayan Alhaji, ba halinta bane rok'o amma dole ce tasa haka yasa ta yanke shawarar kiran sa a waya ta sanar dashi, dan tana jin kunyar samun shi a fuska.

******************************

Shida daidai Mu'azzam na k'ok'arin fitowa ofishin sa Kawu Kabiru ya shigo, Cikin ladabi yace "Kawu barka da yamma". "Yawwa har ka tashi ne". "Eh". "Dama wata yar' shawarar nazo muyi". Mu'azzam yace "Toh yana komawa ya zauna". Shima Kawu Kabiru ya samu wuri ya zauna, Ya dubi Mu'azzam yace "Wani business aka talla ta mun wanda idan akayi In shaa Allahu za'a samu alkhairi sosai, kuma kud'in da ake buk'atar a saka bani dasu duka, shine nace ko zaka bada muyi had'aka k'aruwar mu gaba d'aya". Mu'azzam ya numfasa yace "Wane irin business ne?". "Na wata kwangila ce na ginin estate". Mu'azzam ya jinjina kai yace "Ko zaka iya had'ani dasu mu k'ara tattaunawa". "Wacce tattaunawa Mu'azzam kamar dai kaine babban nine k'aramin kasan dai bazan tab'a kawo macuta harkar nan ba, komai sai da muka gama tsarawa kana nazo maka da zancen". Mu'azzam jim yayi kana yace "Shikenan Allah ya dafa mana". Kawu Kabiru yace "Amin ko kai fah". Sukayi sallama Kawu Kabiru ya fara fita ofishin kana Mu'azzam ya rufa masa baya.

******************************

Anty Sahura ke ta faman kai kawo a d'akin duk kwanakin nan bata samun wadataccen bacci saboda k'udurin ta na son raba Shatu da Mu'azzam cikin gaggawa, kuma ta hanyar da ba wanda zai zarge su, Tsawon minti talatin bata saka d'uwawunta da sunan zama ba, sai safa da marwa tamkar mai nak'uda, Shawarar da tazo mata k'arshe yasa tayi murmushi da cewa "Ina tunanin wannan karon zamuyi nasara". Taja da baya tana zama bakin gado, ta ciji labb'an ta na k'asa, Na'ima ce ta shigo d'akin babu sallama, Anty Sahura ta jefa mata harara, "Lafiya kika fad'o mun d'aki ba sallama". "Yi hak'uri Mama, hankalina ne a tashe wai an kai k'awata Naja asibiti ba lafiya". "Subhanallah Allah ya sawwak'e". "Amin". "Duba drawer can ta madubi ki d'auki kud'in napep nasan su kika zo tambaya". Godiya tama Sahura ta d'auka ta fice cikin sauri, wurin Farouq zata je ba shine abokin sa ya kirata bashi da lafiya,

*********************************

Shatu na jikin Mu'azzam suna hira cikin raha, wayar sa tayi k'ara tamkar ba zai d'auka ba ganin bak'uwar lamba, Ya yanke shawarar d'auka da tunanin maybe important call ne, A speaker ya saka, Cikin murya mai sanyi aka ce "Assalamu alaikum" Shatu jin muryar mace k'irjinta ya doka (sarkin kishi😂) Mu'azzam shima kallon ta yayi kana ya amsa sallamar niyyar sa ya kashe amma yanayin da ya gani kan fuskar Shatu yasa ya tsaya gudun zargi, "Ina wuni Yaya Mu'azzam". "Lafiya, wake magana?". "Zulfa'u ce". mamaki ya kama sa ganin bata tab'a kira sa ba, "Ya mutan gidan?". Ya tambaya a dak'ile, "Lafiya lau, da...m...a da....ma.... Da.." Ta soma rawar murya wanda Mu'azzam yayi shiru yana saurare, Cikin dakiya tace "Uhmm da...ma kud'in registrat....". Bai bari ta k'arasa ba yace "Zan aiko da safe In shaa Allah". Zata fara masa godiya yayi saurin tarar numfashin ta, kana ya kashe wayar,

Numfashi yaja tare da girgiza kai yana mamakin son kud'i irin na Kawu Kabiru da baya na iyalan sa komai, a ransa yace "Allah ya kyauta". kana ta dubi Shatu da ta lafe jikin sa, Yace "Uhmm har kinji kishi ko". Dariya tayi, Ya kama hancin ta yace "MU'AZZAM mallakin shatu ne ita kad'ai", Sumba ta kai masa, Suka yi dariya.

**********************************

Kwance ta tarar da Farouq yana numfashi sama sama cikin tashin hankali, ta k'arasa tamkar zata yi tuntub'e, "Meye sameka haka baby?". Abokinsa dake gefe yace "Ciwon ciki". "Ya ba'a kaishi asibiti ba". "Mun je sun bashi magunguna". Ya jawo wata leda gefen sa ya nuna mata, Ta duba kana ta maida kallon ta kan Farouq tana jera masa sannu, Bata jima ba ganin dare ya soma sosai dan kusan takwas da rabi, ta tafi da cewa gobe zata dawo, Farouq sai da ya dakaci lokacin da yake kyautata zaton tayi nisa, Ya tashi zaune da tuntsirewa da dariya, Suka tab'a da abokin sa, Yace "Abokina baka da kirki wallahi kaga yadda hankalinta ya tashi". Dariya yayi yace "Ka bari kawai". "amma meye ribar ka na haka". "Zaka sani zuwa gaba". Ya fad'a da yin dariya.

*************************

Washegari Mu'azzam da wuri ya fita kasuwa, Shatu na falo kwance tana kallo, doorbell tayi k'ara ta taso ta bud'e, Ganin Anty Sahura yasa gabanta fad'uwa wanda fad'uwar gaban yau yasha bambam da na kullum, Shatu cikin girmamawa ta gaisheta ta amsa da cewa "Lafiya". Ta zauna kan kujera, Shatu kamar kullum ta zauna takure wuri d'aya, "Zuwan yau musamman saboda kece kuma magana nake so muyi dake ta fahimta". Cewar Anty Sahura, Shatu hankalinta ta tattaro kan Anty Sahura tare da fatan ko mene ya zama alkhairi, Anty Sahura ta k'ara gyara zama da murya tace "

OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now