HS 59

98 19 5
                                    

HALACCIN SO
Zee Yabour
*59*

Ba k'aramin sanyi jikinta yayi ba, tana k'ara tsinkewa da lamarin Anty Sahura, yayin da komai yake dawo mata tar, kama daga ranar da Anty Sahura tazo gidan kan tana so suyi magana, har kan zuwa sanar da ita bata haihuwa, da takardar data kawo mata na result na sibiti, Tunani ta zurfafa, duk sanda suke zuwa asibiti gwaji, Mu'azzam baya keb'ewa shi kad'ai balle har ya umarci likitocin su b'oye cewar bata haihuwa, suna zaune tare ake buk'atar ganin su office d'in, ko a gaban su a kawo result, "Tabbas shiri ne irin nata dan ta raba ku, duba da sun bi kowacce hanya sun gaza" Zuciyarta ta fad'a, Wani haushin kanta taji ya lullub'eta na kasa tsayawa tayi dogon nazari a lokacin da Antu Sahura tazo mata da zancen, bayan tasan babban burinta su rabu, Kuma me ma ya hana mata zuwa asibiti dan tabbatar da gaskiyar zancen, Kanta ta d'an dafe tace "Ubangiji ya tsara faruwar haka, babu wani bawa da ya isa tsallake k'addarar sa". Tayi zancen tana jin takaicin nata ya rage, "Taya zan warware wannan abun, Yaya Mu'azzam ya fuskanci ban yaudare sa ba?" Ta tambayi kanta, Ko kusa yanzu tasan bazai saurare ta ba, haka ba zata so dan ta wanke kanta shi kuma ta lalata alak'ar dake tsakanin sa da k'anwar mahaifiyar sa watak'ila ya shafi har auren Na'ima, ba zata zama mai son kai ba, sai dai zata cigaba da rok'on Allah ya dawo da soyayyarta zuciyar shi, ya daidai tsakanin su".

Fitsarin da batayi ba, taji ya sake dawo mata, ta shiga tayi cikin bath tare da shek'e ruwa da yawa ta fito, Umma ta kira ta gaisheta dan tana buk'atar albakar ta, Ta saka mata albarka tare da mata addu'o'in tsari, Bayan ta kashe ta kira Mahaifiyar Ibrahim, Sosai taji dad'in kiran Shatu, tayi ma mata godiya tare da addu'ar fatan alkhairi har tace In Shaa Allahu idan ta haihu zasu zo suna, Shatu ta kashe tare da k'ara mamakin kirki, mutunci da dattako irin na Mahaifiyar  Ibrahim, "Allah ya bashi mata ta gari shima". Ta fad'a da ajiye wayar ta kwanta.

********************************

Kawu Kabiru tamkar wanda aka koro ya fad'a shagon wanda aka rubuta M&S ENTERPRISES, "Shago har shago ga dukiya mak'il amma yan' damfara watak'ila ma duk dukiyar jama'a ce, to ni wallahi ba zasu ci kud'i na ba". Yaron da yayi jagora aka siyan kayan wurin sa ya taso da cewa "Lafiya dai". Yaron Kawu Kabiru zai yi magana yayi caraf yace "Ina fah lafiya kun damfaremu kun had'a mu da yan' biyar biyar to wallahi ko kud'ina ko kayana". "Subhanallah gaskiya kuskure aka samu". "Kun shirya damfara dai ni yanzu dai a bani kud'i ko kaya". "Muje ciki to kaga ogan namu". Kawu Kabiru yace "Muje" Yaron yayi gaba yana bin sa baya, A ransa yana k'ara jinjina girmar shagon wanda yake mak'il da kaya iri iri hadda furnitures iri iri, su carpets electronics, A ransa yace "Mallakin wurin nan ba k'aramin kaya yaja ba, ina jin ina ma mallakar sa ce, amma da sannu zai mallaki wanda yafi sa ma"

Ofishin da suka shiga yasa shi kusan rud'ewa ya gansa tamkar turai, "Maigida ga ogan namu ko kuyi magana" Kawu Kabiru ya d'ago kai da k'arfin sa, Turus yayi k'irjinsa ya masifar bugawa ganin Mu'azzam hakimce kan kujerar mallakin ofishin, "Mu'azzam" Ya fad'a da son tabbatar da abunda idon sa suka gane masa, "Na'am Kawu". Hanjin cikin sa suka hautsina take zufa ta wanke sa, Gudu zai yi ko me, yana jin tamkar k'asa ta bud'e ya shige,

"Bismillah" Mu'azzam ya fad'a yana masa nuni da kujerar dake kallon sa, Wasu yawun tsoro da firgici ya had'iya, K'afar sa tamkar an d'aura masa k'aton dutse tsabar nauyin da ta masa da k'yar ya d'aga ta zuwa kujerar ya zauna, Sam ya kasa kallon Mu'azzam, "Kawu dama kasan da wannan wurin nawa ne". Wata ajiyar zuciya ya sauke a ransa yace "Alhamdulillah ashe bai san me ya kawo ni ba". A zahiri yace "Eh Eh fah shine nazo gani". Mu'azzam murmushin gefen baki yayi ya kalli yaron sa dake gefe yace "Ka shigo dasu". Yace "Toh Ranka ya dad'e".

Garba da Nafi'u da ya aiko wurin Mu'azzam ne suka shigo kowanen su ya had'a gumi, Kawu Kabiru baya yayi cikin razana k'iris ya rage ya fad'i kan kujera, Mu'azzam ya kalle sa yace "Kayi mamakin ganin su ko". Kawu Kabiru kai ya girgiza yace "Ai bansan su balle nayi mamaki". "k'arya kake wallahi ba kai ka aike mu wurin sa ba" Garba ya fad'a, "A gidan uwar wa na sanka sharri zaka mun". Nafi'u yace "Mu zaka k'aryata ai muna da shaidar komai".

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now