HS 25

99 15 0
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na ashirin da biyar

Alhaji Hali da Kawu Kabiru suka nufi ofishin yan' drugs, Su Lamid'o tare da Mu'azzam suka koma kasuwa, Kawu Kabiru hankali tashe ya shigo,  Alhaji kuwa ambaton Allah yake yana rok'on ya kawo masa mafita ga masifar dake kunno kai ahalin su, Kamar lokacin Mu'azzam yau ma ofishin ogan nasu suka nufa, 

"Yallab'ai wallahi Bashar bai aikata ba sharri ake bin ahalin mu dashi", Cewar Kawu Kabiru cikin damuwa, zuciyarsa na bashi tabbacin Bashar ya shigo da k'wayoyin ne ya siyar saboda kud'i, Ogan numfashi yaja yace "Ba zamu tabbatar da haka ba sai mun gudanar da bincike", Alhaji ya numfasa yace "Dan Allah ku duba lamarin, ko bailing sa ne ku bamu", Ogan girgiza kai yayi yace "Wannan case yafi k'arfina duba da a airport aka kama shi, manyan jami'an tsaro sun san da case d'in bani da iko na zartar da komai", Kawu Kabiru zufa ta shiga karyo masa, "Ya salam" Alhaji ya furta tare da dafe kai, "Sai hak'uri kawai" Cewaf Ogan, Alhaji duban sa ya kai ga Kawu kabiru yace "Addu'a ita zamuje mu cigaba da yi", "Alhaji wallahi bazan iya tafiya yanzu ba", "Zaman namu nan bashi da amfani gara mu koma gida mu dage da addu'a", Kawu kabiru ya sake cewa "Ka tafi Alhaji zan biyo ka", Alhaji rai jagule ya mik'e yayi sallama da ogan ya fita,

Kawu Kabiru sai da ya tabbatar Alhajin ya wuce, Ya dubi ogan yace "Hamisu wai da gaske kake babu wani taimako da zaka iya ya fita", "Da gaske nake Kabiru wannan case yafi k'arfina", "Ina ce kana cikin manya akwai hanyoyin da zaka iya bi a fitar da Bashar", "Babu wata hanya da zan iya wallahi", "Haba Hamisu tsawon shekaru nawa muna tare, ka duba amintakar dake tsakanin mu kayi wani abu", "Kabiru na fad'a maka bazan iya komai ba, kuma wannan abu da ya faru ya kamata ya zamar maka izna", "Ban fahimta ba", "Sharrin da ka k'ullawa Mu'azzam shine ya dawo maka, hausawa sunce shi sharri dan' aike ne duk inda ka aika sa sai ya dawo", Kawu Kabiru jim yayi zuciyar sa na tabbatar masa hakane yayin da wani b'angare na son rai ke danne masa gane kuskuren sa, "So da zaka koma gida yafi maka dan zamanka ne b'ata lokacin ka kake", Cewar Hamisu, "Kana magana tamkar ba da had'in kan ka komai ya faru ba" Kawu Kabiru ya fad'a, "Ko menene shirin ka ne, kuma ni faruwar hakan tasa nayi nadama, bazan sake aikata haka ga kowa ba, dan gashi cikin k'ank'anin lokaci Allah ya saka mishi, dan' cikin ka shine ya shigo da k'wayar", "Ya isa Hamisu Dan Allah", Kawu Kabiru ya fad'a cikin zafin rai ya mik'e ya fice office d'in,

Bashar ya buk'aci gani aka had'a shi dashi, Yana ganin Kawu Kabiru yayi saurin sunkuyar da kai k'asa, "Dole ka kasa kallo na ka tafka babbar ta'asa, banda kana mutumin banza ka d'auko miyagun k'wayoyi ka shigo dasu, son kud'in ka har ya kai haka", Bashar kasa cewa komai yayi sanin bai isa wanke kansa wurin Kawu Kabiru ba, "Abunda nake son sanar da kai, kada ka yarda ka amsa ka shigo dasu, ka tsaya kan cewar sa maka aka yi ba tare da ka sani ba", Bashar kai ya d'aga, "Da na san abunda zaka aikata kenan da ban bari ka tafi ba amma ka kori gobe, shashasha kawai", Ya wuce cikin b'acin rai.

***********************************

Mu'azzam rai jagule yau ya dawo gida, faruwar al'amarin Bashar ya sake jefa shi cikin rud'ani, da tunanin wa ke son ganin bayan zuri'ar su da b'ata musu suna, Kamar kullum Shatu ta tarbe sa cikin kulawa, peck ta masa a kumatu gefe da gefe, Suka k'arasa ciki, ko bai fad'a ba yanayin sa ya tabbatar  mata akwai abunda ke damun sa, ko meye tana fatan ba babba ba ne, "Rouhi yau na maka special girki", Ta fad'a tana masa narkakken kulawa, Kallon ta ya sa shi jin wani sanyi a zuciya yace "Me kika dafa Shatuna", "Bani minti biyu", Ta fad'a da murmushi, Bayanta yabi da kallo sonta na ratsa shi, zaman Shatu rayuwar sa ba k'aramar katanga bace dake bashi kariya da abubuwa da dama, Ciki hadda d'auke masa damuwa wanda ki wacce irin damuwa yake ciki ganinta na rage masa kaso mafi girma,

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now