HS 51

140 25 5
                                    

HALACCIN SO
Zee Yabour
*51*

Kallon Farha yayi sosai sanin baya wasa da ita da zata kawo masa zance irin wannan balle yace tsokanar sa take, Farha ganij kallon da yake mata taji tsoro ya shigeta cikin sanyin murya tace "Kayi hak'uri Yaya Mu'azzam ban san zan b'ata ma rai ba". Kai ya girgiza yace "Baki b'ata mun rai ba amma a ina kika ji?". "Gwaggo Jamila ce ta hadeja ta kira ta fad'awa mata wai tana da ciki". "Sai kika ji Umma tace me?". "Tace Ikon Allah Shatu d'auke da cikin Mu'azzam". Wani abu yaji ya dirar masa a zuciya yayin da yaji wani sanyi na jin zai zama Uba ashe yana da rabon ganin jinin sa a duniya, Murmushi yayi na farin ciki sai kuma take fuskar sa ta canza tuna Shatu ba mallakin sa ba ce yanzu, ta guje sa tayi auren ta, "Babu saurin igiyar wani kanta tunda tana d'auke da cikin ka, hasalima sai ta haihu zata fita idda". cewar zuciyar sa, Farha tace "Dan Allah kar kacewa Umma ni na fad'a maka zata dukeni tace nayi surutu". "Jeki school kar ki makara". Yasa hannu aljihu ya bata dubu biyar ta karb'a tana murna, Mu'azzam tsintar kansa yayi da nufar sashen Umma, yana son sake tabbatar da zancen Farha,

Karin kumallo suke tare da Teema, jefi jefi suna hira, Teema tace "Kamar sallamar Yaya Mu'azzam". "Mu'azzam kuma baki ji dai da kyau ba amma me zai kawo sa tun rabuwar su da Shatu ai baya shigowa". Sallamar da ya sake yi ya tabbatarwa Umma shine, Hijabi ne jikinta hakan yasa tayi ma Teema alamar ta mishi iso, tana mamakin me ya kawo shi, Mu'azzam kai sunkuye k'asa ya shigo falon, Ya gaishe da Umma ta amsa cikin sakewa, Zuciyar sa na son k'aryata masa abunda take basa duba da nagarta da kyawun hali uwa uba kirkin Umma yayin da zantukan Hajiya Hafsatu da Anty Sahura, maganganun IYA da ita kanta Shatu yadda bata k'aryata ba ke ture komai ya mamaye zuciyar sa da tsanar su, Ji yake tamkar ya tashi ya bar falon sai dai cikin sa da ke jikin Shatu ya zama dole yayi huld'a dasu yanzu har zuwa lokacin da zai zo duniya ya karb'i abun sa, Rasa ta ina zai doshi Umma da maganar yayi, duba da tun fil azal dama babu sakewa ko wata doguwar magana tsakanin su, Itama Umma shiru tayi tana son jin meke tafe dashi dan ta tabbatar banza ba zata sa ya shigo ba, Zuciyar sa ke ingiza sa yayi magana da nuna masa yana da kowacce dama na yin magana akan cikin sa, Cikin k'arfin gwiwa yace "Dan Allah ko Shatu tana ina?" Yayi zancen tamkar bai san tayi aure ba, Umma da mamakin tambayar ta kalle sa tace "Tana hadeja gidan mijin ta". "Tayi aure da cikina a jikin ta". "Kana nufin kunsan da cikin kafin rabuwar ku?" Umma ta jefo masa tambayar cikin d'aurewar kai, Mu'azzam shiru yayi muradin sa ya cika na jin tabbas akwai cikin sa jikin ta, bashi da haufi akan cewar nasa ne, duba da Shatu ba mutum bace me yawo da zai je zata fita tayi cikin banza, tun saninshi da ita bata kula samari a gaban kowa zai bada shaidar ba mutum bace mai huld'a da maza, Ba tare da yace komai ba, Ya mik'e ya fita, Umma tabi bayansa da kallon mai cike da mamaki, Ita kanta Teema mamaki ya cikata, A take Umma ta kira Shatu,

Tana kwance d'aki tana bitar karatu da wayarta, Kiran Umma ya shigo, ta d'auka, Bayan sun gaisa Umma tace "Shatu ina ilimi da hankalinki ya tafi, kin tab'a ganin anyi aure da ciki, kinsan kina d'auke da cikin Mu'azzam kika bari akayi aurenku da Ibrahim, ko baki da ilimi ne kan saki da idda", Shatu cikin sanyin murya tace "Wallahi bani da masaniya, ban sani ba sai ranar da mukaje asibiti da Ibrahim". "Kada ki mun k'arya Shatu bayan ina da hujja mai k'arfi na cewar kin sani". "Wallhi tallahi Umma ban sani ba, na rantse da Allah bani da masaniya". Umma shiru tayi tabbas tunda ta rantse haka bata sani ba, tasan halin Shatu sarai, hakan na nufin Mu'azzan ya sani kenan ya b'oyewa Shatu meye ribar haka, kuma meyasa tun rabuwar su bai nemeta ba sai yau, ko yaji labarin auren ne, shin meye babban dalilin sakin ma "Kin manta da Hajiya Hafsatu ita kad'ai ta isa raba tsakanin su" Cewar zuciyarta, Umma ta janyen tunanin da cewa "Shikenan, Allah ya sauke ki lafiya". Tace "Amin" Umma ta kashe wayar, Shatu ajiyar zuciya ta sauke da mamakin meyasa Umma zata mata wannan zargin bayan tasan halinta.

Umma kam gaba d'aya tunanin ta ya k'ulle wuri d'aya tana ta faman sak'a da warwara.

*******************************
Tun daga k'ofa yake jiyo fad'an ta tana zagi da cin mutuncin masu aiki, Kai ya girgiza cikin takaicin wannan hali nata, Yayi sallama ya shiga, Ta amsa da cewa "Mu'azzam an shigo". Yace "Eh, barka da safiya". "Yawwa"  tace a dak'ile, dama jiran sa take kamar yadda Asiya ta kawo mata rahoto ta gansa ya shiga sashen Umma, "Me ya shiga yi sashen wancan matar?" Hajiya Hafsatu ta fad'a, "Gaishe ta" Ya fad'a, "Kana da hankali kuwa, bayan duk abunda ya faru har kake zuwa gaisheta, matar da ke son ganin bayan ka, bata da mak'iyi irin ka, lallai yau na k'ara shaida baka san ciwon kan ka ba wallahi". Shiru yayi rasa me zai ce, hakanan yaji baya son sanar da ita zancen cikin yanzu, Mita ta cigaba masa da cewa "Tun wuri kasan me kake wallahi, idan ba haka ba wallahi sai ta kai ka k'asa, ko gantalalliyar Shatun kake son dawo da ita, bayan tayi auren ta ta manta da kai, sai kaine da har yanzu ka kasa cireta cikin rai, ka rungumi yar' uwarka mai sonka tsakani da Allah". Shiru ya sake yi, "Ai dama nasan ba tankawa zaka yi, ni dai na gaya maka gaskiya a matsayina na mahaifiyarka mai son farin cikin ka". "Zan je kasuwa". Ya fad'a, "Sai anjima" Cewar Hajiya Hafsatu babu far'a tare da ita, Tsoron ta su fad'a masa zancen cikin tunda har hankalinsa ya fara karkata ya shiga,

Yana fita ta kira Anty Sahura, Bata bari sun gaisa ba tace "Yaron nan yau ya shiga b'angaren shegiyar can tsorona su k'unsa masa maganar cikin". Anty Sahura tace "Ko sunyi a banza, ina da tabbacij yanzu cikin ya d'auki hanyar zubewa kiran kakarta kawai nake jira, bana da haufi kan malam wada". Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tace "Har naji natsuwa da hankalina ya tashi". "Ki daina damuwa Yaya ai kina dani". "Hakane Allah ya barmu tare". Anty Sahura tace "Amin" tare da kashe wayar tayi shu'umin murmushi, Ta soma kiran IYA, tana ganin kiran tak'i d'auka rashin sanin abun cewa har kiran ya tsinke, "Wallahi bazan bari wanann damar ta wuce ni, na rasa mak'udan kud'i masu yawa" Cewar IYA ta mik'e ta nufi kitchen,

Kofi ta d'auka ta zuba ruwa ta saka yauk'i ciki, Daidai k'ofar  d'akin Shatu ta zuba, Ta koma kitchen ta zubar da saura ta wanke kofin ta ajiye ta koma falo, Ihu tayi tare da kama cikin tace "Wayyo Allah cikina wayyo zan mutu ku taimakeni". SHATU wacce bacci ya soma fisgarta jin ihu IYA tayi saurin saukowa gadon ta nufi k'ofar fita, daidai nan santsi yaja ta ya fad'i, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta tana jin zafin fad'uwar, yayin da tabi k'afarta da kallo ganin jini na zuba.

Naso na muku yafi haka amma
Ina da uzuri mu hadu gobe

OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now