HS 49

119 20 1
                                    

HALACCIN SO
Zee Yabour
*49*

Haka ta fito tamkar mai sabuwar tab'in hauka, babu natsuwa kwata kwata a tare da ita, jefa k'afarta take ba tare da tana kallo gabanta ba, gaf da zata fita gate tayi kaura da wani k'aton dutse saurin duk'awa tayi saboda azaba, Duk da jinin da ya soma zuba bata bi ta kansa ba, Ta fice gidan, ta tari Napep,  Sai can jakara wani lungu, Zauren gidan cike yake da mata mak'il wanda suka zo wurin malamin(Allah ya shiryeku mata maimakon ku mik'a al'amuranku zuwa ga ubangiji sai malamn tsibbu wanda zuwa wurinsu ba tare da gaskata abubda sukace ba ba za'a karbi sallar ka na kwana arba'in ina ga wanda ya gaskata yayi shirka ga Allah, Allah ya ganar damu)

Dandazon matan ta ratsa ta kutsa kai k'aramin d'akin da yake ganawa da mutane, matan wurin suka bita da kallo kowacce na ayyana tana cikin tashin hankali hakan yasa ba suyi yunk'urin dakatar da ita da cewa taci layi, Daidai ya kammala data ciki zata fito, K'iris ya rage ta bangaje ta, Mushirikin ya dubeta yace "Hajiya ince lafiya dai ko?". "Wallahi ba lafiya ba malam, yarinyar nan da muke aiki kanta tana d'auke da juna biyu". "Anya kuwa kinyi aikin nan yadda yace". "Wallahi nayi mallam". "Har na barbad'awa cikin abincin su". "Eh wallahi Mallam wacce nasa ta bani tabbacin tayi". Jim yayi kafin ya jawo k'aramin allon sa na bugun k'asa ya fara, tsawon minti goma yace "Na gano inda matsalar take". "Ina matsalar take?" SAHURA ta tambaya tana duban sa, "Kangon da kika binne an tone shi". "Na shiga uku". Cewar Anty Sahura cikin tashin hankali, "Kema kinyi sakaci na binnewa wurin da kika san za'a yi tonawa". "Wallahi Malam tsoro ya hanani yankar daji sosai shiyasa nayi a wani kango". "Ai kinga matsalar". "Yanzu malam ba wani abu da za'ayi cikin ya zube kar yazo duniya". Dariya yayi yace "Akwai wani abu da zai gagare mu ne(Allah ya shiry) rai ne kad'ai bamu da ikon mayarwa mutum, amma ko kisa ne zamu kawar da mutum". "Yawwa a zubar da cikin Dan Allah". Kai ya jinjina yace "Aikin nada d'an wahala dan zai ci kud'i". "Kud'i ba damuwa bace matuk'ar buk'ata zata biya". "Da kyau, zaki bada dubu d'ari biyar amma fa aikij tamkar yankan wuka babu haufi kan sa". "Shikenan Mallam zan kawo yanxu ban zo da shiri ba". "Babu damuwa sai kin dawo". Ta mik'e ta fita tana jin sanyi a ranta na jin za'a zubar da cikin, Gidan Hajiya Hafsatu ta koma, A inda ta barta nan ta tarar da ita babu natsuwa tare da ita,

"Ina fatan an shawo kan matsalar". HAJIYA Hafsatu ta tambaya, Sahura ta numfasa ta zayyane mata komai ba, "Ba dubu d'ari takwas ba ko miliyan goma ne zan bayar matuk'ar cikin nan ba zai zo duniya ba, dan zuwan sa daidai yake da rushewar burina". Anty Sahura ta k'ara dubu d'ari uku kamar yadda take a duk sanda za'ayi aiki sai ta k'ara nata rabon, Tace "K'warai dan kuwa Shatu ta haihu da Mu'azzam babu rabuwa ta har abada tsakanin su tunda yaro ya shiga tsakani, haka dukiyar Mu'azzam da bakya so su gada, zasu gada ta hanyar yaron da ya shiga tsakani". "Tunanin hakan yasa tun farko nak'i bari ta haihu dashi, dan bana sonta cikin rayuwar sa, bana son kowacce alaka ta cigaba da wanzuwa bayan rabuwar su". "Hanya d'aya ce yanzu muyi k'ok'arin ganin cikin ya zube da gaggawa, zan kira kakarta tayi nata k'ok'ari na ganin maganar cikin bata fita ba, dan matuk'ar Mu'azzam yaji akwai matsala". Hajiya Hafsatu tace "Ko yaji bazan bari ya yarda nasa bane". Sahura tace "Bani kud'in na koma". "Zan miki transfe yanzu". Sahura ta jinjina kai.

*****************************

IYA hankalinta gaba d'aya ya karkata kan zubar da cikin SHATU, Da kanta ta fita taje chemist na bakin layin ta siyo maganin zubar da ciki, ta dawo, Su kansu masu chemist sunyi mamaki sukace watak'ila cikin yan matan dake gidan wata tayi cikin banza,

Har d'aki ta samu SHATU, tana zaune kan sallaya ta idar da sallar la'asar, "Yarinya ana baki shawara kina k'in karb'a, na fad'a miki zubar da cikin nan shine alkhairi gare ki". SHATU kallon Iya tayi tace "Wallahi bazan tab'a zubar da cikin dan' sunna ba". "Da kike ikararin dan' sunna ina da tabbacin uban sa zai karb'e shi". "Ko ba zai karb'e shi ba Allah zai zama gatan sa". "Yarinya ce ke har  yanzu shiyasa, ni bazan biyewa shashancin ki maza karb'a ki sha ya b'are kowa ya huta". Ta fad'a tana mik'a mata maganin, Kallon IYA tayi galala da mamaki, "Kin tsaya kallona ki karb'a yanzu nan kisha kafin na b'ata miki rai wallahi". "K'iyayyar da kikewa cikin nan tabbas ba akan Mu'azzam kad'ai ba ne". cewar Shatu tana kallon IYA, "Idan ba akan shi bane yo kan mene, ni dai na fad'a miki Mu'azzam da ahalin sa ba zasu tab'a karb'ar cikin nan ba wallahi gara tun wuri kiji magana". "Ko kina da hannu kan barina gidan Mu'azzam duba da maganganun da kikayi ranar wanda basu tab'a faruwa tsakanin dake ba, kuma kika yi su a daidai gab'ar da ya dace da shirina na barin gidan sa bayan baki san komai akan haka ba". IYA wasu yawun tsoro ta had'iya tace "Ke ni idan ba zaki zubar da cikin ba ke kika sani, wahala akan ki zata k'are". Tayi saurin mik'ewa ta fice, SHATU tabi bayanta da kallo abubuwa da dama na kai kawo zuciyarta.

******************************

Mu'azzam k'arfin hali da dauriya da uwa uba gudun kasuwancin sa yayi k'asa yasa yau ya fito kasuwa tare da k'ok'arin maida hankali amma duk wanda ya kalle sa zai fuskanci yana d'auke da damuwa, Ganin yanayin sa yayi ma su Kawu Kabiru dad'i suna fatan ya dawwama haka har abada, Mu'azzam in dai zai rufe idon sa video SHATU yake gani zuciyar sa na zafi, haka yake dannewa yana jawowa kansa wasu ayyuka.

Kawu Kabiru ya had'a baki da wasu mutane kan suzo wurin Mu'azzam suce suna so ya musu order kaya, inda zai samu ya damfari Mu'azzam kud'ade masu yawa, Wasu yan' zaman banza ya samu ya tsara musu komai, tare da basu tufafi sukayi shigar kamala.

********************************

"Dama mun ga yadda kake kawo kaya masu kyau ne a kasuwa ne shine muke so ka saka mana order zane na lace mai kyau kamar na container biyu wanda a wurin mu kad'ai za'a same shi". Cewar d'aya daga ciki wnada ya ma kansa lak'abi da Alhaji Iro, D'ayan ya karb'e da cewa "Kayan da zasu samu amsuwa kasuwa sosai, kowa ya gani ya yaba". Mu'azzam kai ya jinjina yace "Ba damuwa". "Amma kamar yaushe zamu same su?". Mu'azzam yace "Sati uku masu zuwa". "Toh sai munji ka". Suka mik'a masa hannu suka gaisa da mishi sallama, Mu'azzam ya koma kan aikin dake gabansa.

Kuyi manaji

OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now