HS 38

80 18 1
                                    


HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na talatin da takwas

Agogon dake d'aure wutsiyar hannun sa ya kalla, bakwai da mintuna, Kansa ya mayar kan kujera tare da lumshe ido, Kusan kowa a plaza ya watse ya bar sa, hakanan yake jin baya son komawa gidan, wanda a yanzu yake jin ya zamar masa tamkar filin jirgin sama saboda fad'in sa, Knocking k'ofar yaji ana yi ya basar baya son magana da kowa yanzu, Lamid'o kansa ya girgiza cikin takaici yace "Kaga dan' banzan yaro ba zai bud'e k'ofa ba, ina ganin wannan itace damar da zan samu ganawa dashi ba tare da wani ya ganni ba". Ya cigaba da knocking k'ofar,

Mu'azzam jin k'arar buga k'ofar ta soma damun sa tana hawa mishi kai, dan dole ya tashi ya bud'e, "Hala kana wani abun ne ina ta bugawa shiru",. Kai ya d'aga tare da cewa "Barka da dare". "Yawwa barka dan kam daren ya soma". Kujera yaja ya zauna, Mu'azzam ma kan tasa ya koma,

"Naji abunda ya faru sam bai mun dad'i ba wallahi amma haka Allah ya tsara sai dai muce Allah ya kyauta". Cewar Lamido fuska na nuna alamar damuwa, Mu'azzam yace "Amin" a dak'ile, "Yanzu da Alhaji baya raye ya kamata mu nuna HALACCI a matsayin mu na k'annen sa kada mu bari yaran sa su tagayyara, hakan yasa nayi shawarar baka yarinyar wurina RUMAISA ka aura, tana da hankali sosai na tabbata zaka ji dad'in zama da ita, kuma ko ba komai akwai zumunci mai k'arfi tsakanin ku". "Bana sha'awar aure". Ya fad'a kai tsaye, "Subhanallah ya kake magana haka Mu'azzam aure ai shine cikar kamalar mutum". Shiru yayi tamkar bai ji ba, dan zaka rantse ba dashi ake maganar ba yadda ya basar, Lamido ya numfasa yace "Shikenan, bazan tilasta maka ba duba da har yanzu kana cikin rad'ad'i na abunda ya faru, amma ka sake nazari mai kyau". Ya mik'e ya fita, Mu'azzam yabi bayan sa da kallo yana ayyanawa abubuwa da dama a ransa.

**************************

GABARI, COURT ROAD HADEJIA

Madaidaicin gida ne mai d'auke da d'akuna uku falo d'aya, sai kitchen, Gida ne na masu matsakaicin kud'i, Komai na daidai an saka a gida, kama daga gadaje kujeru da kayan kallo, Haka kitchen ma an zuba kayan amfani hadda gas cooker,

"Da kyau wannan gida yayi, yanzu zan shaida jikata ta tab'a auren mai kud'i". Cewar IYA tana bin falon da kallo, SHATU wacce ta shigo rik'e da k'aramin akwati d'aki ta shige ba tare da ta damu da sanin fasalin gidan ba, yanzu duniya da abunda ke cikinta ba damuwarta bace fatan ta kawai ta gama da duniya lafiya, Kwanciya tayi kan gado tare da jawo wayarta ta kira Umma, Tana hannun Farha tana game, ganin SHATU ce mai kira ta d'auka,

"Yaya shatu ina wuni?". "Lafiya lau autar umma". Dariya tayi tace "Nayi missing d'inki Allah". "Nima haka, ina teema". "Tana d'aki". "To ba Umma waya". Da gudu ta samu Umma a kitchen ta kai mata, Sosai sukayi hira da Umma irin wacce suka dad'e basu yi ba tun kafin auren ta da Mu'azzam, tayi ma Umma godiyar gidan da ta kama musu, Tace "Sai makaranta, ina ga ya kamata ki koma ki k'ara ilimi zai taimake ki". Ba zata iya k'ara yi ma Umma musu akan komai ba, duba da yadda akayi kan auren ta da Mu'azzam, hakan yasa tace "Toh Umma". "Zan saka a fara neman miki makaranta anan hadejia yafi zaman banza". "Toh Umma nagode". "kuma ki rik'awa kai wa su INNA ziyara". Tace "In Shaa Allah". Suka d'an k'ara hira kana ta kashe, Wayar da Umma sosai ya sanyaya zuciyarta tana jin wani kasu na damuwarta ya rage.

******************************

Mu'azzam ya mayar da shan energy drink al'adarsa a kwanakin nan, Shi ya zama abincin sa kuma ruwan shan sa, idan kaga yaci abinci ya shiga wurin Hajiya ne ta tursasa mishi sha, Gongoni power horse ne hannun sa d'aya yana sha, hannu d'aya kuma motoci yake dubawa wanda zasu zo daga cotonou, Kiran Hajiya ya shigo, Ya d'auka tare da saka speaker, "Ina wuni". "Lafiya lau, kazo ina son ganin ka yanzu". Tana fad'a ta kashe, Gongoni ya d'aga ya shanye, ya jefa wayar alijun gaban rigar sa, Ya d'auki mukullin mota ya fito, Fuskar sa sam babu annuri,

***************************

Hajiya Hafsatu da Sahura suna zaune falo suna tattauna yadda bikin zai tafi, dan gagarumin event suke son tsarawa wanda zai bi social media yayi trending a instagram, "Hajiya Dan Allah ayi irin decoration d'in nan". cewar Asiya tana nuna musu wani a waya, Sahura tayi dariya tace "Da kyau yar' gari, ki nemo mana suwa sukayi decoration d'in". Asiya tace "Toh". cike da zak'uwa,

Basu ji sallamar Mu'azzam ba har ya shigo falon duka hankalin su ya tafi kan tsare tsare yadda za'ayi biki, Zama yayi kam kujera shima ba tare da yace wa kowa komai ba, Hajiya d'ago kai da zatayi ta gan shi, "Mu'azzam yaushe ka shigo ba magana". "Ba jimawa". Ya fad'a, Asiya ta gaishe shi ta bar falon, "Saboda tsinanniyar yarinyar can ka daina far'a bayan kana da alots of chances na farin ciki, ko Alhaji dai ya bar duniya baka canza ba, sai akan wata mara imani da ba komai zuciyarta da uwarta sai son duniya". Mu'azzam shiru yayi kwata kwata baya son maganar,

Hajiya Hafsatu ta cigaba da cewa "Lokaci yayi da zaka fara sabuwar rayuwa mai cike da farin ciki da natsuwa, lokaci yayi da zaka manta da duk wani bak'in ciki, kai ma ka ajiye yara kamar kowa". Kallo Hajiya yayi jin furucinta na k'arshe, Kai ta jinjina masa tace "K'warai, na maka mata wacce zata kawo maka farin ciki rayuwarka kuma ta haifa ma yara". "Hajiya Dan Allah kada ki sani yin aure, bana sha'awar shi". "Akan mace d'aya sai ka rusa rayuwar ka, to ni na damu da rayuwarka idan kai baka damu ba, auren ka da Na'ima babu fashi, sati mai zuwa za'a fara biki, tun daga pre-wedding pics har zuwa kowane event da ake buk'atar ango ban d'auke maka ba". Da zallar mamaki ya kalli Hajiya Hafsatu yace "Idan ma za'a yi auren ina ga d'aurin aure ya wadatar duba da Alhaji bai dad'e da rasuwa ba". "Tanan ka b'ullo, to babu fashi akan abunda nace". Uwa uwa ce bai isa jayayya da ita ba amma babu mahalukin da ya isa saka shi aure yanzu, bayan ya rufe zuciyarsa daga soyayya, taya ma zai iya k'ara karb'ar waya ya' mace cikin rayuwar sa, Haka ya mik'e ya bar falon cikin tsananin b'acin rai, da mamakin yadda kowa ke son had'a shi da nashi, Har ta gefen abokan Alhajin mutum kusan uku suka kira shi suna mishi tayin yaran su, Cikin lokaci k'ank'aninna rabuwar sa da Shatu har labari yabi gari, "Shin maza ns sukayi k'aranci ake mishi tallar matan, ko kuwa?"  Yayi ma kansa tambayar tare da fad'awa dogon nazari.

Anty Sahura sai bayan fitar sa tayi magana tace "Hmm ba k'aramar illa Shatu da uwarta sukayi ma rayuwar Mu'azzam ki duba yadda ya koma, babu far'a sai zafin rai, ko auren ma baya sha'awar sake yi". "Ai sai dai nace Allah ya isa tsakanina dasu". "Shine kawai, bari na tafi gida". Ta fad'a da mik'ewa, Hajiya Hafsatu tace "To kiyi  magana da mai soverniers dan gara tun wuri a soma bugawa". Sahura tace "Sai na fara biyawa can ma tunda layin mu ne". "Yawwa dan babu lokaci". Sahura ta jinjina kai zuciyarta fal farin ciki.

****************************

"Ke Zulfa'u kina ina?". Cewar Kawu Kabiru yana shigowa gida, Zulfa'u dake d'aki tana karatun jarabwar da zasuyi gobe ta taso, "Baba sannu da zuwa". Ta fad'a da gurfanawa, "Kina can d'aki kwance shiyasa kullum bakya rabuwa da ciwo". "A'ah Baba karatu nake". Tsaki yayo yace "Kin sawa kanki jarabar boko kamar wacce ta taso gidan yan' boko". Zulfa'u tayi shiru tana sunkuyar da kai, "Gara ma ki takarta bokon ki ajiye aure zan miki". A razane ta kalle shi, "Kina kallona ko dan baki san wanda zaki auran ba ne, da da kanki zakiyi watsi da bokon". Yana fad'ar haka ya wuce d'akin sa, Zulfa'u hawaye ya wanke fuskar ta, babban burinta ta samu ilimi mai zurfi a ganinta dashi zata taimaki kanta da mahaifiyarta,

Kawu kabiru yana shiga d'aki babbar rigar sa ya cire, ya zauna bakin gado tare da cewa "Yaro kenan, Mu'azzam yaushe aka haifa, baka isa ja da ni KABIRU ba wallahi, duka burika sai sun cika baka isa yimun shamaki dasu ba, auren ka da Zulfa'u kuwa.... Yayi dariya tare da had'a yatsun sa biyu ya d'ana.

Uhmm inji mai ciwon baki😷

OUM MUHRIZ

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now