HS 15

87 19 2
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na sha biyar

K'arar wayar Hajiya ta farkar da ita nauyayyen baccin da take, Siririn tsaki tayi da cewa "Waye ke kirana da asubar fari", Ta jawo wayar gefen ta, Sunan Maimuna da ta gani yasata d'auka, "Hello Hajiya na sauka ba da jimawa", "Ina fatan namiji aka samu" Murya sanyaye tace "A'ah mace ce", "Toh Allah ya raya kuma dai jinin naku na haihuwar mata ne", Maimuna tace "Hajiya baki ga yadda babansu na nunawa damuwar sa", "Ba dai ke kika wa kanki ciki ba, shima ai hadda jinin sa a haihuwar mace", "Yace wai ke na gado da haihuwar mata shi gidansu maza sunfi yawa", "Mara mutunci dama tuni nasan bashi da kunya" Ta datse wayarta cikin takaici, Duka jikokin ta babu namiji, Mansura yaran ta biyar mata, Maimuna wannan itace ta uku, Shiru tayi tana nazari kana ta furta "Ya kamata na k'ara zage damtse wurin cikar burina", Ta sauka kan gadon zuwa band'aki alwala,

**********************************

Alhaji Hali Inuwa yau bai fito kasuwa da wuri, lokuta da dama idan kwanan Umma bai cika fitowar wuri ba saboda natsuwar da yake samu idan yana tare da ita, Mace ce mai tsananin hak'uri da sanin duk wata hanya na kwantar wa miji da hankali, mafi yawa matsalolin sa da ita yake sanarwa, tana bashi shawara wacce idan yayi amfani da ita yana ganin daidai, sab'anin Hajiya Hafsatu da sai da ta tunzara shi ga abunda ba shi ba, Ya sanar mata da zancen Mu'azzam wanda ya kasa barin zuciyar sa, Sosai ta nuna damuwarta wanda har tafi mahaifiyarsa nuna damuwa da lamarin, Haka ta fad'a masa kalamai wanda ya samu natsuwa, Da basa shawara kan su k'ara dagewa da addu'ar mak'iya,

Goma da mintuna ya shirya cikin shiga ta dattako, Hannun babbar rigar sa ta gyara masa da cewa "Allah ya bada sa'ar kasuwa yayi jagora", Murmushi yayi yace "Hajaru kenan wato dai har kullum tamkar yaro haka ake mun soyayya", Itama murmushi tayi tace "Ai soyayya bata tsufa", Yace "Hakane, sai na dawo", "Allah ya tsare hanya", Ya amsa da "Amin" ya fita fuska d'auke da annashuwa,

Yana bud'e murfin mazaunin baya na motar sa, Motar Kawu Kabiru ta shigo gidan, Alhaji kallon motar yayi da mamakin me ya kawo Kawu kabirun sanin duk abunda zai kawo sa har gida ba k'arami ba ne, maida k'ofar yayi ya rufe, Kawu Kabiru ya k'araso cikin giramamaa yace "Barka da safiya Alhaji", "Barka Kabiru", "Dama wurin ka nazo", "Lafiya kuwa", "Eh lafiya wallahi, maganar ce dai naga a gida ya dace muyi", "Toj mu shiga ciki", Yayi gaba Kabiru ya biyo sa baya.

******************************

"Dama zancen Bashar ne da Yusrah, sun kwana biyu suna soyayya, shine Bashar ya nuna sha'awar auren su nan kusa, nace bari na sanar da kai", Kawu Kabiru ya k'arasa da yar' dariya, "Haba Kabiru yanzu kai ba mai bada Yusra ga duk wanda kaso bane balle BASHAR, ai da Bashar da Yusrah duk abu d'aya ne, kana da iko kan Yusra", Kawu Kabiru cikin da jin dad'i yace "Hakane naga ya dace dai ne na sanar da kai a matsayin ka na babba", "Ni dai ba abunda zance sai Allah ya tabbtar mana da alkhairi, hakan ai an k'ara k'arfafa zumunci", Kawu Kabiru ya jinjina kai yace "K'warai da gaske", "Na sakar maka ragamar komai, duk hukuncin da zaka zartar kansu, kama daga saka ranar aure da sauran su", "Toh Alhaji Allah ya k'ara had'a kanmu", Ya amsa da "Amin", A tare suka fito kowanne ya shiga motar sa zuwa kasuwa,

******************************

"Baka da sauran fargaba kan auren Yusrah, nayi magana da Alhaji ya bada goyon bayan sa, tare da bani damar zartar da kowane hukunci" Kawu Kabiru ke sanar da Bashar wanda yana ganin zuwan sa ya same sa office dan jin yadda sukayi da Alhaji, Farin ciki zalla ya bayyana kan fuskar sa yace "Alhamdulillah", "Dan haka ka cire shakkun komai ka cigaba da zuwa wurin ta", Ya amsa da "Toh" Yana shafa sumar kansa, "Nagode Baba" Ya sake fad'a da zumar tashi, "Ba kai kad'ai auren naku zai amfana ba har ni, ka daina godiya" Kawu Kabiru ya fad'a, Bashar mamakin mahaifin nasa ya bashi yadda a kullum yake abu tamkar ba shi ya haife su ba, a ganin sa Uba ya kan yi iya k'ok'arin sa wurin samarwa yaransu farin ciki sab'anin Kawu kabiru wanda buk'atar sa itace gaba da kowa, ya tabbatar banda yana da wani buri ko kusa ba zai yi fighting kan ya samu Yusrah ba, duk wata hidimar su bata gaban shi, Kan shi kad'ai ya sani.

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now