*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*Vote me on Wattpad @Zarah_bb*
*BABI NA.....UKU.*
"Ka ga Jabeer bana son nanata magana, tun yaushe nake ce maka ka za6i d'aya daga cikin yaran nan? Amma kayi kunnan uwar shegu dani, toh bara ka ji bazan ta6a yarda ka aure y'ar talakan nan ba dangin tsiya duk ga mutanan arziki nan suna sonka amma kai ka wani nace sai wannan y'ar matsiyatan" Cewar Mummy.
Duniya idan da abinda Jabeer ya tsana bai wuce akira Jawaheer d'in shi da y'ar matsiyata ba, idanun shi sunyi ja sun canza launi cikin marainiyar murya ya ce
"Mummy ki sani da talaka da mai kud'i duk Allah ne ya halicce su kuma ba wanda yafi wani a wajen Allah sai wanda yafi jin tsoron shi. Mummy wallahi duk wad'annan da kike son na aura ba wanda ta ke da tarbiya, natsuwa, kunya da ilimin islama irin Jawaheer. Sa'annan kuma Mumy........" hannun da Mummy ta d'aga masa ne yasa shi dakatawa. A hasale ta fara fad'in"Jabeer ban kira ka don ka fad'a mani son ranka ba, kuma bance kayi mani wa'azi ba, amma ka sani idan har bazaka aure za6ina ba too fa kaima bazaka aure wannan y'ar matsiyatan ba idan har ina nufashi a doron k'asa sha-sha-sha kawai wanda baisan abinda ya dace da shi ba"
"Allah ya huce zuciyar ki Mummy ban fad'a dan na 6ata maki rai ba! Dan Allah kiyi hak'uri""Ka rik'e hak'urin ka bana so, tashi ka 6ace mani da gani"
Cikin sanyin jiki Jabiro ya fice daga falon zuciyar shi nayi masa k'ona sam ya tsane wannan halin na mahaifiyar sa.*_04:30pm._*
"Wallahi Mu'azzam sam Mummy tak'i ta fahimce ni kuma a gaskiya bana jin zan iya auren wata y'a mace idan ba Jawaheer ba" Jabeer ya fad'a fuskar sa cike da damuwa.
"Hak'uri zakayi Jabeer kasan iyaye sai da lalla6a, but why bazaka sanarwa da Dady ba k'ila koh zai iya yin wani abu akai!""Hmmmmm! Ai Dady bayada abun cewa because duk abinda Mummy tace shima shi zai ce kanwar duka ja ce"
"Too fah! Allah ya kyauta, ka cigaba da addu'a nima kuma zan tayaka duk abinda yafi zama alkhairi a gareku Allah ya za6a maku shi" Mu'azzam ya furta cike da tausayin abokin na sa.********
Zaune take a parlour idonta k'yam akan agogon dake manne ajikin bangon falon ganin 12:45am yasa hankalinta ya k'ara tashi duk da yana yin dare a waje amma baya wuce sha biyun dare but yanzu har k'arfe d'aya saura minti sha biyar bai dawo ba. Kai ka wo ta fara yi a tsakiyar falon tana tunanin mafita, aranta kuwa sai faman addu'a take yi Allah ya maido mata da mijinta gida lafiya. Jin an banko k'ofa da k'arfi ya saka ta dawowa daga duniyar da ta afka, da sauri ta doshe wajen da yake cike da maye ya fara cewa "Jaye mani daga nan tun ban 6a66allaki ba" yana fad'a yana tangad'i. Idan da sabo ta saba da wannan dan kuwa wani sa'in har dukanta yake yi. Duk da izarta da yake yi game da ashar d'in da yake d'ura mata baisa ta k'yale shi ba, a haka ta ja sa har bedroom anan k'asan carpet ya zube yana sambatun sa na mashaya har bacci ya d'auke sa.
Sosai Saleema ke damuwa da halin da mijinta yake ciki amma ba yadda ta iya akuda yaushe tana rok'on Allah da ya yaye masa wannan shaye-shayen da yake yi Allah ya shirya mata mijinta.
_Washe gari_
*_08:30am._*
Tsaf ya shirya cikin riga da wando na kaftani kalar sararin samaniya(Sky blue) hular shi da takalmin shi duk sunyi dai-dai da shigar sa sai k'amshi yake ta famar zubawa, sosai ya yi kyau ya fito cikakken mutum mai kamala idan ka gansa sam bazaka ce mashayin giya bane. A dinning area ya same ta zaune tana jiran fitowar sa, da murmushi kwance akan fuskar sa ya iso wajen da take zaune, kujerar dake kusa da ita ya ja ya zauna bata ce da shi uffan ba ta tashi tayi serving d'in shi har suka kammala breakfast d'in ba wanda ya ce da d'an uwansa ci kanka. Sam Saleem bai ji dad'in hakan ba yana matuk'ar son matarsa kuma tabbas yasan itama tana son sa kuma tana hak'uri da halayyar shi. Ta yunk'ura zata tashi sai ya kamo hannunta kicaniyar k'wace kanta ta soma yi amma kasancewar rik'on da ya yi mata bana wasa bane sai ta kasa k'wace wa dan dole ta hak'ura sai dai ta kauda kanta sam taki bari su had'a ido. Ganin da gaske fushi take yi da shi ya saka sa ya sunkuce ta sai d'akin sa dukda neman zillewar da take yi, bai direta ko ina ma sai kan gadon shi babu zato ba tsammani sai ganin ya yi ta saka masa kuka hankalin sa idan yayi dubu ya tashi kwata-kwata ya tsani ganin kukan ta da k'yar ya samu ya shawo kanta tare da yi mata alk'awarin bazai sake shan komai na maye ba kuma bazai koma yin dare a waje ba. Duk da tasan hakan da kamar wuya a wajen Saleem amma taji dad'i da ya nuna damuwarsa akanta, tsakanin miji da mata sai Allah tuni ta warware harda yi masa rakiya.
Wattpad @Zarah_bb
Ur votes nd comments count alot.
*©Zahra~B~B👌🏻.*
YOU ARE READING
ZAMANTAKEWA!.
Non-FictionSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...