*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*BABI NA TALATIN.*
Murmusawa Zuby tayi game da gyara zamanta kana ta furta
"Ya fi su abubuwa da dama"
"Kamar me da me kenan?" Samee ta tambaya.
"Kyau, kud'i, iya kula da tarairaya"
"Kina nufin su duk basu da wad'ad'annan abubuwan?"
"Suna da amma Abdul ya fi su"
"Amma kuma na ga ko Muby na kashe maki kud'i fa"
"Yes! Yana kashe man but bai kai Abdul ba."
"Wannan k....." Ringing d'in wayar Zuby ya saka Samee yin shiru.D'aga wayar Zuby tayi cikin walwala da farin ciki, ban ji me aka ce a d'ayan 6angaren ba, na dai ji ta ce "To gani nan fitowa yanzun nan."
"OK! Sai kin fito" Ya fad'a tare da katse kiran.
Dubanta Zuby ta maida ga Samee ta ce
"Abdul ya zo ni zan wuce"
"Da wuri haka Zuby?"
"Idan na sa mu dama may be na dawo idan kuma ban sa mu ba sai mun had'u kawai"
"To shikenan nagode" Samee ta fad'a had'e da mik'ewa tsaye.
"Bakomai k'awata"
Har wajen da Abdul yayi parking Samee ta raka Zuby, bayan Samee sun gaisa da Abdul tare da yi mata alkhairi tayi masu sallama ta koma cikin gida. Su kuwa suka tada mota suka wuce.******
"Shikenan yanzu Mama haka zamu sakawa Aunty Zubaida ido sai abin da ta ga dama za tayi?"
"To ya muka iya Maryam? Ai fa d'an da ya fi k'arfin ka wasa kake maida shi, kina gani ko nayi mata magana yanzu Babanku zai taso man da masifa kamar zai cinye ni"
"Hakane kam! Sam Baba baya kyautawa. Ni wallahi babu abin da ya fi k'ona man zuciya irin yadda take saka tufafi kamar wata arniya watarana idan Aunty tayi wata shiga fa idan tun farko baka santa ba wallahi za ka ce ba musulma ba ce" Ta idar da maganar da damuwa fal a fuskar ta.
"Duk abin da ki ke ji Maryam ina jin fiye da shi. Dan haka addu'ar nan da muke yi mata ita zamu cigaba da yi. Shi kuwa mahaifinku Allah ya ganar da shi gaskiya yasan cewa abin da yake d'aure mata ta nayi ba abu ne mai kyau ba."
"Allahummah Ameen Mamata"
Haka Maryam da Mama suka cigaba da tattauna matsalar dake damunsu.
******
"Abokina wai tunanin menene ka keyi ne haka?, wallahi ka rage yawan tunanin nan kada ya je ya haifar maka da wata matsala can daban"
"Wato Sadiq na ma rasa abin da zanyi yanzu, cikin k'arya da gaskiya na fahimce Mummy ko mutuwa zanyi bazata barni na aure Jawaheer ba, na rasa gane wace irin ak'ida ce da Mummy."
"Kada dai ka ce man ba ka je gidan Baba Al'ameen ba?"
"Tun ranar da ka bani wannan shawarar na je gidan na fad'a masa"
"To bai samu damar zuwa inda Mummy'n bane?"
"Ya je" Jabeer ya fad'a atak'aice.
"To ya akayi ne?"
Sai da Jabeer ya ni sa sa'annan ya zayyanewa Sadiq duk yadda Baba Al'ameen yayi da Mummy. Har zuwan Mummy gidan su Jawaheer sai da ya fad'a masa da kuma yadda suka yi da Baban Jawaheer d'in.
Duk'ar da kansa Sadiq yayi tare da dafesa da duka hannayensa, tunani yake yi Mummy wace irin mace ce da kafiya haka. Sosai ya tausayawa abokin sa domin wannan ba k'aramar jarabawa ba ce. Lallai hausawa sunyi gaskiya da suka ce SO BABBAR CUTA CE.
"Ka yi shiru ba ka ce komai ba" Jabeer ya ce da shi.
Wani nannauyar numfashi Sadiq ya suke sa'annan ya furta
"Wallahi Jabeer har ban san me zance da kai ba kuma, dan Mummy ta wuce duk tunani na."
Tsawon minti biyar ba wanda ya ce da d'an uwan shi uffan. Jabeer ne yayi k'arfin halin datse shirun da cewa
"Bakomai Sadiq ka cigaba da tayani addu'a insha Allah komai zai dai-daita"
"Allah ya k'addara hakan"
"Ameen ya rabbi" Cewar Jabeer.
******
"Jawaheer!" Ya kira sunanta cikin muryarsa mai dad'in sauraro.
"Na'am Yayana" Ta amsa cikin siririyar muryar ta.
"Bana gajiya da ba ki hak'uri akan abin da ya faru, dan Allah kiyi hak'uri ki manta da shi kamar bai faru ba, kuma dan Allah ki k'ara ba wa Innah hak'uri."
"Wallahi Yaya ba komai, kama manta da wannan zancen ya rigada ya wuce"
"Nagode sosai Allah yayi maki albarka"
"Ameen Yayana"
Gyara zamansa yayi tare da kafeta da manyan idanunsa ya ce
"Jawaheer a naki tsari wanne kika fi so tsakanin biyun nan?"
"Tsakanin me da me kenan?" Itama ta tambaye shi.
"Da muyi auren mu yanzu da mu bari sai kin kammala scondary school d'in ki nima kafin nan na rubuta final exam d'ita wanne kika fi so?"
Shiru tayi masa ba tare da ta ce da shi komai ba illah tafin hannuwanta da ta saka ta rufe idanunta.
"Me ye na rufe ido kuma?"
Nan ma ba amsa.
"To ai sai ki sauke hannunwan"Ba musu ta sauke tare da duk'ar da kanta k'asa tana wasa da y'an yatsunta.
Murmushi kawai Jabeer yayi a duniya kyawawan d'abi'unta na k'ara birgeshi da ita, dan kuwa kaf halayen Jawaheer sunyi masa shiyasa a kullun sonta k'aruwa yake yi a zuciyar sa. Tuni ya sallama ya kuma tabbatar da Jawaheer ta zama jinin jikinsa sam bazai iya rayuwa bada ita ba.
"Hmmmm! Halan Mummy ta amince da har kake zancen auren?" Maganar da ta maido shi daga zancen zucin da yake yi.
Murmushi yayi har sai da kumatunsa suka lutsa(Dimples/beauty point).
"Kar ki damu da yardar Allah wannan karon zamuyi nasara kuma insha Allahu Allah zai d'ora mu akanta." Jabeer ya k'arasa maganar idon shi k'yam akan Jawaheer.
Cikin sanyin jiki ta ce
"Allah ya za6a mana duk abin da ya fi zama alkhairi a rayuwar mu.""Ameen ya Allah." Jabeer ya amsa mata da shi.
*©Zahra~B~B👌🏻.*
YOU ARE READING
ZAMANTAKEWA!.
Non-FictionSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...