*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*
_Da yawa na nesa da kai/ke zai amfane ka/ki, na kusa da kai/ke zai cuce ka/ki. Kusancin zuciya shi keda amfani ba na gangar jiki ba._
*BABI NA ARBA'IN DA BIYAR.*
A kwana a tashi asarar mai rai, yau saura sati d'aya bikin Jabeer da Jawaheer. B'angaren su Jawaheer sai shiri suke yi ba ka ma hannun yaro haka abin yake a gefen su Aunty Halima da Baba Al-Ameen suma shiri suke yi sosai. Sam Mummy tak'i saka hannunta a hidimar kuma ta rufewa Dady baki dan kuwa komai ya kasa tsinanawa duk da yana jin zafin abin a ranshi amma ya rasa dalilin da yasa ya ke jin bazai iya yin komai ba a bikin. Baba Al-Ameen ya nunawa Dady 6acin ranshi game da ko ohon da ya yi da lamarin amma har Baba Al-Ameen ya gama zancen shi Dady bai ce da shi uffan ba, al-amarin da ya yi matuk'ar ba wa Baba Al-Ameen mamaki. A ranshi kuwa sai furta ya yi
"Allah ya fitar da kai daga sharrin wannan matar ta ka Yaya Sani. Dole mu dage da yi maka addu'a tun bata k'arasa ka ba"
Maida duban sa Baba Al-Ameen ya yi ga Dady ya ce
"Ni zan wuce"
"To! Allah ya kiyaye hanya" Dady ya furta can k'asan mak'oshi.
Mamaki ne ya k'ara kama shi ganin Dady ya yi magana yanzu.
"Meyasa tun d'azu ka kasa yi man magana sai yanzu da zan tafi?" Baba Al-Ameen ya tambaye Dady.
Nan ma shiru Dady ya yi masa shi kansa bazai iya cewa ga dalilin da yasa ya kasa magana ba, kawai abu d'aya ya sa ni game da al-amarin shi ne sam baya son ayi masa zancen bikin Jabeer.
Ganin haka ya saka Baba Al-Ameen ficewa ba tare da ya k'ara cewa komai ba.
******
"Haba! Lubna wai meyasa bakya jin magana ne? Na ce maki kiyi hak'uri, ai ba cewa akayi an fasa auren ba"
"Ni wallahi Hajiya bazan yarda da wannan zancen ba, idan bayan auren Mummy'n sa ta k'yale shi fa? Tunda kinsan ba sona yake yi ba."
"Ai ba za ta soma yin hakan ba, nima da banyi niyyar yarda ba amma tunawa da wani abu da nayi yasa na amince da zancen kema kuma ina son ki amince da hakan"
"Hajiya kin fi kowa sanin irin son da nakewa Jabeer, idan har kika bari na rasa shi a karo na biyu wallahi nima za ki iya rasani"
Furucin Lubna na k'arshe ya yi matuk'ar ta da hankalin Hajiya Ladi. Cike da jin tsoron abin da tilon y'arta ta fad'a murya na rawa ta ce
"Ba ma za ki rasa shi ba Lubna Insha Allahu Jabeer na ki ne in kuwa duk abin da na mallaka zai k'are sai na tabbatar da kin aure shi" Har ga Allah tana matuk'ar k'aunar Lubna ita kad'ai Allah ya bata dan haka bata son duk abin da zai rabata da ita.
Sanin halin mahaifiyar ta yasa ta yarda da zancen.
Jin Lubna tayi shiru bata ce komai ba yasa Hajiya Ladi tunanin ko bata amince da auren Jabeer a matsayin matar sa ta biyu ba. Cike da fargabar abin da Lubna za ta fad'a Hajiya Ladi ta furta
"Ba ki ce komai ba Lubna"
A jiyar zuciya Lubna tayi kafin ta ce
"To Hajiya na yarda amma ina fatar ba za'a d'auki lokaci ba"
"Eh, ba za'a d'auka ba" Hajiya Ladi ta fad'a cike da farin ciki game da gogewa Lubna hawayen da ke kwance a saman fuskarta.
Haka dai ta cigaba da lallashin Lubna tare da kwantar mata da hankali.
******
"Baby wallahi nayi missing d'inki over"
"Bawani baka yi missing d'ina ba tunda har kake iya tafiya wata k'asa ka barni" Zuby ta fad'a cike da shagwa6a.
"Noo baby bahaka bane kema kin san dan tare da Dady mu ka je ne, da dake zan tafi but am very sorry kin ji" Abdul ya ce da ita tare da janyo ta jikin shi.
Lamo tayi ta cigaba da yi masa kukan shagwa6a.
"Ohhh! Dear ki daina mana kin san bana son kukan nan na ki"
Banza tayi masa. Da k'yar Abdul ya samu shawo kan Zuby ta hak'ura daga nan kuma suka afka wata duniyar.
Wa'iyazu-billah! Allah ka karemu daga yin *zina* Allah ka nisanta mu daga gareta Allah ka kare mana farjinmu. Allah ka yi mana katangar k'arfe daga duk abin da zai saka mu yin da na sani a rayuwar mu. Allah ka k'ara mana wadatar zuciya! Allahummah Ameen.
Please don't forget to vote and comment on Wattpad @Zarah_bb
Ur vote nd comment count alot.
Muje zuwa............
*©Zahra~B~B👌🏻.*
YOU ARE READING
ZAMANTAKEWA!.
Non-FictionSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...