BABI NA.....D'AYA.

5.8K 278 28
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*


*Na Xarah~B~B.*


  *{NWA}.*

  www.zahrabb.blogspot.com


  *26-07-2017.*



     *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM!!.*

     _Ina mai k'ara godewa Allah daya bani ikon sake rubuta wani littafe, yadda na farasa lafiya ina rok'on Allah yasa na gama shi lafiya alfarmar Annabi (SAW)._

*Ban yarda wani ko wata su juya mani labari ba ko su cire wani abu ko su k'ara ba dan haka a kiyaye.*

   *Wannan labarin banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba idan ya yi dai-dai da ke ko kai akasine aka samu.*

    _Godiya gareku masoyana na nesa dana kusa maza da mata nagode sosai da kulawar ku agareni Allahu ya bar k'auna tsakanin mu. #one love._

*Na gaishe ku k'ungiya mai albarka NAGARTA WRITERS ASSOCIATION Allah ya k'ara had'a kanmu alfarmar Annabi (SAW).*

_Ku na daban ne a rayuwata matsayin ku gareni ya wuce duk tunanin mai tunani Allah ya bar so da k'auna tsakanin mu my luvly nd proudly *RAZ.*_

*LITTAFAI  MASU FITOWA INSHA ALLAH:-*

*-DAGA TAIMAKO!.*
*-KAYAN ARO!.*
*-WA ZAN AURA???!.*



*BABI NA.....D'AYA.*

   *Gidan Saleem da Saleema.*

    "Haba Saleem wallahi kaji tsoron Allah, ka tuna fa koh yaushe zaka iya mutuwa, shin idan ka mutu da wannan halin me zaka kare kanka da shi a wajen mahaliccin ka?, shin baka tunanin haihuwa zakayi, koh son kake ka barwa yaranka abun fad'a bayan ba kai?"
   "Shin wai ke mai yasa bakida uzuri da hak'uri ne, kyace duk abunda mutum yayi sai kinyi k'orafi akai" wanda naji an kira da Saleem ya fad'a fuskar shi ba walwala.

"Dole ka ce banida hak'uri tunda ina fad'a maka gaskiya" ta fad'a cike da tsiwa.
   "Dukda banida isashshen ilimi amma nasan cewa haramun ne mace ta d'aga muryar ta akan ta mijinta, shin ta haka ne kike tunanin in daina abunda nake? Shin haka ake lurar da mutum idan ya kauce? Karfa ki manta ke matata ce"
  Tsayuwarta ta gyara game da sassauta murya tace
   "Laifin ka ne Saleem sam baka kyautawa, dan Allah kazo mu fahimce junan mu ko ma gyara *zamantakewar mu*, mu kenan kullun cikin fad'a"
  "To kiyi hak'uri zan daina"

"Hmmmm!..... Allah yasa, dan kullun haka ka ke fad'a amma kak'i ka canza"

Ganin idan yaci gaba da zama a gidan abun ba karewa zaiyi ba ya saka shi barin gidan.
******

  "Jawaheer meyasa har yanxu kin kasa amincewa dani a matsayin masoyinki kuma wanda ke son auren ki? Koh baki yarda da irin son da nake yi maki bane?"

"Uhm... Bahaka bane Yaya Jabeer, na yarda kana sona kuma nima ina sonka amma kasan kafi k'arfina shiyasa kaga kamar ban amince dakai ba, bana son nayi abunda zai sa in jawa iyayena wulak'anci"
    "Hmmmm.... Meyasa bazaki yarda da abunda nake fad'a maki bane, ni banfi k'arfin ki ba, a duniya ba wanda yafi wani sai wanda yafi tsoron Allah. Sam bana jin dad'in hakan da kike yi, why a koda yaushe kike irin wannan tunanin ne?"

"Toh na daina, amma kana ganin iyayenka zasu yarda ka aure ni? A matsayina ba y'ar kowa ba bamuda komai sai wadatar zuciya!"
   Fuska ya d'aure ya ce
"Tunda bazaki daina wannan zancen ba kici gaba da yi"

Ganin kamar ranshi ya 6aci yasa ta maida dubanta gare shi, har ga Allah tana son Jabeer amma matsalar d'aya ce mahaifan sa sam basa son talaka especially Mummy'n shi dan har ta fi Dady'n sa zafi da k'yamar talaka, sanin kanta ne zaiyi wahala iyayen shi su yarda da wannan auren.
   "Kayi hak'uri bazan sake ba insha Allah" Ta furta can k'asan muk'ushinta.

"Yauwa Jawaheer d'ita Allah ya bar mani ke, kawai ki cigaba da tayamu da addu'a kinji koh?"

Kai kawai ta gyad'a masa alamar "eh ta ji".

******

  *Gidan su Zubaida(Zuby).*

"Tayi maki kyau zauna nan har sai k'annan ki sunyi aure kina Kallo saboda tsabagen ruwan ido da kwad'ayin abun duniya, wallahi ina guje maku ranar da zakuyi dana sanin abunda kuke yi dake har mahaifin ki"

Cikin rashin damuwa da nuna ku oho da zancen mahaifiyar ta tace
  "Kiyi hak'uri mama, bafa yadda kike nufi ne abun yake ba, kuma menene laifin Baba anan?"

"Hmmmm.... Yo ina zakiga laifin sa tunda ya daure maki kina yadda kike so? Toh wallahi bara kiji wannan abun ba so bane sam gwanda tun wuri ku farga kafin lokaci ya k'ure maku" mama ta fad'a game da mik'ewa ta nufi d'akin ta, sosai ranta ke k'ona game da halin mijinta da d'iyar ta"

Zaune take anan inda mama ta barta ko motsawa batayi ba, baba ne ya shigo da sallamar sa hannun shi rik'e da bakar leda. Ganin y'ar tashi zaune ita kadai a falo ya sanya shi cewa
   "Lafiya na ganki zaune ke ka d'ai, ina mamar taki?"

Cike da shagwa6a ta fara fad'in
  "Ba mama bace ta rink'a yi mani fad'an wai na tara samari ina cin kud'in su"

"Kiyi hak'uri ki kyale ta kinji y'ar baba, ai farin jini ne ya kawo hakan" Baba ya fad'a cikin sigar lallashi.

Murmushi tayi tare da cewa
   "Yauwa babana Allah ya bar mani kai"

"Ameen Ameen y'ar babanta".

*******

Zaune suke akan tabarmar dake shinfid'e a tsakar gidan. Cike da natsuwa suke magana, sosai suke mamakin hali irin na mak'wabcin su, gashi dai Allah ya azzurta shi da dukiya amma sam baya son talaka. Suna wannan zancen ne sai ga Jabeer ya shigo gidan da sallama k'unshe a bakin shi, cike da jin kunya ya gaida su yana sosa k'eya. Murmushi Innah tayi tare da cewa
   "Zauna mana Jabeeru kayi tsaye kamar wani bak'o"

"A'a Innah wucewa zanyi dama cewa nayi bara na gaishe ku"
  "Toh Jabeeru mungode sosai Allah ya yi albarka" Malam ya fad'a fuskarsa a sake.
   Sallama yayi masu kana ya fice.

"Kinga yaro mai hankali da natsuwa sam bazaka ce Alhaji Sani da Hajiya Zainabu ne mahaifan shi ba"

"Haka Allah ke lamarin shi, sai kaga ya fidda rayayye cikin matacce ko ya fidda matacce cikin rayayye" inji Innah.

"Toh Allah ya sa muda ce ya kuma yi mana kyakkyawan k'arshe" Malam ya furta idon shi k'yam akan matar shi.

"Ameen Ameen Malam".



  Toh ya ku ka ji first chapter???

    Waiting for ur comments.
 



*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang