BABI NA GOMA SHA BAKWAI.

724 61 2
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*





*Na Xarah~B~B.*




*{NWA}.*



www.zahrabb.blogspot.com


  *Vote me on Wattpad @Zarah_bb*

_Ba ka/ki sanin dad'in lafiya sai idan ciwo ya same ka/ki. Ba za ka/ki san dad'in zaman lafiya ba sai ka/ke gamu da tashin hankali. Ana sanin dad'in had'uwa ne idan rabuwa ta zo._



   *BABI NA GOMA SHA BAKWAI.*



   Kai tsaye(Direct) makaranta ya wuce kasancewar yana da lecture da safe. Ya jima da shiga lecture hall sannan Malamin da zaiyi masu karatu ya shigo, har lecturer ya gama karatunsa ya fita Jabeer bai gane komai ba dan kwata-kwata hankalin shi baya wajen. Abokin sa da tun shigowar Jabeer ya fahimce yana cikin damuwa ya matso daf da shi tare da dafa kafad'ar shi ya ce 

"Jabeer lafiya kuwa naga kamar kana cikin damuwa?"
   Shiru yayi baice masa komai ba. Dan Jabeer bai cika son fad'awa kowa damuwar shi ba especially personal issue d'in shi amma ya zaman masa dole yanzu ya fad'a ko ya samu mafita. Sai da ya sake maimaita tambayar shi sa'annan Jabeer ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, duban sa ya maida gareshi kana ya furta

"Bansan meyasa ta tsane talaka ba Sadiq, Allah ya sa ni ina iya k'ok'arina dan ganin na bi umurninta a kullun burina bai wuce in faranta mata ba, amma alfarma d'aya ta kasa yi mani ita. Bani shawara Sadiq me ya kamata nayi? Wallahi kaina ya tushe"

   "Wa kake magana akai ne Jabeer?"

"Mummy ce Sadiq, Mummy ce" Ya fad'a kamar zaiyi kuka.
   Shiru Sadiq yayi tabbas yasan halin abokin na sa da zurfin ciki, tun da yau har ya furta masa damuwar sa to tabbas al'amarin babbane.

"Ka natsu Jabeer ka fad'a mani wace alfarma ce Mummy ta kasa yi maka"
   "Akan Jawaheer ne, Mummy bata son na aure Jawaheer badan komai ba sai dan suna talaka, menene aibun talaka Sadiq? Ina ce su ma ba su suka yi kansu ahaka ba, To meyasa za'a tsane su?"

"Hak'uri zaka yi Jabeer, tabbas maganar ka gaskiya ce sam bai kamata a k'i ko a tsane talaka ba idan har mutum bazai iya taimaka masu ba a matsayin su na wad'anda basu da shi to bai kamata a d'ora masu karan tsana ba. Amma ita rayuwa da ka gani kowa da yadda Allah ya halicce shi dan haka kayi hak'uri ita Mummy nata tsarin kenan. Idan da dama ka hak'ura ka bi umurnin mahaifiyar ka ko ka fad'awa wani wanda kasan zata ji maganar shi ko Allah zai sa adace"

   "Zancen na hak'ura da Jawaheer baima ta so ba dan itace rayuwata bana tunanin zan iya cigaba da rayuwa bada ita ba ina ji a jikina suna gaf da rasani idan har suka dage akan sai na rabu da ita"

"Tir k'ashi" Sadiq ya fad'a yana jinjina kansa.

   Tsawon minti biyu ba wanda ya k'ara cewa uffan kowanan su da abin da yake tunani a ranshi, sai can daga bisani Sadiq ya ce

"Ka same Dady da maganar ko zai yarda"
    "Ra'ayin su d'aya da Mummy in yanzu Mummy ta ce ta yarda da auren to ko Dady zai yarda shi duk abin da take so shi yake so"

"Kuma ba wani wanda take jin kunyar shi? Ma'ana wanda ke iya sakata yin abu ko bata so"

   "Bana tunanin akwai shi Sadiq. Mummy ta daban ce duk yadda zanyi maka bayani bai zan lallai ka fahimta ba"

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Abin da Sadiq ya fad'a a zuciyar sa a fili kuwa cewa yayi "To yanzu me kake tunanin ya kamata kayi?"

   "Ban sa ni ba Sadiq, kawai kai ka fad'i yadda ka ga ya kamata ayi kawai"

"To ka je ka same k'anin baban nan naka ta na ta6a raka ka gidan shi, sai ka fad'a masa k'ila bazai rasa abun yi ba ko me ka gani"
   "Hakan ma yayi, insha Allah anjima zan tafi"

"OK! Allah yasa adace"
    "Ameen Ameen Sadiq nagode sosai Allah ya bar zumunci"

Jin bazai iya cigaba da zama makarantar ba yasa yayi sallama da Sadiq ya fice.

******

A 6angaren su Mummy kuwa bayan sun ta shi suka shirya suka nufi (Dinning area) wajen cin abinci. Zama tayi ita da Juwairiyya suna jiran fitowa Dady da Jabeer dan suyi breakfast, ba su jima da zama ba sai ga Dady ya fito. Serving d'in su Mummy ta shiga yi har Jabeer sai da ta zubama a tunanin ta yana hanyar fitowa. Ganin har ta gama serving d'in abincin bai fito ba yasa ta kalli Juwairiyya ta ce

   "Je ki d'akin Son ki ce yayi sauri ya fito breakfast d'in sa na jiran shi"

"To" kawai ta amsa mata da shi game da ta shi ta nufi side d'in shi.

   K'wank'wasa k'ofar ta fara yi jin anyi shiru yasa ta tura k'ofar da sallama a bakinta, ganin baya cikin d'akin ya bata damar isa wajen da b'an d'aki yake, murya can k'asa ta ce "Yaya Mummy na kiran ka" jin baiyi alamun yana ban d'akin ba yasa tayi tunanin ko bai ji ta bane, matsawa tayi daf da k'ofar ta k'arayin magana nan ma shiru. Kunnanta ta kara ko zata ji motsin ruwa jin bata ji komai ba yasa ta tura k'ofar a hankali wayam ta gani ba kowa a ciki. Cike da mamaki ta koma dan sanar da Mummy, har lokacin basu fara cin abincin ba suna jiran sai sun zo. Ganin ta ita kad'ai yasa Mummy cewa

"Ina yake ne?"
    "Mummy ba kowa a d'akin har toilet na duba"

"What??" Mummy ta fad'a game da mik'ewa tsaye.
    "Kin ga zauna bara mu kira shi mu ji ina ya tafi" Dady ya furta cikin sanyin murya.

Zama tayi ba tare da ta ce masa komai ba.

   Wayar sa Dady ya d'auka dake ajiye akan dinning table, number Jabeer yayi dialing. Ringing biyu ya d'auka murya can k'asa yayiwa Dady sallama, amsa sallamar Dady yayi had'e da tambayar shi inda yaje bai tsaya yayi breakfast ba.

"Dady makaranta na je inada darasin safe"
    "Amma Son shine zaka fita ba sanarwa?"

"Ayi hak'uri Dady"
    "OK! bakomai Son sai ka dawo Allah ya taimaka"

"Ameen ya rabbi. Dadyna nagode"
    Murmushi kawai Dady yayi had'e da tsinke wayar.

Sai yanzu hankalin Mummy ya kwanta kasancewar ta ji duk yadda suka yi da Jabeer...






*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora