*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*Vote me on Wattpad @Zarah_bb*
*BABI NA.....HUD'U.*
"Dan Allah Hajiya tunda yaron nan har ya na ce akan wannan yarinyar yake so ki barshi ya aureta mana!"
"Daman wannan maganar ce ta saka ka kirana?"
"Eh! Itace" Cewar Dady."Toh bazan ta6a yarda tilon d'ana ya aure y'ar matsiyata ba, kuma bana son ka k'ara yi mani wannan zancen" Mummy ta fad'a cike da gadara kamar ba shine mijinta ba.
Cike da 6acin rai Dady ya mik'e tare da nunata da d'an ya tsa ya ce
"Ni za ki fad'ama wannan maganar Zainabu? Lallai kin gama raina ni amma zanyi maganin ki tunda ke sam baki san darajar mijin ki ba, kuma aure tsakanin Jabeer da Jawaheer ki rubuta ki ajiye kamar anyi an gama in shaa Allah" Yana gama fad'ar haka ya wuce fuuuuuuuuu ya bar gidan.
Ikon Allah da mamakin ya hana Mummy iya furta komai dan bazata iya tuna yaushe rabon da Alhaji ya kira sunanta bare har ya nunata da d'an yatsa har ta manta amma yau gashi ya fad'a kansa a tsaye, sake da baki tabi k'ofar da Dady ya fita da kallo. A ranta kuwa sai cewa tayi"Lallai sai na k'ara tasarma Alhaji tsaye watau har ya yi bakin da zai yi mani musu. Wani shu'umin murmushi tayi game da furta gobe zan tafi wajen boka cika aiki dan sam bazata sa6u ba bindiga a ruwa" k'wafa tayi kana ta nufi hanyar da zata sadata da side d'in ta.
Sam ranar Mummy ta kasa sukuni sai tunani take yi ganin bazata iya hak'ura har gobe taje gidan boka cika aiki ba yasa ta janyo wayarta game da latsa numbar Hajiya Ladi, ringing d'aya ta daga tare da yiwa k'awarta kirarin da tasan tana matuk'ar son ayi mata, duk da 6acin ran da Mummy ke ciki amma sai da tayi murmushi sa'annan ta d'ora da cewa "Hajiya kina ina?"
"Gani a gida" Hajiya Ladi ta bata amsa.
"OK ki sameni yanzu a gida please"
"Toh gani nan zuwa hope dai lafiya?""Ina fa lafiya Alhaji na son 6ata mana tsari"
"What??" Hajiya Ladi ta furta tana zaro idanu kamar wadda taga wani abin tsoro."Hmmmm! Ke dai bari Hajiya! Yau Alhaji harda nuna ni ya fad'aman magana"
"Ki ce munyi sake d'an zaki ya girma""Bari kawai Hajiya sai dai kin shigo kiyi sauri dan yau d'innan nake son muje wajen boka cika aiki dan ina ganin wancan maganin ya sake sa"
"Gani nan zuwa yanzun nan""OK sai kin zo" Mummy ta furta had'e da katse kiran.
A 6angaren Dady kuwa tun a ranar ya so ya yiwa Jabeer zancen tare da k'ara basa k'warin gwiwa amma kasancewar aiki ya yi masa yawa bai samu damar zama da Jabeer ba.
*_05:05pm._*
Hajiya Ladi ta iso gidan Mummy cikin shigarta ta alfarma. Bayan sun gaisa basu tsaya 6ata lokaci ba Mummy ta ja mota suka nufi hanyar da zata kaisu dajin da boka cika aiki yake.
Bayan sun isa wajen suka jira ya sallame wad'anda suka sama a gurin. Suna shiga boka cika aiki ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya mai ban tsoro ya jima yana yi sai kuma ya sha kunu kamar ba shine ya yi dariyar ba.
Zamanta Mummy ta gyara game da maida dubanta ga boka kana ta ce "B......!"
Cikin muryar sa marar dad'in sauraro ya katseta da fad'in
"Nasan abinda ke tafe da ke Hajiya, nan ta ke kuwa ya zayyana mata dalilin zuwanta wajen shi. Shiru ya yi na wasu y'an sakanni kafin ya sake bushewa da dariya kwaryar da ke hannunsa ya d'aga sama tare da yin wasu magagganu da sam na kasa fahimtar abinda yake fad'a". Jim kad'an ya sauke sai ga wasu k'ullunan magani ya bata nan ta ke ya fad'a mata yadda zatayi amfani da su. Godiya tayi masa game da zube ma shi mak'udan kud'i sa'annan suka fice.
A hanya suka cigaba da sak'e sak'en su, sai da ta fara sauke Hajiya Ladi kafin ta wuce gida cike da nishad'i.
Don't forget to vote and comment.
*©Zahra~B~B👌🏻.*
ESTÁS LEYENDO
ZAMANTAKEWA!.
No FicciónSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...