*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*
*BABI NA HAMSIN DA BIYU.*
Kwance take akan cinyar shi yana wasa da gashin kanta.
"A koda yaushe ina k'ara godewa Allah da ya mallaka man ke a matsayin matata kuma uwar y'ayana ina alfahari da ke uwar gidana kuma amarya ta."
Sosai ta ji dad'in kalaman mijinta, ita kanta tasan ta yi sa'ar miji dan kuwa duk wani abu da ake nema ga d'a namiji Jabeer ya na da shi. Murmusawa tayi tare da gyara kwanciyarta sa'annan ta furta
"Nima ina alfahari da kai mijina"
Haka suka cigaba da bayyanar da ainahin k'aunar da suke yiwa junan su.
******
"Haba! Mummy yanzu anyi man adalci kenan? A ce kamar ni ayi bikin Yaya Jabeer ba na nan" Juwairiyya ta fad'a cikin muryar kuka.
"Kiyi hak'uri y'ata bikin ne yazo ba shiri kuma ni kaina ba na son auren kawai dan anfi k'arfi na ne. Ni da mahaifinki ba wanda ya je bikin dan duk ba ma so"
Ido Juwariyya ta zare ta ce "Meyasa Mummy? Yaushe kika daina son Aunty Lubna ne?"
"Hmmmmm! Ba ita Son ya aura ba, da itace kema sanin kanki ne sai na d'auko ki d'aga makaranta"
"Kar dai ki ce man Jawaheer ya aura"
"Itace Juwairiyya" Mummy ta ce da ita ranta nayi mata k'una dan ko sunan ta bata son ta ji an kira."
"Garin ya ya haka ta faru Mummy?"
Bata 6oye mata komai ba ta sanar da ita duk abin da ya wakana.
"Amma wannan Kawu Adamun ya cucemu wallahi"
"Banni da shi idan yasan wata ai baisan wata ba dan wallahi sai Son ya auri Lubna ko yana so ko baya so"
"Wallahi kuwa Mummy hakan ya yi."
"To a wace unguwa suke ne in je in mata rashin mutunci"
"Ohon ma su"
"Kar dai ki ce ba ki sani ba Mummy?"
"Ta ya zan sani bayan banje gidan ba. Ke fa komai na bikin nan Al-ameen ne da Halima suka yi shi, ko gidan ma na ji ance shegen Al-ameen d'in nan ya siya masa"
"Ki ce goyon baya ya samu da yawa"
"Sosai ma kuwa dan rabona da Son tun Washegarin auren sa da yazo na kuresa game da yi masa gargad'in kar ya sake taku k'afar sa gidannan."
"Haba! Mummy meyasa za ki kore sa?"
"Saboda yak'i bin umurnina, ni kuwa ban haifi d'an da ya isa ya sa6a umurnina ba"
"A'a Mummy kiyi hak'uri dan Allah"
"Bazan yi ba" Ta fad'a cikin d'aga murya.
Ganin haka yasa Juwairiyya ta ja bakinta ta yi shiru.
*_3 days later!._*Bayan kwana uku!.
Zaune take tana kallon Hausa film sallamar da akayi ne ya saka ta maida dubanta ga k'ofar falon dan ganin waye.
ESTÁS LEYENDO
ZAMANTAKEWA!.
No FicciónSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...