BABI NA.....GOMA.

763 69 4
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*








*Na Xarah~B~B.*




*{NWA}.*



www.zahrabb.blogspot.com


  *Vote me on Wattpad @Zarah_bb*


_Aboki guda d'aya ne zai taya ka kwanciyar k'abari, shine aikinka. Aikata alkhairi don ka samu aboki na k'warai a wannan kogo da ba shi da makawa._



     *BABI NA.....GOMA.*


    Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, ba laifi Jabeer ya girma ya yi wayau sosai ya na samun kulawa wajen Mumyn shi da Dadyn shi. Yana da shekara uku aka saka sa makaranta. Sannu sannu yaro yana k'ara wayau kyawon shi na k'ara fitowa.

   BAYAN SATI D'AYA!.

  Du ka iyalan Malam Muhammadu suna a harabar gidan driver na saka masu kaya cikin boot. Al'ameen ne ya kalle mahaifan na sa fuskar sa cike da annuri ya ce

   "Ummah! Abba! Allah ya kare mana ku Allah ya kaiku lafiya ya maido mana da ku lafiya"

Cike da jin dad'in addu'ar d'an na su su ka amsa da "Allahumma Ameen"
Hafsat da ke manne a jikin Ummah ta ce

  "Shikenan bazaku je dani ba Ummah?"

Hannunta Ummah ta d'ora akan bayan Hafsat tana bubbugawa ta furta

   "Kiyi hak'uri autana kinga sabon cike ne dake bai kamata kiyi tafiya mai tsawo haka ba amma ki bari idan kin haihu sai ki tafi"

"Ni gaskiya Ummah ji na ke kamar ku fasa tafiyar nan"

   "Meyasa Hafsatuna?"

"Bakomai amma haka kawai na ji bana son ku tafi"

   Abba dake sauraron firar su tun d'azu ya yi murmushi kana ya furta "Kar ki damu Hafsatu In shaa Allahu lafiya k'alau zamu ta fi kuma lafiya k'alau zamu dawo kin ji ko?"

"To Abba" Abin da ta fad'a kenan.

Tsaf driver ya kammala saka kayan tare da shaida masu ya gama.
   "Yauwa Isah sannun ka"

Murmushi kawai Isah ya yi.

   Sallama su ka k'ara yiwa junan su tare da neman yafiyar juna. Har sun shiga mota Isah driver yana neman ta da motar sai ga Sani kamar wanda aka jefo, ganinsa yasa bai tada motar ba. Bayan ya gaisa da k'annan sa ya nufi inda iyayen sa suke gaishe su ya yi kana ya d'ora da fad'in

"Abba ina za ku tafi ne haka?"

Ba Ummah ka d'ai ba har Abba ya yi mamakin ganin Sani agidan amma ko bakomai sun ji dad'in ganin sa bama kamar Ummah ba dan haka kawai take tausayin d'an na ta dangane da rayuwar da ya samu kansa a ciki. Sai da Sani ya k'ara maimaita tambayar da ya yi sannan Abba ya ce 

   "Sokoto zamu tafi" Ya ba shi amsa a tak'aice.

"To Allah ya kiyaye hanya sai kun dawo"

   "Ameen ya rabbi" Suka amsa a tare.

Ummah kasa d'auke kanta ta yi daga dubin yaran na ta da suka zo daf da k'ofar da take suka jera, haka kawai ta rink'a jin wani bak'on lamari mai wuyar fassarawa. Sun d'an jima a haka kafin Abba ya juyo daga front seat d'in da ya ke(kujerar mai zaman banza) tare da fad'in

"To ku kula Ameenu mu zamu wuce Allah ya yi maku albarka"

   Du kan su suka amsa da "Ameen"

Motar Isah ya ta da, tuni mai gadi ya wangale masu gate, haka suka rink'a d'agawa iyayen su hannu har suka fice daga gidan.

*****

  Alhamdulillah! Sun isa Sokoto lafiya, y'an uwa da abokanin arziki sai toruruwa ake zuwa gaishe su, haka suma sun zagaya wajen wasu y'an uwan. Sosai ya yi masu alkhairi dan kuwa duk ya bi su da kyautuka sai addu'a da fatan alkhairi suke yi masa.

B'angaren yaran su kuwa kusan kullun sai sunyi waya da su ba ma kamar Hafsat da zasu yini suna waya da Ummah. Sani kuwa abin nasa ya motsa dan tun zuwan su sau d'aya suka yi waya da shi. Kwanan su hud'u a Sokoto suka yi sallama da mutane suka kama hanyar dawowa Kano wannan karon duk suna gidan baya zaune, sai tattalin juna suke abun gwanin sha'awa ga su sun manyanta amma hakan baisa suka daina bawa junan su kulawa ba.

  *****

   Zaune yake a kujerar da ke d'akin sa ya zabga uban tagumi shi sam ya rasa abunda ke damunsa, idan ya tuna wasu abubuwan shi kansa yasan baya kyautawa amma ya ka sa gane dalilin sa nayin hakan. Yana tsaka da wannan tunani ta turo k'ofar d'akin ta shigo cike da rausaya, ta ci ado tayi kyau ainun sanye take cikin dogowar riga ta shadda ta sha aikin na'ura har ta ga ji sai k'amshin turare take zubawa. Har ta iso kusa da shi ta zauna amma baisan da wanzuwarta ba kasancewar ya yi ni sa cikin tunani. Kafad'ar sa ta dafa, firgigit ya zabura ganin ita ce ya saka shi sakin murmushi mai k'ara fito masa da ainihin kyansa. Ido ta marmad'a game da fad'in

"Lafiya kuwa kake Dady'n Jabeer? Me kake tunani haka wanda har na shigo baka sa ni ba?"

Shiru ya yi bai amsa ta ba, sai can ya ni sa ya ce...






*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Where stories live. Discover now