*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*
_Wannan gaisuwar takuce Hauwa M Jabo(My Jabo), Futuhatul khair, Hauwa Nayaya, Billy Tabaco, Bahijjah Beebalo, Jamila, Aunty Jidda, Hauwa Demary. #one luv._
*BABI NA ASHIRIN DA BIYAR.*
Tafiya suke cikin natsuwa. Rashida na k'ara kwantarwa Jawaheer da hankali da haka har suka iso dai-dai k'ofar gidan su Jawaheer, dubanta Rashida tayi ta ce
"Ki k'ara hak'uri Jawaheer komai yayi zafi maganin shi Allah ke dai kawai ki cigaba da addu'a da yardar Allah komai zai zama normal kin ji ko?"
"Insha Allah Rashida nagode sosai da kulawar ki agare ni Allah ya bar zumunci"
"Ameen ya rabbi"
Sallama suka yi Rashida ta wuce kasancewar gidan su na d'an gaba da gidan su Jawaheer sai dai bawani ni sa sosai. A soron gidan suka ci karo da Jabeer fitowar shi daga d'akin Mu'azzam kenan, cike da jin dad'in ganin ta ya ce
"Sannu da zuwa Queen ya hanya?"
D'aure da fuska da amsa masa da "Lafiya" Ba tare da ta tsaya jin abin da zai fad'a ba tayi shigewar ta cikin gida.
Da mugun mamaki Jabeer ya bi ta da kallo.
A 6angaren Jawaheer kuwa tana shiga cikin gida d'akin ta ta shige game da fad'awa kan d'an madaidaicin gadonta tana rizgar kuka mai ban tausayi.
Kamar hoto haka Jabeer ya tsaya a gurin sam ya kasa motsa ko d'an ya tsansa.
"Kai lafiya kayi tsaye anan kamar hoto?" Mu'azzam ya fad'a yana k'ok'arin rufe d'akin.
Kasa ce masa komai Jabeer yayi, kusa gare shi Mu'azzam ya isa game da d'ora hannunsa akan kafad'ar Jabeer ya furta
"Ya dai abokina? Meya faru ne? Na ga dai lafiya k'alau ka fito d'akin kana fara'a, kuma yanzu na ganka cikin damuwa lafiya?"
"Kenan ba Innah kad'ai ta sauya man ba harda Jawaheer" Jabeer ya ce da shi cikin rawar murya.
"Kamar ya? Kayi man bayani yadda zan ga ne"
Bai rage komai ba ya fad'a masa abin da ya faru yanzu shi da Jawaheer. Sosai Mu'azzam yayi mamaki.
"Anya kuwa ba Mummy ba ce?" Cewar Jabeer.
"Me kuma Mummy tayi?" Mu'azzam ya tambaye shi.
"Mu'azzam ina ji a jikina kamar akwai abin da Mummy ta yiwa Innah da Jawaheer, ka duba fa ka ga a tarihin zaman mu Innah dai-dai da d'ai rana ba ta ta6a sauya man ba sai yau, hakama Jawaheer."
Shiru Mu'azzam yayi sannan ya ce
"Kayi hak'uri Jabeer zan bincika inga meke faruwa insha Allah"
"To shikenan nagode Mu'azzam"
Sallama suka yi jikin Jabeer a sanyaye ya fito daga gidan.
*_Four days later!._*
Kallo d'aya zaka yiwa Jabeer kasan ya canza dan kuwa yayi bak'i ya rame sai ka ce wanda ya shekara yana jinya. Shi ba abin da yafi d'aure masa kai irin yadda Jawaheer ke gudun sa sam tak'i bari su had'u rabon sa da ya ganta tun ranar da suka had'u a soron gidan su ta dawo daga islamiyyah, wayar ta kuwa kullun idan ya kira sai ace masa a kashe take. Duk lokacin da ya yiwa Mu'azzam zancen sai dai ya ba shi hak'uri ya ce shi ma har yanzu ya kasa ga no dalilin sauyawar su, tunanin sa ne ya katse sanadiyar wata sarawa da kansa yayi, hannunsa yasa ya dafe kan na sa yana k'ok'arin ta shi ya d'auko maganin sa ya sha dan yanzu wajen kwanan sa had'u yana fama da matsanan cin ciwon kai.
*******
"Haba Jawaheer wannan kukan ba maganin da zai yi maki, dan Allah ki cire duk wani abu a ranki, ni kaina ina jin zafin hukuncin da na yanke maki akan Jabeer amma inaga wannan hanyar kawai ce mafita agareki tun da mahaifiyar sa bata son ku tare"
Cikin muryar kuka ta ce "Hakane Innah amma damuwata d'aya Jabeer baisan dalilin gudun sa da nake yi ba, haka zalika bai san dalilin da yasa kika sauya masa ba, ina ganin kamar bai dace ayi masa hukunci akan abin da ba shi da masaniya akan sa"
"Lokota da dama ina wannan tunanin Jawaheer, amma ki cigaba da hak'uri ki d'auki wannan lamarin a matsayin k'addarar ki idan Jabeer mijin ki ne wallahi sai kin aure sa idan kuwa ba mijin ki bane to fa idan kin so shi kamar ki mutu ba za ki aure sa ba dan haka ki rage wannan damuwar dan Allah"
"To Innah nagode Allah ya sa mu da ce"
"Ameen Ameen Jawaheer. Allah yayi maki albarka"
"Ameen Innah ta"
*****
"Yauwa Abban Waleed daman ina son na tambaye ka, ya ku ka yi da Hajiyar Jabeer" Aunty Fati ta fad'a idon ta k'yam akan mijinta.
"Hmmm! Ke dai bari kawai, wallahi sam matar nan batada mutumci. Nan ya zayyane mata duk yadda suka yi da ita"
"Ikon Allah, amma kam dai bata kyautawa kanta ba"
"Banni da ita, da yardar Allah sai tayi da na sanin duk abin da take aikatawa."
"To Allah ya sa muda ce, Allah kuma yasa mu fi k'arfin zukatan mu" Cewar Aunty Fati.
"Ameen ya rabbi" Baba Al'ameen ya amsa mata da shi.
*©Zahra~B~B👌🏻.*
YOU ARE READING
ZAMANTAKEWA!.
Non-FictionSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...