*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*
*BABI NA HAMSIN DA TARA.*
Yau kwanakin da ya ba ta suka cika tun safe yake tsammanin ganin text d'inta ko kira amma shiru har yanzu bai ga ko d'aya daga cikin su ba."Anya kuwa zan samu kar6uwa wajen wannan yarinya kuwa? Ko dai ba ta sona?" Tambayoyin da suka addabi zuciyar Zaid kenan, amma sam ya kasa samun amsar su.
"Allah na rok'eka kasa na samu kar6uwa a wajen Maryam, Allah ya sa ita ma tana sona kamar yadda nake sonta" Addu'ar da yake yi kenan a ranshi.
Jin anyi kiran sallar azahar yasa shi tashi cikin rashin kuzari ya nufi bathroom dan d'auro alwala, yana fitowa ya wuce masallaci.
*_03:00pm._*
Kwance yake yana juyi tun bayan dawowarsa daga masallaci ya kwanta ko Allah zai sa bacci ya d'auke shi amma abin ya ci tura, hak'ura ya yi ya tashi zaune tare da rungume pillow, ajima-ajima ya duba wayarsa amma shiru sosai gabansa ke fad'uwa.
Yana tsaka da tunane-tunanensa ya ji wayarsa tayi k'ara alamar sak'o ya shigo, hannunsa har rawa yake yi ya duba cikin sa'a kuwa yaga number Maryam ce, zunbur ya tashi daga zaunan da yake ya dawo tsakar dak'i ya tsaya.
"Allah kasa naga alkhairi a wannan text d'in" Abin da kawai Zaid ya fad'a, bakinsa d'auke da bisimillah ya bud'e message d'in.
_Bakomai na aminta da kai Allah yasa hakan ne mafi alkhairi a rayuwar mu baki d'aya, mu had'u gobe k'arfe hud'u na yamma bye._
Wayyo dad'i sam Zaid ya kasa babbance sama yake ko k'asa.
"Alhamdulillah!Alhamdulillah!!" Abin da kawai bakin Zaid ke furtawa.
Da gudu ya bar d'akin ya nufi side d'in mahaifiyarsa. Zaune ya sameta a falo, kusa gareta ya zauna cike da farin ciki yake fad'in
"Ummi ta yarda, wallahi ta amince"
"Wacece?" Ummi ta tambaye shi cike da mamaki dan bai ta6a yi mata zancen kowa ba.
Shiru ya yi bai ce da ita komai ba.
"Magana nake yi kayi shiru, wacece?"
Sai yanzu ya gane inda Umminsa yazo wata kunya ce ta kamasa.
"To yanzu me zance mata bayan ko labarinta ban ta6a bata ba" Ya fad'a a zuciyarsa.
"Uhmm! Uhmm!!" Ya rink'a cewa yana sosar kansa.
Murmushin su na manya Ummi tayi had'e da cewa "Kai nake sauraro"
Wayarsa tayi k'ara alamar an kirasa, wani dad'i ya ji ganin ya samu hanyar guduwa.
"Ummi ina zuwa bara na d'auki wayar nan dan Allah" Ya ce da ita game da barin falon.
Girgiza kai kawai Ummi tayi had'e da yin murmushi a lokaci guda kuma tayi godiya ga Allah da ya nuna mata wannan ranar.
"Yau zan yiwa Alhaji albishir" Ta furta cike da farin ciki.
******
*_05:05pm._*
Tsaye suke sun jingina a jikin motar dake ajiye a wajen. Kallonsa Zaid ya maida ga Marwan ya ce
"Albishirinka"
YOU ARE READING
ZAMANTAKEWA!.
Non-FictionSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...