BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI.

603 52 11
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*













*Na Xarah~B~B.*














*{NWA}.*









www.zahrabb.blogspot.com









*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*






       _Wannan shafin na kine ke kad'ai *Rabi'at A'A* na gode sosai da k'aunar da kike nunawa littafe na. JJ na gaida ke sosai._











     *BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI.*





   Wayarta dake cikin jakar islamiyyah ta ji tana vibration, sai ma lokacin ta tuna da bata fitar da ita ba. Inda jakar take ta je ta fitar da wayar tare da cireta daga vibration, ganin Waliyya ce ta kirata yasa ta aje wayar har tayi sallah sa'annan ta bi kiran. Cike da natsuwa ta gabatar da sallarta ta azahar sosai tayi addu'a kafin ta ta shi daga wajen. Zamanta ke da wuya ta ji wayarta tayi k'ara alamar sak'o ya shigo, hannunta ta zila kad'an ta janyo wayar tare da duba sak'on tana dubawa taga number da tayi mata text ne jiya.

    _"Sannu da zuwa my love! Ya kike ya gajiyar school?"_

Abin da taga an rubuta kenan a text d'in.

   "Shin wai wannan waye ke son ya takura man? Ina ma ya samu number na? Ya akayi ya san na je makaranta?" Tambayoyin da Maryam ta yiwa kanta kenan. Ganin bata da amsar su yasa tayi dialing number Waliyya, ringing biyu ta d'auka game da yin sallama.

Amsa sallamar Maryam tayi kafin ta ce  "Ya akayi ne? na ga miss call d'inki"

   "No bakomai, gaishe ki ne kawai nayi"

"Kai tawa! Yanzu fa muka rabu, ko har kinyi missing d'ina?" Maryam ta ce da ita tana murmushi.

    "Eh nayi, ko laifi ne?"Cewar Waliyya.

"A'a ranki ya dad'e ai bakya laifi"

Dariya suka yi a tare sannan suka yi sallama suka tsinke wayar.

******

   "Wai lafiya kwana biyu na ga duk ka hargitse?"

"Hmmmmm! Ai dole na hargitse Marwan"

"Meyasa ka ce hakan?"

    "Saboda tak'i ta kar6i soyayya ta sam ta kasa fahimtar irin son da nake yi mata"

Sake da baki Marwan ke kallon Zaid, sosai ya yi mamakin maganar Zaid.

"Ashe akwai ranar da Zaid zai ce yana son wata mace? Lallai ko ma wacece tayi sa'ar samun miji" Marwan ya fad'a a ranshi. A fili kuwa sai cewa ya yi

"Wacece ita? Kuma a ina take?"

Bai 6oye masa komai ba,  tun farkon had'uwar su har yadda suka yi da Waliyya duk sai da ya fad'a masa. Shiru Marwan ya yi kafin ya ce

   "To meyasa ba za ka fuskance ta ka fad'a mata da kanka ba"

"Tsoro nake ji! Tsoro nake ji Marwan"

   "Tsoron me kake ji Zaid?"

"Kar ta ce bata sona. Wallahi Marwan ina sonta so bana wasa ba dan Allah ka taimaka man"

"Lallai ba k'aramin so Zaid ke yiwa yarinyar nan ba" Ya fad'a a zuciyar shi.

     Shiru Marwan ya yi na wasu sakanni kafin ya kalle abokin na shi cike da kulawa ya ce

"Ka  kwantar da hankalinka Zaid ba za ta ce bata sonka ba Insha Allah, yanzu abin da kawai nake so da kai kayi k'ok'ari ka gabatar da soyayyar ka gareta nasan duk macen da ta same ka to ta gama sa'a a rayuwarta" Haka dai Marwan ya cigaba da lallashin abokin shi tare da ba shi baki.

******

*_07:45pm._*

   Sallamar ta daga sallar Isha'i kenan. Al-Qur'anin dake gefenta ta d'auka tare da fara karatu, ta jima tana karatu kafin ta ajiye shi, addu'a sosai ta yiwa mijinta Allah ya k'ara shirya mata shi. Allah ya k'ara basu ikon fahimtar junan su yadda *ZAMANTAKEWAR* su zata k'ara yin kyau kuma ta zama abin kwatance ga kowa. Ta d'auki lokaci tana addu'a kafin ta shafa.

Dressing mirrow ta nufa fuskarta ta k'ara gyarawa game da sake feshe jikinta da turare. Kai tsaye falo ta nufa, d'aya daga cikin kujerin falon ta zauna had'e ta kunna TV kafin mai gidanta ya dawo sai dai sam hankalinta baya ga kallon yana a k'ofar falon tana jiran dawowar abin k'aunar ta, ajima-ajima ta kalle k'aton agogon dake manne ajikin bangon falon.

K'arfe tara da rabi(09:30pm) dai-dai ta ji parking d'in motar sa, wata ajiyar zuciya tayi tare da yin hamdala ga Allah kafin ta mik'e tsaye dan tarbo sahibinta. A k'ofar falon suka ci karo da shi, sannu da zuwa tayi masa game da kar6ar ledar hannun shi.

   Amsawa ya yi cikin jin dad'i had'e da rik'o hannunta yana murzawa. Cike da shagwa6a ta furta

"Me ya tsayar da kai? K'arfe tara har da rabi fa"

   "Wani uzuri ne kiyi hak'uri wify" Saleem ya fad'a tare da janta suka zauna kan two seater(Kujerar zaman mutum biyu)dake falon.

"Ni gaskiya na ga ji da wannan uzurin da kullun ake fad'a koma an k'i a sanar da ni" Ta furta kamar za tayi kuka.

   Janyo ta ya yi jikin shi. "Kiyi hak'uri my sweetheart idan lokacin ki san shi ya yi za ki sa ni kuma sai kin fi kowa jin dad'i idan kika san ko wane uzuri ne."

   "To ni ka fad'a man yanzu"

"A'a time d'in ki sa ni bai yi ba amma idan ya yi zan fad'a maki"

   "To Allah ya kaimu lokacin lafiya"

"Ameen Ameen matata abin alfaharina, a kullun sonki da k'aunar k'i k'aruwa suke yi a zuciya ta. Ina sonki sosai Saleema ta"

   "Love you too my husby" Ta ce da shi cike da jin dad'in kalaman mijinta.


   Tooo fa! Readers gare ku, wane irin uzuri ne ke tsayar da Saleem kuma har ya kasa fad'awa Saleema? Meyasa ya ce idan ta ji uzurin zata fi kowa farin ciki?.

    Duk wadda/wanda ta/ya amsa dai-dai akwai gift.




Please don't forget to vote and comment on Wattpad @Zarah_bb

    Ur vote nd comment count alot.






     Muje zuwa.........









*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang