BABI NA ASHIRIN DA TARA.

574 57 2
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*







*Na Xarah~B~B.*





*{NWA}.*




www.zahrabb.blogspot.com



*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*



_Happy Eid-el-kabeer and Jumu'at Mubarak to all my luvly and caring Fans._



  *BABI NA ASHIRIN DA TARA.*



    A 6angaren Mummy kuwa tun bayan fitar Jabeer take kai kawo acikin falo, tunani take yi waya fad'awa Jabeer ta je gidan su Jawaheer. Dan tabbas yanayin da ya fita ya tabbatar mata da ya ji zancen.

"Wa zai fad'a masa kuwa in ba Jawaheer ba"

   "Anya kuwa? Yadda Jawaheer take da tsoro kamar farar kura ai bazata fad'a masa ba."

"To ko dai abokin da yayi sallama da shi ne?." Haka dai ta cigaba da zancen zucinta.

Sallamar da Jabeer yayi ta maido ta daga zancen zucin da take yi. Ba ta ko amsa masa sallamar ba ta watso masa tambaya da cewa

   "Daga gidan uban wa kake?"

Shiru yayi baice da ita komai ba.

   "Da kai nake magana Son"

"Daga gidan su Jawaheer nake"

    "Ku tumar nan! Me ka je ka yo acan? Ba na ce kada ka k'ara zuwa ba?"

"Kin ce" Ya fad'a atak'aice.

    "To me ka je yi gidan?"

"Hak'uri na ba su"
      "Da akayi me?"

"Abin da kika je kika yi masu. Haba! Mummy bai kamata kina irin wannan ba, dan Allah menene aibun auren talaka?"

   "Au! Ita Jawaheer d'in ce ta ce maka na je gidan na su?"

"Wallahi kada ma ki zargeta amma ba ita bace"

   "To waye?"

"Ni dai na fad'a maki ba ita bace" Bai jira abin da zata koma ce masa ba yayi shigewarsa. Yana jinta tana ihun kiran sa ya k'yaleta.

  "Lallai ma Son! Yaushe ya raina ni har haka?" Haka ta cigaba da yin sabbatu game da tunanin menene mafita game da wannan lamarin.

******

*_03:55am._*

Sosai ta yiwa mijinta addu'ar shiriya acikin sujudarta ta k'arshe, haka ma bayan tayi sallama ta dad'e tana kwararo addu'a tare da fatan gamawa da iyayenta had'e da wannan duniyar lafiya.

   Saleem dake kwance akan gado, wani so da tausayin matar sa ne ke k'ara shiga zuciyar sa. Ku san kullun idan ya farka da daddare sai ya ganta tana nafilfili game da yi masa addu'a. Bai yi aune ba sai ji yayi hawaye na bin fuskar sa, duk wannan abun da Saleem ke yi Saleema batasan yana yi ba. Jin an fara kiraye-kirayen sallar asuba yasa ta mik'ewa tsaye, ta ku biyu zuwa uku tayi ta isa wajen da Saleem yake kwance, a hankali ta fara bubbuga hannun shi tare da kiran sunan sa cikin murya k'asa-k'asa. Kamar da gaske baccin yake yi ya rink'a yi mata mashalo da k'yar ya ta shi, sai da ta tabbatar ya tafi masallaci sa'annan itama ta ta da sallar.

******

"Wai waye gwani acikin samarin nan na ki Zuby?"

   Sai da tayi wata dariya sa'annan ta ce "Daman ba ki san gwanin na wa ba?"

"Shi ne matsalar y'an nigeria ka tambaye su su ma su tambaye ka ba tare da sun baka amsar ka ba" Sameera wadda suke kira da Samee ta fad'a tana murmushi.

  "Damar abin dai kema y'ar nigeria ce" Zuby ta ce da ita.

"To na ji, ni dai ki ba ni amsar tambaya ta" Cewar Samee.

   "Ki canka kawai y'ar mata"

"Bawani cankar da zanyi ke zaki fad'an"

    Sai da Zuby ta murmusa sannan ta furta "Ai sai ki jira"

"Au! haka za ki ce?"

    "Eh!"
"Bai da matsala ina zaune za ki zo ki fad'a man"

   "Kin san da haka meye na wahalar da kanki da tambaya"

"Ai na daina wahalar da kan na wa" Samee ta fad'a tana kallonta.

   Haka dai suka cigaba da firar su ta k'awaye kuma *AMINNAN JUNA.*

Wayar Zuby ce da ta d'auki ruri ya katse masu firar da suke yi, ganin sunan My Abdul ya bayyana akan screen d'in wayar yasa ta yin wani malalacin murmushi kafin ta d'aga wayar da cewa

    "Hello My dear ya kake ya hutawa?"

"Ai ba wata hutawa tun da ba kya kusa"

   "Haba dai?"

"Allah kuwa"
   "To yanzu ya kake son ayi?"

"Gaskiya ina son mu had'u. kina ina yanzu?"

    "Ina gidan su Samee"

"OK gani nan zuwa yanzu in d'auke ki"

   "OK sai ka zo" Ta fad'a game da tsinke wayar.

"Lallai kin fi son Abdul fiye da sauran"

   "Meyasa kika ce haka?"

"Sobada Muby yayi maki miss call ya fi a k'irga Sa'eed ma haka amma kina ganin kiran su kika k'i d'agawa but Abdul kira d'aya yayi kika d'aga."

   "Ita kad'ai ce hujjar ki, na cewa na fi son Abdul?"

"Eh! Ko k'arya na fad'a?"

    "A'a ranki ya dad'e ai bakya k'arya"

Dariya Samee tayi kana ta ce "Kenan shi ne gwanin?"

    "Haka nake tunani dan ba k'arya na fi son Abdul da su"

"Meyasa kika fi son sa?" Samee ta tambaye ta.

   Murmusawa Zuby tayi game da gyara zamanta kana ta furta.......









*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora