BABI NA GOMA SHA TARA.

649 59 2
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*





*Na Xarah~B~B.*



*{NWA}.*



www.zahrabb.blogspot.com


  *Vote me on Wattpad @Zarah_bb*



_Abinda ka/ki koya da farko a cikin addini shine abin da za'a tambaye ka/ki a cikin k'abarinka /ki. Ba tarin ilimi ke da muhimmanci ba, aiki da shi._


*BABI NA GOMA SHA TARA.*



    Tasss tasss kake ji ya wanke ta da mari har sau biyu, tsabagen mamaki da ya cika mata ciki yasa ta kasa d'agawa daga inda take dan duk abun Saleem sai dai ya daketa bai ta6a marinta ba sai yau, kumatunta ta dafe hawaye na ambaliya a fuskar ta. Ta d'au lokaci a haka kafin cikin muryar kuka ta furta
"Ni ka mara Saleem?"
    "Eh an mare ki ko kinada abunda zakiyi?. Kuma wallahi idan ba ki iya bakin ki ba watarana sai na 6a66allaki" Saleem ya fad'a cikin muryar maye.

Da k'yar ta iya jan k'afarta ta nufi d'akin ta ba tare da ta ce da shi komai ba. Tana shiga d'akin ta fa d'a kan gado game da sakin wani kuka mai ta6a zuciyar mai sauraro.

_Flash back!._

      *WACECE SALEEMA??!.*

  Saleema d'iya ce ga Alhaji Abubakar da Hajiya Maimunatu, su uku iyayen su suka haifa. Aunty Hauwa itace babba tayi aure harda yara biyu sai Yaya Aliyu ke bin ta yana gurin service sai autar su Saleema tana final year d'inta a polytechnic. Sun samu ingantacciyar tarbiya da kulawa a wajen iyayen su. Watan Saleema d'aya da kammala karatun ta suka had'u da Saleem soyayya yake nuna mata bil hak'k'i, ganin yaran sun dai-daita kansu yasa Abban Saleema ba Saleem damar turo iyayen shi. Haka iyayen sa suka zo aka saka rana nan da wata uku.
    Kwanci ta shi ba wuya a wajen Allah lokacin da aka saka na bikin ya zo aka sha shagalin bikin su.

       *WANENE SALEEM??!.*

Hon. Ibrahim Hassan da Hajiya Saudatu sune iyayen Saleem su biyu ne a wajen mahaifan su shine babba sai k'anwar sa Asiya tayi aure amma bata haihu ba. Saleem yana da wani 6oyayyen hali da ba wanda ya san shi da shi sai abokanin sa da suke yin abun tare. Halin kuwa ba komai bane illah shan barasa sam har suka yi aure da Saleema bata san yana da wannan mugun halin ba.

Bayan auren Saleem da Saleema soyayya mai tsafta suke yiwa junan su, kowanan su yana tattalin d'an uwan sa. Watan su biyu da aure Saleema ta fara fuskantar canje-canje a wajen Saleem mugun halin shi ya bayyana abun har ya kai ka iyayen su, sosai suka yi mamaki lokacin da akace Saleem na shan giya. Shawara aka yanke na za'a raba auren su, da kuka da magiya Saleem ya bada hak'uri tare da yin alk'awarin daga ranar ya daina shan barasa. Hakan da yayi yasa iyayen suka hak'ura, sosai akayi masa nasiha.

    Wannan kenan!.

*******

Washegari tun da safe Saleema ta shirya kayanta zata tafiyar ta gida dan yau ta kai bango, tsawon shekarar su biyu kenan da Saleem amma ya k'i ya canza halin shi kullun cikin yin alk'awarin ya daina yake amma a banza. Trolly'n ta data saka kayanta ta janyo tana bud'e k'ofa suka ci karo da shi, d'auke kanta tayi kamar bata ganshi ba tana k'ok'arin ra6awa ta gefen shi ta wuce, rik'e mata hannu yayi had'e da fad'in

   "Ina za ki tafi ne haka Saleema? harda d'aukar akwati"

"Gidan mu" Ta ba shi amsa atak'aice.
     "Meyasa?"

"Hmmmmm! Tambaya ma kake yi ko? Lallai ma Saleem ka ce wani abu wallahi"
    "Me na ce?"

"Ban sa ni ba" Ta ce da shi cike da tsiwa.

    "Haba Saleema dan Allah ki tsaya mu fahimce junan mu please"

"Wane fahimtar juna zamuyi? Idan har shekarun da muka kwashe tare baisa muka fahimce juna ba ai bana tunanin wannan lokacin zai sa mu fahimce juna. Ko so kake in zauna kayi ta dukana da marina? Hmmmm to bari ka ji ni ba jaka bace da zan zauna idan kayo shaye-shayen ka kayi ta dukana, dan haka ni tafiya ta zanyi sai ka neme ta duka"

   "Kin ga dan Allah ki daina zancen tafiyar nan, da wane ido kike son in kalle su Abba?"

"Idon da kake kallona da shi ka sharara mani mari" Ta fad'a tana k'ok'arin k'wace kanta daga rik'on da yayi mata, cikin sa'a kuwa ta k'wace tabi hanyar fita......







*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin