*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*
_Ba kamar mutum uku a duniya: Na farko wanda ya so ka sa'ar da kowa ya k'i ka. Na biyu wanda ya ba ka sa'ar da kowa ya hanaka. Na uku wanda ya zo maka sa'ar da kowa ya gujeka. Allah yasa muda ce Ameen._
*BABI NA TALATIN DA TARA.*
Cike da natsuwa take tafiya, kallo d'aya zaka yi mata kasan mace ce mai kamon kai. Tun da ta fito daga gidan su Waliyya yake bin ta, tun yana yi mata horn har ya fito waje amma sam ta k'i ta kulasa idan da abin da ta tsana a rayuwa shi ne namiji ya rink'a bin ta a hanya. Ganin ba ta da niyyar kulasa yasa ya hak'ura da bin na ta ya yi tsaye yana kallon gidan da za ta shiga. Ita kuwa jin an daina yi mata magana yasa hankalinta ya kwanta duk a tunanin ta ya ta fi shiyasa tana zuwa dai-dai k'ofar gidan su ta shige da sauri.Wani iska ya furzar game da furta
"Allah yasa nan ne gidan su" Saurayin ya fad'a had'e da shiga motar sa ya fice jiki a sanyaye.
A 6angaren Maryam kuwa ganin ta shigo gida kamar wadda aka biyo yasa Mama tambayar ta ko lafiya.
"Lafiya k'alau Mama" Maryam ta bata amsa a tak'aice game da nufar d'akin su.
******
Kwance yake a kan gado hannuwansa rungume da pillow, da zarar ya rufe idon sa ba abin da yake gani illah kyakkyawar surarta da kuma yadda take tafiyarta cikin natsuwa. Yau kusan kwana biyu kenan kullun sai ya je unguwar su ya tsaya nesa kad'an da gidan da ya ga ta shiga ranar ko Allah zai sa ta fito ya ganta amma ba nasara haka zai yini har yamma ko mai kama da ita bazai ga ni ba balantana ita, haka zai dawo gida cikin sanyin jiki. A rayuwar sa bai ta6a jin yana son wata y'a mace ba wadda a lokaci d'aya ya ji ta kwanta masa kamar wannan Yarinyar, duk da iyayen sa sun yi ta za6a masa mata amma sai yaga bata yi masa ba sai dai ya basu hak'uri, ganin haka yasa suka tattara suka ajiye, sai dai suka cigaba da taya shi addu'a Allah ya za6a masa mata mafi alkhairi a rayuwar su ba ki d'aya.
Daren ranar sam Zaid bai runtsa ba, kwana ya yi yana nafilfili game da yin addu'a, sai da ya yi sallar asuba sa'annan ya kwanta.
******
"Dady dan Allah ka k'ara rok'on Mummy ta barni na aure wadda nake so." Jabeer ya fad'a kansa a sunkuye.
Shiru Dady ya yi na wasu sakanni kafin daga bi sa ni ya ce
"Ka k'ara hak'uri Son insha Allah za ka aure wadda ka ke so ka ji ko?"
"To Dady na gode sosai Allah ya saka da alkhairi"
"Ameen Ya rabbi Son" Dady ya furta yana mai tsananin jin tausayin d'an na sa, sam ya rasa gane wannan halin na matar sa. Ya tsane ganin Jabeer cikin damuwa amma kuma ko ya yi yunk'urin yiwa Mummy magana sai ya kasa ya rasa dalilin hakan.
******
"Jawaheer wai ya zancen auren ku da Jabeer ne?"
"Yana nan"
"Mummy'n sa ta amince da auren ne yanzu?"
"A'a! A dai tayamu da addu'a"
"Hmmmmm! To Allah ya sauwak'a ya kuma za6a maku abin da yafi zama alkhairi a rayuwar ku" Cewar Sarah.
"Allahumma Ameen Sarah, na gode sosai da kulawar ki Allah ya bar zumunci tsakanin mu."
"Ameen Ameen" Sarah ta amsa da shi.
******
*_11:05am._*
"Son kar ka bari na sa ke yi maka magana akan auren y'ar matsiyatan nan, na fad'a na kuma sa ke fad'a ba za ka ta6a auren ta ba idan har ina numfashi a dorun k'asa, wai me kake son ka maida kanka ne? Haba! Dan Allah ka yiwa kanka fa d'a ka zo ka aure y'ar kirki kuma y'ar arziki" Mummy ta k'arasa maganar cikin muryar lallashi.
"Mummy dan Allah kiyi hak'uri, amma bana son Lubna sam tarbiyarta bata yi man ba, Mummy ki duba fa ki ga irin shigar da yarinyar nan ke yi sai ka ce wata arniya kuma........." Ka sa idar da maganar ya yi sanadiyar wata tsawa da Mummy ta yi masa, cikin d'aga murya ta fara fad'in
"To wallahi Son baka isa ka karya wannan alk'awarin da na yi ba, ko dan ka ga ina lalla6a ka? To bara ka ji aure kai da Lubna anyi angama"
"To ai sai ayi in ga ni" Suka ji an fad'a daga bakin k'ofar falon.
Kallonta Mummy ta maida a wajen k'ofar dan ganin wanda ya yi maganar. Su na had'a ido ta ji hanjin cikin ta sun d'uri ruwa....
Ku canka ko waye Mummy ta gani ta rikice haka???.
_Ina jiran amsoshin ku._
Please don't forget to vote and comment on Wattpad @Zarah_bb
Muje zuwa.......
*©Zahra~B~B👌🏻.*
YOU ARE READING
ZAMANTAKEWA!.
Non-FictionSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...