BABI NA SITTIN DA TAKWAS.

596 52 11
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*






*Na Xarah~B~B.*



*{NWA}.*



www.zahrabb.blogspot.com


*Follow me on Wattpad @Zarah_bb.*

       _Kina ina? Asea B Aliyu wannan shafin nayi shi ne domin jin dad'inki. Na gode sosai Allah ya bar zumunci a tsakanin mu Ameen.#One Luv._

       *BABI NA SITTIN DA TAKWAS.*

   Washegari tunda safe Alhaji Mati yazo asibiti kawo mata breakfast.

   Bayan sun gaisa ya kalleta cike da tausayawa ya ce

"Sannu Lubna ya mai jikin?"

   "Ta ji sauki"

Ya d'an jima kafin ya tashi ya wuce gida zuwa anjima ya dawo.

    Idonta k'yam akan mahaifiyarta wadda har yanzu bata farka ba, da ba dan taga tana numfashi ba da ta ce ta mutu.

Da misalin k'arfe biyu na rana Hajiya Habiba ce tazo duba Hajiya Ladi kasancewar taji labarin abin da ya faru, sosai ta tausayawa k'awarta ganin halin da take ciki.

   Nurse ce ta shigo d'akin bayan sun gaisa ta isa wajen da Hajiya Ladi take kwance, k'arin jini ta cire mata kasancewar ya k'are sai ta jona mata ruwa tare da yi mata allurai sa'annan ta fice.

   Sai bayan sallar La'asar sannan Hajiya Habiba ta yiwa Lubna sallama ta fita.

Haka dai Lubna ta cigaba da jinyar Hajiya Ladi tare da taimakon Alhaji Mati dan komai da ake buk'ata na asibiti shi ke siya. Kwanan ta biyu a asibiti sannan ta farka  a hankali ta fara bud'e idanunta har ta bud'e su gaba d'aya.

   D'ayan hannunta wanda ba shi da k'arin ruwa ta saka ta dafe kanta sakamakon jin wata sarawa da ya yi mata.

Lubna dake zaune tana gyangyad'i kasancewar kwanan nan duk bata samun isashshen bacci ta farka nan taga mahaifiyarta ta farka da sauri ta isa wajenta tana yi mata sannu.

   "Lubna me ya same k'afata zafi nake ji sosai?"

"Sannu Hajiya, accident kika yi amma da sauki."

    "Wash! Lubna kaina zai cire."

A rud'e Lubna ta fita dan kiran likita bata jima ba sai gashi sun dawo tare da Dr da kuma nurse, abubuwan da ya kamata likitan ya shiga yi mata tare da taimakon nurse bayan sun kammala ya maida dubansa ga Lubna ya ce

   "Ki same ni a office akwai maganar da za mu yi"

"To" Kawai ta amsa masa da shi.

    Baifi minti biyar da fita ba ta mara masa baya.

Zaune ta same sa yana duba wasu file dake ajiye a gaban shi. Zama tayi game da cewa

   "Sannu da aiki Dr"

"Yauwa ya mai jikin?" Ya fad'a yana rufe file d'in.

   "Da sauki."

"To Allah ya k'ara sauki"

   "Ameen Ya rabbi."

"Yauwa daman akan zancen patient d'in mu ce"

   "Uhm ina jinka"

"D'ayan k'afarta ta samu matsala sosai tun daga y'an yatsun k'afarta har zuwa sama kuma kinga tana da ciwon sugar dan haka yanzu zamu d'orata akan wasu magugguna idan anyi nasara abun ya yi sauki to idan kuma aka samu akasin haka to dole sai anyi mata aiki."

ZAMANTAKEWA!.Where stories live. Discover now