*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*Follow me on Wattpad@Zarah_bb*
_Ina mai bawa masoyan wannan littafe hak'uri akan ji na da ku kayi shiru kwana biyu hakan ya farune akan wasu dalilai.#one luv._
*BABI NA HAMSIN DA TAKWAS.*
Sosai tayi nisa a cikin tunani, abubuwa duk sun tunkushe mata tama rasa ta ina za ta fara.
"To ko wajen boka zan koma ne?"
"Kin manta yadda ku kayi ne? Kin manta cewa ya ce idan har ba matsala aka samu a aikin ba kar ki sake ki dawo masa?" Zuciyarta ta tunasar da ita.
"Yau na shiga uku ni Zainabu, yanzu ya zanyi maganin da nawa Alhaji ya karye?" Ta fad'a kamar zatayi kuka.
Haka ta cigaba da sak'awa da warwarewa amma sam ta gagara samun mafita.
******
Tsaye yake a gefen titi yana jiran babur ya hau, ya jima amma ko keke bata wulga ba balantana babur kasancewar layin bai fiye mutane ba, wayarsa dake cikin aljihunsa tayi ringing alamar ana kiransa, d'auko wayar ya yi ganin Juwairiyya ce ke kiransa yasa shi fad'uwar gaba. Addu'a yake yi Allah yasa kada ta ce Mummy na neman sa, cike da fargaba ya d'aga wayar.
"Hello! Yaya ina wuni ya gida ya Aunty Jawaheer?" A ka furta a d'ayan 6angaren.
D'auke wayar ya yi daga kunnansa dan k'ara tabbatar da wadda ta kirashi. Ganin tabbas Juwairiyya ce yasa ya maida wayar cike da mamakin yau Juwairiyya da tambayar Jawaheer kuma harda kiranta Aunty, anya biri na mai kuwa?.
"Hello! Hello!! Yaya kana ji na kuwa?" Maganar da ta maido sa daga zancen zucin da yake yi.
"Eh, ina jinki ya akayi ne?"
"Dan Allah Yaya idan kana free ina son ganinka akwai maganar da za mu yi"
"Hmmm! Wace magana ce da ba za'a yi ta a waya ba?"
"Kayi hak'uri Yaya please ka bani time"
Sosai yake mamakin yadda Juwairiyya ta sauya.
Jin ya yi shiru yasa ta cewa "Dan Allah Yayana"
"OK! Na ji"
"Yaushe zaka zo?"
"Ina?"
"Gida"
"Au nima zan sameki? Allah kin ma rainani"
"A'a bahaka bane Yaya kayi hak'uri. Idan na fito Mummy zata iya fahimtar wani abu kuma sirri ne nake son muyi bana son ta sani"
"OK! Na ji zanzo amma ni kaina ba na son Mummy ta ganni dan nayi mata laifi"
"To Yaya idan da dama ka zo yanzu dan ba ta nan ta fita sai muyi maganar."
Shiru ya yi na wasu mintina yana wani nazari kafin daga bisani ya ce
"To ganinan zuwa Insha Allah."
"OK! Yaya na gode sosai Allah ya saka maka da mafificin alkhairi"
"Ameen" Ya amsa mata da shi had'e da datse kiran.
Takawa ya fara yi can sai ga babur, tsayar da shi ya yi tare da yi masa bayanin inda zai kaishi.
Basu jima a hanya ba suka isa k'ofar gidansu. sallamar mai babur ya yi sa'annan ya shiga cikin gidan. Kiranta ya yi ya shaida mata ya iso ta same sa a balcony.
YOU ARE READING
ZAMANTAKEWA!.
Non-FictionSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...