BABI NA ARBA'IN DA D'AYA.

583 56 2
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*










*Na Xarah~B~B.*






*{NWA}.*



www.zahrabb.blogspot.com



*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*




_Kada jin dad'in wani/wata ya tsone ma ido, ba ki/ka san abin da ya/ta rasa ba kafin Allah ya ba shi/ta ni'imar da yake cikinta/take cikinta. Kada damuwar ka/ki ta tada ma ka/ki hankali, ba ki/ka san alkhairin da za ta janyo ma ka/ki ba. Hak'uri shi ne maganin zaman duniya. Allah yasa muda ce da rabon sa Ameen._



    *BABI NA ARBA'IN DA D'AYA.*



*_02:30pm._*

   Mummy ce a tsakar d'akinta sai kai ka wo take tana nausar d'ayan hannunta. Sam ta rasa inda zata sa kanta dan bak'in ciki.

"Gaskiya fa Kawo Adamu ya fad'a maki, meye aibun talaka da bakya son sa? Haba! Zainabu ki yiwa kanki karatun ta natsu in dan wannan duniyar"

   "Kar ki damu da zancen sa ki share sa kawai ki aura masa d'iyar aminiyar ki, kada rashin had'a su auren ya shafe k'awancen ku"

Duk wad'annan zantukan da zuciyar ta take yin su. Kwata-kwata kanta ya k'ulle ta rasa me ma zata yi.Haka dai ta cigaba da sak'awa da warwarewa har aka yi kiran sallar la'asar.

     *_04:10pm._*

Zaune take a gafen gado duk abin duniya ya dameta, ta jima a haka kafin ta d'auki wayarta dake kusa da ita game da danna kiran number Halima har ta katse ba'a d'aga ba haka ta sake kira nan ma shiru wajen kira hud'u Mummy ta yiwa Aunty Halima amma bata d'aga ba nan fa Mummy ta k'ara fusata.

    A 6angaren Aunty Halima kuwa tana band'aki(Bathroom)shiyasa bata amsa kiran ba, tana fitowa ta duba wayar ta nan ta tarar da miss call d'in Mummy, murmushi kawai tayi had'e da furta

"Tun safe nake jiran naga kiran ki dan na san sai kin kira."

   Sai da Aunty Halima ta gama duk abin da take yi sannan ta samu guri ta zauna tare da dialing number Mummy, ringing d'aya Mummy ta d'aga ko sallamar da Aunty Halima tayi mata bata amsa ba ta hau fad'in

"Kin kyauta Halima, shi ne kika kai k'arata wajen Kawo Adamu ko? Me ya shafe ki a cikin wannan lamarin da har zakiyi man shishshigi a ciki?Tayi maki kyau kuma buk'atar ki ta biya amma ki sa ni za ki sha mamaki da ni kike zancen." Haka Mummy tayi ta yiwa Aunty Halima masifa sam ko magana ta k'i bari Aunty Halima tayi ganin masifar ba k'arewa za tayi ba yasa Aunty Halima ta katse kiran tana cewa

   "Oho dai, kyaji da shi komai ma za ki fad'a sai kiyi tayi, an fad'awa Kawo Adamu. Da can da ake lalla6ar ki ai k'in amincewa kika yi, haka kawai za ki hana yaro auren wadda yake so akan wani dalili na ki marar tushe. Da ba'a auren talaka ai da kema ba kiyi auren ba."

******

Kallo d'aya za ka yi masa kasan cewa yana cikin tsananin jin dad'i da farin ciki ji yake kamar ya ta shi sama dan murna, tun bayan lokacin da Kawo Adamu ya sanar da shi cewa gobe za'a je nema masa auren Jawaheer ya kasa zama ya kasa tsaye duk ya bi abokanin shi ya sanar da su hakama ya sanar da Mu'azzam da ya fad'awa su Baba da Innah gobe za'a zo nema masa auren Jawaheer.

    Haka abin yake ko a wajen Jawaheer tun da Labarin ya risketa take mik'a godiyar ta ga Allah. Jikinta har rawa yake ta kira Rashida da Sarah ta shaida masu, sosai suka taya ta murna.

******

Yauma kamar kullun zaune yake cikin motar sa yana hangen ta inda zai ganta.

    "Ka je k'ofar gidan da kaga ta shiga ranar ka aika yaro ayi maka sallama da ita" Wani shashe na zuciyar sa ya ayya na masa haka.

"To idan ba nan ne gidan su ba fa? Idan ma nan ne wa za ka ce a kirama? Ko ka san sunan ta ne?" Wani 6angare na zuciyar sa ya tambaye sa.

   Sitarin motar sa ya kaiwa duka had'e da furzar da iska daga bakin shi, addu'a yake Allah ya sa yau ya ganta kuma Allah yasa tayi amanna da shi. Kamar a mafarki ya hangota sai dai wannan karon su biyu ke tafiya, idon sa ya murza dan tabbatar da ba mafarki ne yake yi ba, tabbas ba mafarki bane ita d'in ce.

"Alhamdulillah!" abin da ya furta kenan game da fitowa daga motar ya jingina ya na latsar wayar da ke hannun shi dan baya son su fahimce su yake kallo. Suna isowa daf da shi ya yi masu sallama cikin muryar sa mai dad'in sauraro. Banza suka yi da shi tare da cigaba da tafiyar su ganin haka ya saka sa bin bayan su yana cewa

"Bai da ce a yiwa musulmi sallama ba yak'i amsawa sam wannan ba hali bane na mutanan kirki, dan Allah ku taimaka ku bani ko da minti biyu ne"

   Jin kalaman sa yasa Waliyya juyuwa tare da amsa sallamar sannan ta d'ora da cewa

"Lafiya dai ko Malam?"

"Lafiya k'alau Malama dan Allah idan ba za ki damu ba ina son nayi maki wata tambaya"

    "Uhm! Ina jin ka" Ta ce da shi a tak'aice.

Duk jan hannunta da Maryam ke yi amma ta k'i ta zo, sai ma mai da kallon ta da tayi ga wannan saurayin. Ganin hakan yasa Maryam cigaba da tafiyar ta ta bar Waliyya anan.

   "Dan Allah me sunan ki?

"Waliyya!" Ta ba shi amsa a tak'aice.

   "Wow nice name"

"Thank you"

   "You are always welcome. Yauwa Waliyya bai kamata ace na tsayar da ke a hanya ba kin ga har k'awarki ta tafiyar ta amma dan Allah idan ba damuwa ina son ki bani digit d'in ki sai na kira ki"

  Shiru tayi tana wani tunani kafin daga bi sa ni ta ce

"OK ba matsala"

    "Yauwa na gode sosai"

Number d'inta ta ba shi sannan suka yi sallama ta wuce. Shi kuwa hamdala ya yi ga Allah sa'annan ya shige motar sa.

   Da sauri Waliyya ta rink'a tafiya dan ta cimma Maryam amma ina tayi mata ni sa, tana hangota lokacin da ta shige cikin gida. Sai dai a soron gidan ta tsaya tana jiran ta dan bata son ta shiga gidan Umma ta tambaye ta ina take, ta fi minti uku a soron gidan tana jiran Waliyya kafin ta iso, tana shigowa soron Maryam ta banka mata wata uwar harara had'e da cewa

"Meyasa kika dawo? Ai da ki kwana acan, daga ganin mutum kin tsaya kina surutu da shi a hanya"

   "Kiyi hak'uri k'awata kin san ba kyau wulak'anta d'an adam"

Ba tare da Maryam ta koma ce mata komai ba ta k'arasa cikin gidan, itama mara mata baya ta yi.


    Ya ku ka ji wannan chapter????

Please don't forget to Vote nd comment on Wattpad @Zarah_bb



    Muje zuwa..........







*©Zahra~B~B👌🏻.*

ZAMANTAKEWA!.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora