*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA).*
www.zahrabb.blogspot.com
*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*
*BABI NA SITTIN DA BIYU.*
*_Bayan awa d'aya!._*
Zaune suke a saman kujerar da ke d'akin, zamanta ta gyara tare da maida dubanta gare shi ta ce
"Kud'i nake so."
"Kamar nawa?" Alhaji Mati ya tambayeta yana k'ok'arin gyara zaman hularshi.
"1 million."
"Me za ki yi da one million Lubna?"
"Au! Ba za ka bani ba har sai ka tambayeni abin da zanyi da su?"
"Ba haka na ke nufi ba, kawai dai naga kamar kud'in sunyi yawa"
"To shi ke nan ka barsu kawai" Ta fad'a cikin fushi had'e da mik'ewa tsaye.
"Ina za ki je da kika tashi?"
"Me ya dameka da inda zanje?"
"Haba Lubnata, kiyi hak'uri, me akayi akayi one million, yanzun nan ba sai anjima ba zanyi maki transfer, yi hak'uri ki zauna" Alhaji Mati ya ce da ita tare da janyota jikinsa.
Wani makirin murmushi Lubna ta yi kafin ta furta
"Ina jira"
"Yauwa ko ke fa da kika yi murmushin nan kinga yadda kika yi kyau kuwa?"
"Hmmm ko?" Ta ce da shi.
"Eh mana" Ya bata amsa.
K'ara wayar Lubna tayi alamar sak'o ya shigo. Tana dubawa taga Alhaji Mati ne ya yi mata transfer.
Kallonsa tayi tare da marmad'a masa ido.
"Ya! Sun shigo?" Ya furta yana murmushi.
"Eh" Ta ce da shi tare da k'ara narkewa cikin jikinsa.
Wani dad'i ya ji, a duniya in da abin da Alhaji Mati keso bai wuce ya ji Lubna cikin jikinshi ba. Rungume ta ya k'ara yi, sun jima a haka kafin Lubna ta furta
"Akwai maganar da na ke son muyi"
"OK ina jinki"
"Ina da ciki"
"What????" Ya fad'a da k'arfin tsiya tare da tunkud'eta daga jikinsa.
Cike da mamaki take kallon sa.
"Kima daina kallona kinfi kowa sanin k'a'idojina, sam a tsarina ban yarda da yin ciki ba"
"Ban fahimce ka ba" Ta ce da shi tana zarar ido.
"Ban yarda da cikin ba, ni sam ba nawa bane"
"Uhm! Dan Allah inma wasa kake ka daina, sanin kanka ne bana yarda da kowa ta wannan b'angaren sai kai, idan ba na ka bane na waye?"
"Kin fi ni amsar wannan tamabayar, yanzu alfarma d'aya zan iya yi maki kizo muje a zubar da shi" Ya k'arasa maganar tare da barin d'akin.
Cikin rashin kuzari tabi bayansa ba tare da ta koma yin magana ba.
Koda ta fita har ya tada mota ita kawai yake jira, tana shiga ya nufi wata private clinic da ita.
Kai tsaye office d'in likita suka nema bayan sun shiga office d'in sun gaisa sannan Alhaji Mati ya yi masa bayanin abin da suke so.
Shiru Dr Joseph ya yi.
YOU ARE READING
ZAMANTAKEWA!.
Non-FictionSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...