BABI NA SITTIN DA UKU.

654 54 3
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*









*Na Xarah~B~B.*






*{NWA}.*






www.zahrabb.blogspot.com





*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*




         *BABI NA SITTIN DA UKU.*



   A b'angaren su hajiya Ladi kuwa tafiya suka yi ba ta wasa ba. Can wani k'ungurumin daji suka dosa a k'afa kasancewar mota bata shiga wajen, sun jima suna tafiya kafin suka isa mazaunin bokan Hajiya Habiba na gaba Lubna da hajiya Ladi suna biye da ita.

    Layi suka bi saboda sun cimma mutane da yawa kowa da abin da ya kawo shi,  wa'iyazu billah Allah ka karemu daga yin shirka Allah ya bamu ikon yarda da K'addara ta khairi ko akasin haka Ameen.

Sai kusan yamma sa'annan layi yazo gare su. Kafin ma Hajiya Ladi ta fad'i abun da ya kawota tuni boka ya bayyana mata kuma duk abin da ya fad'a shi ne yazo da ita. Wata mahaukaciyar dariya bokan ya yi kafin ya d'ora da cewa

    "Me kike son a yiwa Jabeer da Alhaji Mati?"

Cikin rawar murya ta fara magana

    "Ina son a sakawa Jabeer son Lubna mai tsanani wanda idanun sa za su rufe baya ganin kowa sai ita. Shi kuma Alhaji Mati a karkato mana da hankalinsa ta yadda komai muka ce da shi a ta ke zai aikata ko ma meye ba tare da ya yi musu ba."

Cikin muryarsa marar dad'in sauraro ya ce

    "Angama"

Wata k'warya ya d'auko tare da yin wasu y'an tsaface tsafacensa amma sam ya gagara ganin komai a cikin k'waryar kasancewar Jabeer baya wasa da karatun Al-qur'ani game da addu'ar neman tsari daga dukkan abin k'i.

   K'ara yi ya yi ko zai ga akasin abin da ya gani a farko amma sam ba abin da ya canza. Fuskarsa a murtuk'e ya d'ago jajjayen idanuwansa da ba su da kyan gani ya ce

"Wannan yaron Jabeer a halin da yake yanzu ba abin da ke iya samun sa na sihiri ko asiri dan haka aikin sa sai dai wani lokacin."

    Ido hajiya Ladi ta zaro game da fad'in

"Ba wani abu da za'a iya yi?"

      "Gaskiya babu abunda zamu iyayi"

Lubna hankalinta a tashe kaman zatayi kuka ta gyara durƙusonta game da furta,
     "Adai taimaka mana boka, a ƙara dubawa"

Sai da ya ƙara y'an tsubbace-tsubbacenshi sannan ya ce musu,

    "Eh to ba za'a rasa ba, zan baki k'ullin magani da turare. Maganin ki tabbatar da kin sa masa shi a abinci turaren kuma a d'akin baccinsa za'a turara shi."

"To" Kawai ta ce da bokan ba dan tasan ta yadda zata saka ma Jabeer magani a abinci ba har ma ta turara masa turaren a d'akin sa.

    "Yauwa!" Boka ya furta da k'arfi, maganar da tayi sanadin dawowar Hajiya Ladi daga gajeren tunanin da ta afka.

Gaba d'ayan su suka maida duban su ga boka ba tare da sun ce uffan ba.

    Wata mahaukaciyar dariya ya yi a lokaci guda kuma ya murtuk'e fuska. Duk wannan abun da boka yake yi ya samo asali ne da ganin Alhaji Mati a yanayin da tsafinsa zai kama jikinsa da ya yi.

   Hoton Alhaji Mati ne rad'au a cikin k'waryar da ke rik'e a hannun bokan yana shak'iyancin sa. Sosai boka ya yi tsafi akan Alhaji Mati.

A gefen cikin Lubna kuwa magani boka ya basu tare da fad'a masu yadda za suyi amfani da shi. Kud'i masu yawan gaske boka ya neme da a zube masa, ba musu Hajiya Ladi ta zube masa su.

ZAMANTAKEWA!.Where stories live. Discover now