*ZAMANTAKEWA!.*
*Na Xarah~B~B.*
*{NWA}.*
www.zahrabb.blogspot.com
*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*
*BABI NA SITTIN.*
Haka abin yake ko a wajen Zaid, tsaf ya shirya cikin riga da wando na shadda kalar light brown, takalminsa da hularsa sunyi dai-dai da kayan sa. Hannunsa sanye da agogo mai kyau da tsada,
kallo d'aya za ka yi masa kasan cewa yana cikin farin ciki marar misiltuwa, wayar sa dake ajiye a gefen gado ya d'auka tare da danna kiran number Marwan, har ta kusa katsewa sa'annan ya d'auka.
"Ina ka ajiye wayar ne baka d'aga da wuri ba?"
"Ba na kusa da ita ranka ya dad'e" Marwan ya fad'a yana dariya.
"Hope ka shirya dan gani zan fito daga gida"
"Haba dai?"
"Allah, kar dai baka shirya ba?"
"Eh ban shirya ba"
"What???" Zaid ya fad'a cikin d'aga murya.
"Ba sai bayan sallar magrib kace za mu je ba?"
"Bana son iskanci Marwan please idan ma wasa kake ka daina"
Dariya Marwan ya rink'a yi masa kafin ya ce "Ka zo gani k'ofar gida ina jiranka na Maryama"
Wani gauron numfashi ya sauke had'e da cewa "Haba ko kai fa, sai na iso"
"A iso lafiya"
"Allah yasa" Zaid ya ce da shi.
"Ameen" Marwan ya amsa masa game da tsinke wayar.
******
A b'angaren su Maryam kuwa koda suka isa gidan aunty'n Waliyya ta saka mai aikinta ta gyara masu falon bak'i kasancewar ta san da zuwan su da kuma dalilin zuwan na su.
K'arfe hud'u da minti goma sha biyar na yamma(04:15pm)kiran Zaid ya shigo a wayar Maryam, d'aga wayar tayi tare da yin sallama,
Amsawa ya yi game da cewa
"Gani a hanya saura kad'an na k'araso unguwarku"
"Unguwarmu?" Ta furta a d'an tsorace dan ta san ba ta tab'a fad'a masa ko yi masa misalin unguwarsu ba.
"Hmmmm! Kina mamakin na san unguwarku ko? To ki daina yin mamaki domin kuwa har gidan ku na sani"
"Wai a ina yake samun labarinta ne har haka?" Abin da ta ayyana a ranta kenan.
Jin tayi shiru yasa shi ce mata "Bye sai mun iso"
"Ka ga" Kalmar da ta hana sa katse kiran kenan.
"Ya akayi ne?"
"Ba'a gida zamu had'u ba"
"Meyasa??"
Shiru tayi bata ce komai ba.
"Kinga Maryam ni nafison na zo gidanku ta yadda za'a san da zamana, dan Allah ki yarda da ni wallahi ba zan cutar da ke ba."
"Na yarda da kai, kar ka damu duk d'aya ne nan ma gidan auntyna ce zamu had'u"
"Duk da haka na fi son gida ta yadda zan gaishe da Mama da Baba."
YOU ARE READING
ZAMANTAKEWA!.
ספרות לא בדיוניתSuna matuk'ar son junan su amma iyayensa sun tsane talaka. **** Babanta ne amma ya zama tamkar mugun aboki agareta sam mahaifiyar ta bata son hanyar da ya d'orata akai. **** A matsayin su na ma'aurata sam sun kasa zama su fahimce junan su...