BABI NA SITTIN DA HUD'U.

631 51 2
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*









*Na Xarah~B~B.*






*{NWA}.*




www.zahrabb.blogspot.com

*Follow me on Wattpad @Zarah_bb*




            *BABI NA SITTIN DA HAD'U.*

               

    Likitocine ke iya k'ok'arin su ganin numfashin Zuby ya dawo dai-dai amma abin ya ci tura, sun shafe fiye da mintuna talatin(30minutes)kafin suka yi nasarar ceto ranta.

    Fitowa Dr's d'in suka yi daga d'akin, nan Maryam da Amatullah suka tare su dan jin abin da ke wakana.

"Ku bi Dr Aliyu Sarki a office d'in shi zai yi maku bayanin komai" Dr Yusuf ya ce da su yana k'ok'arin cire safar hannunshi(Hand gloves).

    "To" Kawai suka ce masa game da bin bayan Dr Sarki.

Zamansa ke da wuya suka shigo office d'in bakin su d'auke da sallama, alama ya yi masu da su zauna.

   Mama da Amatullah ne suka zauna Maryam kuwa tsaye tayi a gefen mama.

"Ina mijinta ko Babanta?" Tambayar da Dr ya yi masu kenan."

   "Ba tayi aure ba, babanta koma yana hanya gashinan zuwa, lafiya dai Dr? Kayi mana bayani please" Amatullah ta ce da shi cikin rawar murya.

Shiru ya yi na wasu sakanni kafin ya gyara zaman farin gilashin dake mak'ale a idanunsa, cike da natsuwa ya fara magana,

   "A gaskiya bazan b'oye maku ba marar lafiyar tana cikin wani hali, amma Alhamdulillah yanzu komai ya dai-daita sai dai kawai wata matsala d'aya.."

"Wace matsala Dr?" Maryam ta fad'a tana zarar ido.

   "Zuciyarta tana gab da bugawa idan har ba'a kiyaye abubuwan da zan fad'a maku ba"

Shiru suka yi suna sauraren sa hakan ya bawa Dr Sarki cigaba da bayanin shi.

   "Abu na farko shi ne a guje b'ata mata rai na biyu kuwa abata duk abin da take so dan hanamata shi zai iya janyo matsala a zuciyar wanda idan akayi rashin sa'a zata iya bugawa, idan kuma zuciya ta buga to mutum zai rasa ransa."

"Insha Allah za'a kiyaye likita" Mama ta furta ciki da tunanin to menene ya janyowa Zubaida shiga wannan halin da take ciki?.

    Magugguna Dr ya rubuta masu sannan ya mik'a masu takardar game da fad'in

"Ga wannan a siyo"

    Karb'a Amatullah tayi had'e da cewa

"Zamu iya shiga mu ganta?"

    "Eh amma banda hayaniya please"

"OK! Mun gode sosai Dr" Ta fad'a.

   "Bakomai" Ya amsa mata da shi yana murmushi.

A tare suka bar office d'in jikin su ba kuzari.

    Suna fitowa suka ci karo da Baba nan suka yi masa bayanin abin da ke faruwa.

Sosai ya jimanta lamarin. D'akin da Zuby take a kwance suka shiga.

   Kwance take akan gado idanunta a rufe, d'ayan hannunta dauk'e da k'arin ruwa.

Shiru suka yi na wani lokaci kafin Amatullah ta katse shirun ta hanyar fad'in

   "Bara naje na siyo maguggunan a chemis d'in asibitin" Ta k'arasa maganar tare da ficewa daga d'akin.

ZAMANTAKEWA!.Where stories live. Discover now