BABI NA HAMSIN DA BIYAR.

570 61 4
                                    

*ZAMANTAKEWA!.*






*Na Xarah~B~B.*




*{NWA}.*




www.zahrabb.blogspot.com





*Follow me on Wattpad@Zarah_bb*



   _Wannan shafin sadaukarwa ne ga duk wasu masoya masu son junan su domin Allah. Allah ya had'a mu da masoyan mu na gaskiya Ameen._





        *BABI NA HAMSIN DA BIYAR.*




     "Baby wai sai yaushe zaka turo iyayenka ne gidan mu?"

"Kar ki damu nan bada dad'ewa ba, jira kawai nake Dady ya dawo nima na k'agara naga munyi auren nan"

   "Allah ko babyna?" Zuby ta tambaye shi.

"Allah kuwa" Abdul ya bata amsa.

   "To yanzu kamar yaushe kake sa ran dawowar Dady?"

"Nan da wata biyu In shaa Allah"

    Ido ta zaro tare da cewa

"Har two months baby?"

    "Eh, ko sunyi yawa ne?"

Kanta kawai ta girgiza alamar Eh.

   "Kiyi hak'uri ai kamar gobe ne za kiga wata biyun sun yi kin ji my love?"

"OK! Allah ya kaimu."

   "Ameen Ameen."


******

   "Yanzu shawarar da zan baka tunda kuna exchanging messages da ita yanzu ka k'yaleta kwana biyu kada kayi mata text, ta nan zaka gane idan ta fara damuwa da kai."

"Allah ko Marwan?"

   "Allah kuwa"

"To taya zan fahimce hakan?"

   "Za ta iya yi maka text ta tambaye ka ko lafiya kake, to daka ga haka ta fara sonka abokina dan kula itace soyayya."

"Haba dai?" Cewar Zaid.

  "Allah" Marwan ya bashi amsa.

"Amma fa ka kawo shawara mai kyau wallahi"

   "Kai dai ka gwada mu ga ko a dace"

"Insha Allah daga yau ma zan fara" Zaid ya fad'a yana murmushi.

   "Allah yasa za ka iya dan nasan halinka sarai"

"Haba! Zan k'ok'arta na gwada"

   "Allah yasa"

"Allahummah Ameen."

******

  *_10:20pm._*

Juyi kawai take yi kan gado ta rasa me keyi mata dad'i, tun d'azu take jiran text d'in aljaninta sunan da take kiransa kenan amma har yanzu shiru take ji. Duk ta ji bata jin dad'i sam bacci ya k'auracewa idonta. Addu'a take yi Allah yasa yanzu sak'on ya shigo wayarta. Ajima-ajima ta duba wayarta amma shiru ba message.

   Agogon dake manne ajikin bangon d'akin su ta duba ganin k'arfe goma sha biyu saura mintina yasa hankalinta k'ara tashi.

"Shin meke shirin faruwa da ni ne?" Maryam ta fad'a had'e da tashi zaune ta rafka uban tagumi.

    "To meyasa zan damu da shi bayan ban ma san shi ba"

"Me zai hana ki damu da shi tunda ya damu dake? Hausawa sun ce ka damu da wanda ya damu da kai, kika sani ko lafiya ce bashida shiyasa baiyi maki text d'in ba?" D'ayan zuciyarta ta ayyana mata hakan.

ZAMANTAKEWA!.Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin